'Yan Arewa Za Su Amfana da Amurka Ta Kawo Tallafi Mai Kyau a Fannoni 3 a Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa ƙasar Amurka na ci gaba da tallafawa Najeriya wajen bunkasa ababen more rayuwa da harkokin makamashi
- Hukumar Kasuwanci da Raya Kasa ta Amurka (USTDA) na tallafawa kasashe da dama ciki har da Najeriya a fannoni daban-daban
- Najeriya na daga cikin kasashen da tsarin ya fara bayyana, musamman a bangarori uku, makamashi, sadarwar zamani da kiwon lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
America - Amurka na neman fadada kasuwancinta, samar da ayyukan yi, karfafa tasirinta a duniya da kuma tabbatar da amfani da amintattun fasahohi a manyan ayyukan raya kasa.
A bangare guda kuma, Najeriya na bukatar ingantaccen makamashi, karfafa tsarin sadarwar zamani, samar da ayyukan yi da kuma aiwatar da manyan ayyukan raya kasa da za su bunkasa tattalin arziki tare da tabbatar da zaman lafiya.

Source: Getty Images
Premium Times ta ce wannan haduwar muradun kasashen biyu ne suka sa sababbin matakan da Hukumar Kasuwanci da Raya Kasa ta Amurka (USTDA) ke dauka suka zama abin lura.
USTDA ba tallafi kawai take bayarwa ba
A ranar 9 ga watan Yuli, yayin wani taron Washington RoundTable, babban jami'in USTDA, Thomas Hardy, ya bayyana cewa manufar tallafin da hukumar ke bayarwa ita ce taimaka wa ƙawayen Amurka da bunkasa muradun tattalin arziki da tsaro.
A cewarsa, hukumar na taimakawa wajen tsara manyan ayyukan raya kasa tun daga farko domin tabbatar da irin ayyukan da za a gina, kamfanonin da za su aiwatar da su da kuma ka'idojin da za su jagorance su.
Najeriya na daga cikin kasashen da wannan tsari ya fara bayyana karara, musamman a bangarori uku da suka hada da makamashi, sadarwar zamani da kiwon lafiya.
Arewa za ta amfana da tsarin Powergas
Daya daga cikin manyan ayyukan da USTDA ta tallafa shi ne aikin Powergas, wanda ya shafi gina karamin tashar adana iskar gas (LNG) domin karfafa iskar gas a Arewacin Najeriya.
A cewar USTDA, aikin zai taimaka wajen rage matsalar makamashi tare da bai wa kamfanonin Amurka damar samar da ingantattun fasahohi.
Thomas Hardy ya bayyana cewa ingantaccen samar da makamashi a Arewacin Najeriya zai taimaka wajen karfafa tsaro a fadin kasar, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.
Ana kara karfafa sadarwar zamani
Hukumar USTDA ta kuma tallafa wa binciken aikin kebul na karkashin teku mai suna Medusa, wanda ake sa ran zai kara karfin sadarwa a gabar tekun Atlantika ta Afirka.
Ana sa ran aikin zai inganta ingancin intanet, karfafa tsaron bayanai da rage barazanar hare-haren yanar gizo.

Source: Twitter
Ga Najeriya, wannan na nufin samun ingantaccen tsarin sadarwar zamani, yayin da Amurka ke tabbatar da amfani da fasahohinta da ka'idojinta.
Hukumar ta kuma taka rawa wajen samar da cibiyar kula da masu cutar daji a Asibitin Koyarwa na Legas.
Najeriya ta saba wa ikirarin Amurka
A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun saba wa ikirarin Amurka cewa ta kwace wasu muhimman kayayyaki daga ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan
PFIPC: Kamfanin Amurka ya kawo ɗauki ga shugaban hukumar bogi da ake ta surutu a Najeriya
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Birgediya Janar Samaila Uba, ya shaida cewa ba Amurka ce ta ƙwace na'urorin daga hannun ‘yan ta’adda ba.
A cewarsa, gwamnatin Najeriya ce ta miƙa waɗannan kayayyaki ga Amurka a matsayin wani ɓangare na haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci tsakanin ƙasashen biyu.
Asali: Legit.ng

