Magana Ta Fito kan Zargin Obasanjo Ya Yi wa Tinubu Aiki, An Hada Obi da Kwankwaso
- Kungiyar Yoruba Ronu ta hakikance cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya hada tikitin takarar Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi
- An yi zargin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da yi wa Bola Tinubu aiki a boye domin tazarce a 2027 ta hanyar hada 'yan takarar NDC
- Tsohon mai ba Obasanjo shawara kan harkokin siyasa, Dakta Akin Osuntokun, ya yi magana kan ikirarin cewa Obasanjo ne ya hada tikitin Peter Obi da Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kungiyar Yoruba Ronu Leadership Forum ta zarge shi da yin aiki a boye domin tabbatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu wa'adi na biyu.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar, Akin Malaolu, ya sanya wa hannu ranar Lahadi, 26 ga watan Yuli, 2026 kungiyar ta ce matakan siyasar da Obasanjo ke dauka ba domin karfafa jam'iyyun adawa ba ne, illa raunana su kafin zaben 2027.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa kungiyar ta yi nuni da wasikar da Obasanjo ya aikewa tsohon gwamnan Ogun, Segun Osoba, inda ya zargi tsohon mataimakin shugaban kasa,Atiku Abubakar, da yunkurin tsige shi a baya.
Obasanjo ne ya hada Obi, Kwankwaso - Osunokun
Jaridar Leadership ta kawo labarin cewa tsohon mai ba Obasanjo shawara kan harkokin siyasa, Dakta Akin Osuntokun, ya musanta hakan cewa Obasanjo na yi wa Tinubu aiki a boye.
Amma ya tabbatar da cewa tsohon shugaban kasa ne ya hada Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso suka zama abokan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar NDC.
Amma kungiyar Yarbawa ta ce:
"Abin da mutane ke dauka a matsayin hari kan Atiku, a zahiri hari ne da aka shirya kan jam'iyyun adawa."
Har ila yau kungiyar ta ce bai dace Obasanjo ya ambaci sunan marigayi Na'Abba ba saboda ba ya raye domin kare kansa.
Kiran kungiyar Yarbawa ga Obi
Ta kuma yi ikirarin cewa goyon bayan da Obasanjo ke nuna wa Peter Obi da Kwankwaso wata dabara ce ta boye goyon bayan Tinubu.

Source: Facebook
A cewar kungiyar:
"Da wannan wasika, Obasanjo ya tabbatar da hasashen cewa yana yi wa dan uwansa Bola Tinubu aiki domin ya sake lashe zabe."
Kungiyar ta kara da cewa kafin hadakar adawa ta cimma matsaya kan dandalin siyasa, an tuntubi manyan shugabanni ciki har da Obasanjo, wanda suka ce ya yi kokarin ganin Peter Obi ya zama dan takarar hadakar.
Obi da Kwankwaso na samun karbuwa - Babachir
A baya, mun kawo labarin cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya bayyana ra'ayinsa kan tikitin da zai iya lashe zaben shugaban kasa a babban zaben 2027.
Babachir ya ce haɗakar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a takarar shugaban ƙasa za ta fi samun damar lashe zaɓen 2027 idan aka kwatanta da kowannensu ya tsaya shi kaɗai idan lokaci ya yi.
Ya yi hasashen cewa haɗakar Obi da Kwankwaso za ta samu kashi 70 cikin 100 na damar yin nasara, yayin da Shugaba Bola Tinubu zai samu kashi 50 cikin 100 na samun karbuwa a kasar nan.
Asali: Legit.ng

