Hukumar NCAA Ta Hukunta Matukin Jirgin Sama da Ya Sauka a Titin Motoci a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar NCAA ta dakatar da matukin jirgin sama da ya sauka a hanyar motoci a jihar Delta
- An dauki wannan mataki ne bayan matukin ya saukar da jirgin sama a kan titin Ogwashi-Uku ba tare da sahalewar hukuma ba
- Rahotanni sun nuna cewa hukumar tsaron farin kaya ta DSS da NCAA na gudanar da bincike kan abin da ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta sanar da dakatar da matukin jirgin da ya sauka a wani titin motoci a jihar Delta.
Hukumr NCAA ta bayyana cewa wannan mataki na dakatarwar zai ci gaba da aiki kan matuƙin jirgin saman har sai an kammala bincike kan lamarin.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa watan Yuni, 2026 ne wani jirgi mai zaman kansa mai lambar rajista N989BC, mallakin kamfanin VMO Aero Ltd, ya sauka a wata hanyar motocinda ke yankin Ogwashi-Uku na jihar Delta.

Kara karanta wannan
'Yan Arewa za su amfana da Amurka ta kawo tallafi mai kyau a fannoni 3 a Najeriya
Jirgin, wanda ke dauke da ma'aikata hudu, ya sake tashi daga wurin zuwa Legas ba tare da samun amincewar da dokoki suka tanada ba.
NCAA ta dakatar da jirgi da matukansa
Da yake zantawa da manema labarai a Legas yayin taron Airport Business Summit, shugaban NCAA, Kyaftin Chris Najomo, ya ce an dakatar da matukin jirgin da mataimakinsa daga gudanar da aiki har sai an kammala bincike.
Ya ce:
"Bincike na ci gaba da gudana a halin yanzu, tuni dai hukumar NSIB ta mika rahoton abin da ta binciko ga NCAA, kuma yanzu muna gudanar da namu binciken."
Najomo ya bayyana cewa an ajiye jirgin a kasa, sannan an dakatar da lasisin gudanar da aiki na Permit for Non-Commercial Flight (PNCF) da aka ba shi har zuwa lokacin da za a gama bincike.
Hukumar DSS ta shiga binciken
Shugaban hukumar NCAA ya ce, a matsayinsa na matukin jirgi na tsawon shekaru 45, ba zai iya fahimtar yadda matukin jirgi zai ga hanyar motoci kuma har ya sauka a kanta ba.
A rahoton Tribune Nigeria, Najomo ya ce:
"Ni matukin jirgi ne na tsawon shekaru 45. Ba zan iya ganin hanya kawai in sauka a kanta ba. Dole ne a binciki sauran dalilan da suka haddasa hakan."

Source: Getty Images
Najomo ya kara da cewa Hukumar Tsaro ta DSS ta shiga binciken lamarin, yana mai cewa har sai an kammala binciken, matukan jirgin za su ci gaba da kasancewa a dakace.
NCAA ta ci tarar kamfanin Saudiyya
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NCAA ta ci kamfanin jiragen saman Saudiyya tarar N6m saboda take haƙƙin fasinjoji da kuma kasa bin umarnin da aka ba shi.
Daraktan hulda da jama’a na NCAA, Michael Achimugu, ne ya bayyana hakan, inda ya ce matakin ya biyo bayan gazawar kamfanin wajen magance wasu matsalolin fasinjoji.
Achimugu ya ce NCAA ta dade tana bai wa Saudi Airlines damar warware korafe-korafen da fasinjoji suka shigar tare da bin umarnin hukumar, amma kamfanin ya gaza cika umarni.
Asali: Legit.ng
