Bayan Ya Fice daga APC, Omo Agege Ya Samu Takara a Jam'iyyar NDC
- Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege, ya sanar da matakin siyasa da zai dauka bayan ya fice daga APC
- Omo Agege, wanda daya ne daga cikin masu fada a ji na APC ya yi murabus daga jam'iyya mai mulki a wani sauyi na siyasar jihar Delta
- Bayan tsohon Mataimakin shugaban majalisar ya fadi dalilinsa na barin APC, NDC ta yi nasa tukwici bisa abin da ta kira kwarewarsa a aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Delta - Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege, ya bayyana cewa zai nemi takara bayan rabuwa da jam'iyyar APC.
Omo-Agege ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa NDC, tare da sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takarar kujerar Sanatan Delta ta Tsakiya a zaɓen 2027.

Source: Facebook
The Cable ta kawo labarin cewa Omo-Agege ya ce wannan mataki ya biyo bayan shawarwari da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, magoya baya da kuma abokan siyasa da suka shafe makonni ana yin nazari kan makomar siyasar sa.
NDC ta ba wa Ovie Omo Agege takara
Arise News ta wallafa cewa jam'iyyar NDC ta amince da ba wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege damar tsayawa takarar kujerar Sanaran Delta ta Tsakiya a 2027.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar NDC, Osa Director, ya fitar, jam’iyyar ta bayyana jin daɗinta kan shigar jagoran cikin NDC.
Jam’iyyar ta ce za ta samar musu da ingantaccen dandali mai gaskiya, haɗin kai da kuma fifita muradun jama’a domin su cimma manufofinsu na siyasa tare da bayar da gudunmawa ga ci gaban jihar Delta da Najeriya baki ɗaya.
Dalilin NDC na ba takara Omo-Agege
NDC ta bayyana cewa an yanke shawarar ba Omo Agege damar tsayawa takara ne saboda irin ƙwarewar siyasa, gogewa a shugabanci da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da dimokuraɗiyya da shugabanci nagari.

Source: Facebook
Jam’iyyar ta ƙara da cewa Omo-Agege ya nuna ƙwarewa wajen hidimtawa al’umma, abin da ya sa ta ga dacewar ba su damar fafatawa ƙarƙashin inuwarta a babban zaɓen 2027.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa shugaban na da ƙarfi a siyasance tare da samun goyon bayan jama’a a yankunansu, lamarin da zai taimaka wajen samar da wakilci nagari ga al’ummar Delta ta Tsakiya da Delta ta Arewa.
Sanata Omo Agege ya bar APC
A baya, kun samu labarin cewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege ya fice daga jam’iyyar APC bayan rikice-rikicen siyasa da ya hana ruwa gudu a jihar Delta.
Omo-Agege ya ce ba zai ci gaba da zama cikin jam’iyyar da ba zai iya kare muradun mutanen mazabar shiyyar Delta ta Tsakiya ba, saboda haka zai nemi sabuwar makoma da kowa zai mora.
Wannan na zuwa ne yayin da aka ruwaito cewa Omo-Agege ya gaza samun tikitin takarar kujerar sanata a zaben fitar da gwani na APC, kuma ana yi masa kallon mai tasirin gaske a siyasar Delta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

