Biyu babu: Ministocin Tinubu da Suka Rasa Takara a APC bayan Sun Yi Murabus

Biyu babu: Ministocin Tinubu da Suka Rasa Takara a APC bayan Sun Yi Murabus

FCT, Abuja - Wasu tsofaffin Ministocin Shugaba Bola Tinubu sun yi murabus domin neman takarar muƙaman zaɓe gabannin babban zaɓen 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Shawarar da tsofaffin ministocin suka yanke ta haifar da sakamako daban-daban, inda biyu kacal suka samu nasarar samun tikitin takara.

Wasu tsofaffin Ministocin Tinubu sun rasa tikitin takara a APC
Saidu Usman Alkali, Yusuf Maitama Tuggar da Bayo Adelabu Hoto: Buhari Sallau, Bayo Adelabu
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro Ministocin da suka yi biyu babu bayan sun yi murabus daga gwamnatin Shugaba Tinubu kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ministocin Bola Tinubu 5 sun yi murabus

Tsofaffin mambobin majalisar zartarwa guda biyar ne suka ajiye muƙamansu bayan da fadar shugaban kasa ta umarci dukkan waɗanda aka ba wa muƙaman siyasa masu neman takarar zaɓe da su yi murabus kafin su shiga zaɓubbukan fitar da gwani na jam'iyyu.

Murabus ɗinsu ya yi daidai da tanade-tanaden dokar zaɓe ta shekarar 2026 wadda majalisa ta amince da ita kuma Shugaba Tinubu ya rattabawa hannu.

Kara karanta wannan

2027: Atiku da manyan ADC za su san makomarsu game da takarar shugaban kasa

Daga cikin waɗanda suka yi murabus ɗin akwai tsohon Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, tsohon Ministan sufuri, Saidu Alkali, tsohon Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar.

Haka zalika akwai tsohuwar karamar Ministar kwadago da samar da ayyukan Yi, Nkeiruka Onyejeocha; da kuma tsohon karamin Ministan ayyukan jin kai, Yusuf Sununu.

Yadda ta kaya da ministocin da suka yi murabus

A cikin mutane biyar ɗin, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Nkeiruka Onyejeocha da Yusuf Sununu ne kawai suka samu nasarar samun tikitin takara.

Onyejeocha ta lashe tikitin APC na mazaɓar tarayya ta Isuikwuato/Umunneochi a jihar Abia bayan da ta fito a matsayin yar takara ɗaya tilo da ba ta da abokin fafatawa.

Sununu shi ma ya samu tikitin APC na mazaɓar tarayya ta Yauri/Shanga/Ngaski bayan da ya janye daga neman kujerar sanata ta Kudancin Kebbi.

Tsofaffin ministocin da suka gaza samun tikiti

Sauran ministocin ukun da suka yi murabus, ba su kai labari ba bayan sun fafata a zaben fitar da gwani.

Ga jerinsu nan kasa:

1. Saidu Usman Alkali

Kara karanta wannan

Bayan lashe zaben fitar da gwani, kallo ya koma kan Tinubu game da kujerar Shettima

Tsohon Ministan sufurin ya ajiye muƙaminsa na majalisar zartarwa ne domin neman tikitin takarar gwamna na APC a jihar Gombe, in ji rahoton The Guardian.

Amma matakin ya kasa samar da sakamakon da ake tsammani yayin da ya rasa zaɓen fitar da gwanin a hannun Jamilu Gwamna, wanda ya samu goyon bayan Gwamna Inuwa Yahaya.

Saidu Alkali ya rasa tikitin APC a Gombe
Tsohon Ministan sufuri, Saidu Usman Alkali Hoto: Saidu Usman Alkali
Source: Facebook

Daga baya Alkali ya kaurace wa zaben fitar da gwanin, an ji shi ya yi zargin rashin adalci da gaskiya a lokacin gudanar da aikin.

Sakamakon zaben fitar da gwanin ya nuna cewa Saidu Usman Alkali ya zo na uku ne a bayan tsohon Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.

Yayin da Pantami ya samu ƙuri'u 12,120 ya zo na biyu a takarar, Alkali ya samu ƙuri'u 11,612 a matsayin na uku.

2. Yusuf Tuggar

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya yi murabus ne domin neman tikitin takarar gwamnan jihar Bauchi a inuwar jam'iyyar APC.

Ya rasa tikitin APC a hannun tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, bayan gudanar da zaben fitar da gwani.

Kara karanta wannan

'Mutumina ne': Peter Obi ya yi magana da ake zargin yana gujewa Atiku

Yusuf Tuggar ya rasa tikitin APC a Bauchi
Tsohon Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar Hoto: @MFANigeria
Source: Twitter

A cewar shugaban kwamitin zaɓen fitar da gwani na gwamna na APC a Bauchi, AIG John Bassey Abang (mai ritaya), Mohammed Abubakar ya samu ƙuri'u 57,517 ya doke Yusuf Tuggar, wanda ya samu ƙuri'u 26,001.

3. Bayo Adelabu

Bayo Adelabu wanda ya yi murabus bayan cikar wa'adin da shugaban kasa ya ɗibar masu, ya yi fatan samun tikitin takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Oyo gabannin zaɓubbukan 2027.

Sai dai kuma, tsohon Ministan wutar lantarkin ya sha kaye a zaben fitar da gwani a hannun Sanata Sarafadeen Alli.

Bayo Adelabu ya rasa tikitin APC a Oyo
Tsohon Ministan lantarki, Bayo Adelabu Hoto: Bayo Adelabu
Source: Twitter

Sanata Sharafadeen Alli ya samu ƙuri'u 578,143, ya yi galaba a kan Bayo Adelabu, wanda ya samu ƙuri'u 19,193, jaridar The Cable ta kawo rahoton.

Biyo bayan sakamakon, Adelabu ya yi zargin magudi a tsarin zaɓen fitar da gwanin, inda ya jaddada cewa zaɓen bai fito da ainihin muradin mambobin jam'iyyar ba.

Ya lura cewa zai ƙalubalanci sakamakon zaɓen, inda ya ƙara da cewa tawagarsa tana shirin mika takardar ƙorafi ga shugabancin jam'iyyar na matakin ƙasa.

Kara karanta wannan

2027: Jam'iyyar ADC ta amince mutum 3 su nemi takarar shugaban kasa a Najeriya

Bola Tinubu ya lashe tikitin APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya samu tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2027.

Shugaba Tinubu ya zama dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2027 bayan samun gagarumar nasara a zaben fitar da gwani na jam’iyyar.

Sakamakon zaben APC daga jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja ya nuna cewa Tinubu ya yi wa babban abokin hamayyarsa Stanley Osifo tazarar kuri’u mai yawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com