Magana Ta Kare, APC Ta Tsayar da 'Dan Takarar Gwamna a Jihar Gombe
- Jam’iyyar APC ta ayyana Dakta Jamilu Ishiaku Gwamna a matsayin ɗan takararta na gwamnan Gombe a zaɓen 2027 mai zuwa
- Jamilu Gwamna samu nasarar bayan Farfesa Isa Pantami da Sanata Sa’idu Ahmed Alkali sun sanar da cewa sun janye daga neman takarar
- Dukkanin 'yan siyasar biyu sun yi zargic cewa APC ta shirya yi masu adalci tare da zargin ana boye wadansu muhimman batutuwa game da zaben
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Gombe – Jam’iyyar APC ta bayyana Dakta Jamilu Ishiaku Gwamna a matsayin wanda ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar a jihar Gombe domin babban zaɓen shekarar 2027.
An sanar da hakan ne bayan kammala zaɓen fitar da gwani da aka gudanar a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa tun da farko dai APC ta zaɓi Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takarar maslaha, sai dai matakin ya fuskanci adawa daga wasu masu neman takarar.
Gwamna ya samu tikitin takara a Gombe
Kafar TVC News ta kawo labarin cewa Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen fitar da gwamnan APC, Sanata Sani Abubakar Danladi, ya ce an gudanar da zaɓen ne bisa tanadin dokar zaɓe ta 2022 da kuma ƙa’idojin hukumar INEC da na jam’iyyar.
Ya bayyana cewa jimillar masu kaɗa ƙuri’a 556,081 ne aka tantance suka shiga zaɓen a dukkannin ƙananan hukumomin jihar.

Source: Facebook
A sakamakon da aka bayyana, Dakta Jamilu Gwamna ya samu ƙuri’u 247,161 inda ya kayar da sauran masu neman takarar biyu.
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, ya samu ƙuri’a 12,120 inda ya zo na biyu, yayin da tsohon ministan sufuri, Sanata Sa’idu Ahmed Alkali, ya samu ƙuri’u 11,612 ya zo na uku.
Sanata Danladi ya ce:
“Ni Sanata Sani Abubakar Danladi, ina ayyana Jamilu Ishiaku Gwamna a matsayin wanda ya lashe wannan zaɓen fitar da gwani tare da mayar da shi halastaccen ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2027.”
Yadda Pantami da Alkali suka janye takara
Shugaban kwamitin ya kuma bayyana cewa kwamitinsu ya karɓi wasiƙun janye takara daga Farfesa Pantami da Sanata Sa'idu Alkali. Sai dai ya ce an gabatar da wasiƙun ne bayan an soma aikin zaɓen, wanda hakan ya sa sunayensu suka ci gaba da kasancewa a cikin takardun ƙuri’a, tare da ƙididdige ƙuri’un da aka kaɗa musu.
Sani Abubakar Danladi ya yaba wa shugabannin APC na ƙasa da na jihar bisa goyon bayan da suka bayar wanda ya taimaka wajen gudanar da zaɓen a cikin nasara.
Haka kuma ya jinjina wa jami’an tsaro da 'yan kwamitin zaɓen saboda haɗin kai da suka bayar wajen tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da zaɓen.

Kara karanta wannan
Gwamna Dikko Radda ya samu tikitin APC, zai nemi tazarce a zaben gwamnoni na 2027
Ya kuma yabawa gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, inda ya ce bai nuna son kai a kan yan takarar ba.
Rahotanni sun nuna cewa Jamilu Gwamna ya taɓa neman takarar gwamnan Gombe a ƙarƙashin PDP a zaɓukan fitar da gwani na 2018 da 2022, inda ya zo na biyu a lokutan biyu.
Sanata Goje ya sha kaye a Gombe
A baya, mun kawo labarin cewa tsohon gwamnan Gombe, Danjuma Goje ya rasa tikitin jam'iyyar APC na tsayawa takarar Sanatan Gombe ta Tsakiya karo na biyar a zaben 2027.
DCP Muhammed Ahmed, wanda gwamna Inuwa Yahaya ke goyon baya ne ya samu nasara a zaben fitar da gwanin da aka gudanar ranar Litinin 18 ga watan Mayu, 2027 a jihar.
'Dan takarar na APC ya ce an gudanar da zaben a cikin lumana ba tare da wata matsala ba a kananan hukumomin yankin Gombe ta Tsakiya da ya fito a shirin da ake na tunkarar babban zabe.
Asali: Legit.ng

