'Ya'yan Tsofaffin Shugaban Kasa da Gwamnoni da Suka Samu Takarar Majalisar Wakilai a APC

'Ya'yan Tsofaffin Shugaban Kasa da Gwamnoni da Suka Samu Takarar Majalisar Wakilai a APC

Abuja, Nigeria - A ranar Asabar, 16 ga watan Mayu, 2026 ne jam’iyya APC mai mulki ta gudanar da zabukan fitar da gwani na yan Majalisar wakilan tarayya a jihohi 36 na Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

APC ta gudanar da zabukan fitar gwani kai tsaye wanda aka fi sani da kato bayan kato, bayan yunkurin cimma matsaya kan ‘yan takara ta maslaha ya ci tura a galibin kujerun siyasa.

Manya.
'Ya'yan tsofaffin gwamnoni biyu, Chinedum Orji da Erhiatake Ibori-Suenu da 'dan marigayi Muhammadu Buhari, Yusuf Hoto: Yusuf Buhari, Erhiatake Ibori-Suenu
Source: Facebook

Jam'iyyar APC ta gudanar da zabukan tsaida gwani

Sakamakon rikicin da ya biyo bayan bin tsarin masalaha, APC ta yanke shawarar shirya zabukan domin tsaida yan takararta na zaben 2027, kamar yadda jaridar Punch ta kawo.

Duk da an samu rikici a wasu jihohin yayin gudanar da zaben fitar da gwani, rahotanni sun nuna cewa kwamitocin da APC ta shirya a mazabun yan Majalisar wakilai sun sanar da wadanda suka samu nasara.

Kara karanta wannan

2027: Tsohon gwamnan Ebonyi zai jagoranci kwamitin tantance masu neman takara a NDC

A sakamakon da aka sanar, an ga ‘ya’yan tsofaffin shugabannnin kasa da tsofaffin gwamnoni sun samu nasara a wasu mazabu, lamarin da ya ba su damar lashe tikitin takarar kujerar majalisar tarayya.

APC ta ba 'ya'yan tsofaffin shugabanni takara

Legit Hausa ta gano vewa zuwa yanzu, ‘ya’yan tsofaffin shugabannin kasa biyu da wasu tsofaffin gwamnoni sun samu tikitin takarar APC a zabukan da aka gudanar ranar Asabar, 16 ga Mayu, 2026. Ga su kamar haka.

1. Yusuf Buhari

Yusuf Buhari, dan marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya zama dan takarar APC a mazabar Sandamu/Daura/Mai’adua ta tarayya a zaben Majalisar Wakilai na 2027.

Muhammadu Buhari ya kasance daya daga cikin fitattun shugabannin Najeriya, inda ya mulki kasar a matsayin shugaban mulkin soja da kuma shugaban kasa na farar hula.

Yusuf Buhari.
Yusuf Buhari, 'dan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari Hoto: Yusuf Buhari
Source: Facebook

Ya rasu a tsakiyar shekarar 2025, sannan aka birne shi a garinsu na Daura. Rasuwarsa ta jawo alhini sosai a fadin kasar, har ma aka ayyana ranar hutun kasa domin jana’izarsa.

Yusuf ya shiga siyasa a hukumance bayan bayyana aniyarsa ta neman kujerar majalisar wakilai a inuwar APC, inda ya samu nasara a zaben da aka gudanar a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Sanata Goje ya sha kaye, ya rasa tikitin APC na komawa Majalisar Dattawa a 2027

2. Olumide Osoba

Olumide Osoba, 'dan tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osoba, ya samu tikitin APC na takarar 'dan Majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Abeokuta North/Obafemi Owoy'de/Odeda.

An fara zaben 'dan tsohon gwamnan a wannan kujera ne a shekarar 2011, sannan aka sake zabensa a 2019 da 2023.

Olumide Osoba
Dan tsohon gwamnan jihar Ogun, Hon Olumide Osoba Hoto: Senator Shuaib Afolabu Salisu
Source: Facebook

Dan majalisar ya samu nasara ne ba tare da hamayya ba a zaben fitar da gwani da aka gudanar a fadin mazabar ranar Asabar da ta gabata, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Idan ya yi nasara a zaben 2027, zai zama karo na hudu da Olumide Osoba zai wakilci mazabar a Majalisar Wakilai.

3. Erhiatake Ibori-Suenu

Erhiatake Ibori-Suenu, diyar tsohon gwamnan jihar Delta, ta samu tikitin APC domin wakiltar mazabar Ethiope ta tarayya a zaben Majalisar Tarayya na 2027.

A yanzu haka tana wa’adinta na farko a Majalisar Wakilai, kuma zaben 2027 zai zama wa'adinta na biyu idan ta samu nasara.

Kara karanta wannan

APC ta sauya sakamakon zabe, an ayyana Yusuf Gagdi a matsayin sahihin ɗan takara

Erhiatake Ibori-Suenu
Diyar tsohon gwamnan jihar Delta kuma yar Majalisar wakilai, Hon. Erhiatake Ibori-Suenu Hoto: Hon. Erhiatake Ibori-Suenu
Source: Facebook

Yar Majalisar ta tabbatar da nasarar da ta samu a zaben fitar da gwanin APC a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Ta ce:

"Ina godiya ga mutanen mazabar Ethiope ta Gabas da ta Yamma, wannan nasara ba tawa ce kaɗai ba, tamu ce baki ɗaya. Yanzu ne lokacin da za mu haɗu wuri guda cikin haɗin kai da manufa ɗaya.

4. Chinedum Orji

Chinedum Orji, 'dan tsohon gwamnan jihar Abia, Theodore Orji, na daga cikin ‘ya’yan tsofaffin gwamnoni da suka samu tikitin APC a zabukan fitar sa gwani na ranar Asabar.

An zabe shi a matsayin dan takarar APC a mazabar Ikwuano/Umuahia ta tarayya a zaben yan Majalisar Wakilai mai zuwa a 2027.

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa APC ta tabbatar da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Abia, Hon Chinedum Orji, a matsayin wanda ya samu nasara a zaben fitar da gwani.

Kara karanta wannan

Zaben Fitar da Gwani: Manyan 'yan majalisa na APC da suka gaza samun tikitin komawa

Chinedum Orji
Tsohon shugaban Majalisar dokokin jihar Abia, Rt. Hon. Chinedum Orji Hoto: Chinedum Orji
Source: Facebook

Sanata Danjuma Goje ya rasa tikitin APC

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Gombe, Danjuma Goje ya rasa tikitin jam'iyyar APC na tsayawa takarar Sanatan Gombe ta Tsakiya karo na biyar a zaben 2027.

DCP Muhammed Ahmed mai ritaya, wanda gwamna Inuwa Yahaya ke goyon baya ne ya samu nasara a zaben fitar da gwanin da aka gudanar ranar Litinin.

Tun da farko dai an zabi Ahmed a matsayin dan takarar masalaha na APC a mazabar Sanatan Gombe ta Tsakiya, amma Danjuma Goje ya nuna bai yarda ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262