Atiku ko Amaechi?: ADC Ta Sanya Ranar da Za Ta Tsayar da Ɗan Takarar Shugaban Kasa
- Kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC ya tantance Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Muhammed Hayatu-Deen
- Ana ci gaba da tattaunawa domin cimma matsaya tsakanin ‘yan takarar kafin zaben fitar da gwani na jam'iyyar da za a yi ranar 25 ga Mayu
- Amaechi da Atiku sun nuna amincewa da tsarin sulhu idan aka gudanar da shi cikin gaskiya da adalci yayin da Hayatu-Deen ya yi martani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC ya tantance tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a Abuja.
Hakazalika, kwamitin ya tantance tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi da kuma babban masanin tattalin arziki, Muhammed Hayatu-Deen.

Source: Twitter
ADC na son fitar da dan takara ta sulhu
An gudanar da tantancewar ne a otel din Transcorp Hilton a ranar Laraba, yayin da ake shirin zaben fitar da gwani na shugaban kasa a ranar 25 ga Mayu, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan
"Ba dan koyo ba"; Atiku ya gano dan takarar da ya cancanci tutar ADC don karawa da Tinubu 2027
Rahotanni sun nuna cewa shugabannin jam’iyyar na ci gaba da tuntubar ‘yan takarar domin cimma matsayar sulhu kafin ranar zaben.
Majiyoyi sun bayyana cewa shugabannin ADC na son kauce wa kashe kudade da wahalhalun gudanar da zaben kato bayan kato.
Da aka tuntubi Sakataren yada labaran jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya ce har yanzu ba a yanke hukunci kan tsarin da za a bi wajen fitar da dan takara ba.
Ya ce:
“Har yanzu ba a yanke hukunci ba.”
Sai dai wata majiya daga jam’iyyar ta bayyana cewa ana tattaunawa da ‘yan takarar domin a samu mafita cikin lumana.
Majiyar ta ce:
“Shugabannin jam’iyyar na tattaunawa tsakaninsu tare da ganawa da masu neman takara domin a warware batun cikin gaggawa.”
Ta kara da cewa idan ba a cimma matsaya ba, jam’iyyar za ta gudanar da zaben kato bayan kato.
Amaechi da Atiku sun yi magana
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, bayan tantancewar, Rotimi Amaechi ya ce zai amince da tsarin sulhu muddin an gudanar da shi cikin gaskiya da adalci.
Ya ce:
“Ni dan jam’iyya ne. Idan hakan ne matsayar jam’iyya kuma kowa ya shiga tsarin, babu matsala.”
Shi ma Atiku Abubakar ya taba bayyana cewa ADC za ta fara kokarin sulhu kafin ta koma zaben kato bayan kato idan hakan bai yiwu ba.
Atiku ya kuma bayyana cewa zaben 2027 zai zama karo na karshe da zai nemi shugabancin Najeriya, sannan zai amince da d'an takarar da jam'iyya ta tsayar.

Source: Twitter
Hayatu-Deen ya yi alkawari
Muhammed Hayatu-Deen ya bayyana ADC a matsayin jam’iyyar da ta fi dacewa wajen kayar da APC tare da kawo mafita ga matsalolin Najeriya.
Ya ce ‘yan Najeriya sun fi bukatar shugabanci mai kawo mafita kan tsadar rayuwa, rashin tsaro da rashin aikin yi.
“Mutane na bukatar shugabanci mai tafiya da gaskiya da dabarun farfado da tattalin arziki da dawo da fata ga jama’a.”
- Muhammed Hayatu-Deen.
Matasa sun yi magana kan siyasar ADC
Wani dan jam'iyyar ADC, Kabir Abdullahi ya tabbatar wa Legit Hausa cewa za su fita su zabi wanda suke ganin ya dace da mulkin Najeriya kuma wanda zai iya kayar da APC.
"Zan fita na yi zabe ranar Litinin, ina ma kowane dan takara fatan alheri amma ni Atiku zan zaba, saboda shi ne dan siyasar da nake ganin zai iya kalubalantar Tinubub a zaben 2027," in ji Kabir Abdullahi.
Abdullahi AA Funtua kuwa, ya ce akwai bukatar 'yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwatarsu su fitar da APC daga mulki a 2027, yana mai cewa:
"Malam kowa a kasar nan yana dakuwa, wallahi yanzu mun wuce shan kida, yanzu mun koma dakuwa kawai alaji. Idan da ace za ka je wani gari da ka kwana biyu ba ka je ba, kila ba za ka iya gane mutane ba, duk sun jejjeme.
"Lallai dole ne talaka ya cire kwadayi, ya fito ya zabi ADC, kai ko ba ADC ba, mu dai a zabi wata jam'iyyar ba APC ba, haba, malam mulki sai ka ce na hauka."
An hana ADC tsayar da 'dan takara?
A wani labari, mun ruwaito cewa, ADC ta musanta rahotannin da ake yadawa cewa ba za ta samu damar tsayar da 'yan takara ba a babban zaben 2027.
Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya ce wadannan labarai ba su da tushe, an kirkire su ne domin haifar da rudani.
Jam’iyyar ta kara da cewa tana ci gaba da gina kanta a matsayin babbar jam’iyyar adawa, tare da mai da hankali kan tattara goyon bayan ‘yan Najeriya.
Asali: Legit.ng

