Fargabar Koro Malami daga Amurka zuwa Najeriya Ya Yi Sanadiyyar Rayuwarsa
- Wani limamin cocin Katolika ɗan Najeriya, Fasto Benjamin Madu, ya rasu a Massachusetts da ke Amurka
- Majiyoyi suka ce hakan ya biyo bayan an umurce shi ya koma Najeriya saboda ƙarewar takardar izinin zamansa ta aiki
- Marigayin ya shafe shekaru yana yi wa marasa lafiya da al'ummomin Katolika hidima a kasar lamarin da ya tayar da hankula
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Massachusetts, US - Wani limamin cocin Katolika ɗan Najeriya, Fasto Benjamin Madu ya rasa ransa a Amurka a wani irin yanayi.
Limamin wanda ke shirin barin Amurka bayan karewar takardar izinin aikin faston na addini, ya rasu ne a jihar Massachusetts.

Source: Original
Madu limami ne na Diocese na Abakaliki a jihar Ebonyi da ke Kudancin Najeriya, kamar yadda rahoton Vanguard ya ce.
Fasto ya mutu barazanar koro shi daga Amurka
Ya rasu makon jiya bayan ya shafe shekaru yana aiki a matsayin limamin asibiti da kuma faston coci.
Da yake sanar da rasuwarsa, Fasto Jim Achadinha, shugaban al'ummomin Katolika na Gloucester da Rockport, ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi mai matuƙar tayar da hankali.
Achadinha ya ce Madu ya yi wa 'Holy Family Parish da Our Lady of Good Voyage Parish' hidima cikin farin ciki, alheri, kirki da kuma karamci.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, mahukunta ba su bayyana musabbabin rasuwarsa ba.
Sai dai kakakin ofishin babban lauyan yankin Essex ya ce babu alamar cewa wani laifi ne ya haddasa mutuwarsa.
An shirya gudanar da binciken gawa, yayin da jami'ai ke ƙoƙarin tuntubar 'yan uwansa da ke Najeriya domin sanar da su halin da ake ciki.
A cewar rahotanni,Tsaw wani mutum da ya san abin da ya faru ya ce limamin ya mutu ne sakamakon kashe kansa.
Fasto Richard Henning na Archdiocese na Boston ya miƙa ta'aziyya ga iyalai, abokai da duk waɗanda ke jimamin rasuwar limamin.
Ya ce:
"Muna miƙa addu'o'i da ta'aziyya ga iyalansa, abokan aikinsa limamai da abokansa a Najeriya, da kuma mutanen da Fasto Benjamin Madu ya yi wa hidima a asibitin Cape Ann da Salem."

Source: Facebook
Tsawon lokacin da faston ke Amurka
Tun daga shekarar 2021, Madu ya fi yin aiki a matsayin limamin asibitin Salem, tare da hidima a majami'un St. Ann's, Our Lady of Good Voyage da St. Joachim's.
Ranar Talata mai zuwa ce za ta cika shekara 25 da naɗa shi limamin cocin Katolika a St. Theresa Cathedral da ke Abakaliki.
An tsara Madu zai koma Najeriya a wannan wata saboda takardar izinin aikin sa ta R-1 za ta ƙare ranar 29 ga Yulin 2026, cewar Punch.
Jami'an coci sun ce Diocese ɗinsa ta umarce shi ya dawo gida tun farkon watan Yuli maimakon ƙarshen watan kamar yadda aka tsara a baya.
Dokokin shige da fice na Amurka sun wajabta masa barin ƙasar kafin ya sake neman sabunta takardar izinin aikinsa.

Kara karanta wannan
PFIPC: Kamfanin Amurka ya kawo ɗauki ga shugaban hukumar bogi da ake ta surutu a Najeriya
Fasto ya mutu a otal
An ji cewa wani faston ɗariƙar Katolika ya yi bankwana da duniya bayan ya je otal cin duniya da tsinke tare da masoyiyarsa.
Fasto Joseph Kariuki Wanjiku mai shekara 43 a duniya ya kama ɗaki ne a otal ɗin da yammacin ranar Juma'a.
Sai dai, faston ya mutu ne da safiyar ranar Asabar bayan ya kwashe wasu sa'o'i a otal ɗin tare da budurwarsa.
Asali: Legit.ng

