An Yi Rashi: Babban Malamin Addinin Musulunci Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Yi Rashi: Babban Malamin Addinin Musulunci Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Sheikh Surajudeen Akanni, wanda aka fi sani da Arizukuna, ya yi bankwana da duniya bayan gajeriyar rashin lafiya
  • Malamin addinin Musuluncin ya rasu ne da yammacin ranar Talata, 28 ga Yulin 2026, kuma aka yi jana'izarsa ranar Laraba, 29 ga watan Yulin 2026
  • Matar fitaccen mawakin Fuji, Kwam 1, ta bayyana Arizukuna a matsayin uba a gare ta yayin da ta yi masa ta'aziyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Oyo - Sheikh Surajudeen Akanni, wanda aka fi sani da Arizukuna, ya rasu bayan ya yi gajeriyar rashin lafiya.

Legit.ng ta rahoto cewa malamin addinin Musuluncin ya rasu ne da yammacin ranar Talata, 28 ga Yulin 2026.

Sheikh Arizikunna ya rasu
Marigayi Sheikh Surajudeen Arizikunna Hoto: Ola Kunle
Source: Facebook

Legit Hausa ta fahimci cewa an yi jana'izarsa ranar Laraba, 29 ga Yulin 2026, bisa koyarwar addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

'Babu yan bindiga a Niger': Gwamnati ta gano yadda aka samu rashin tsaro

Arizukuna ya kasance babban jagoran addini na kasa na Hizbullah International Prayer Ministry, sannan yana rike da sarautar Amir Zakireen na jihar Oyo.

Haka kuma, ya kasance aminin fitaccen mawakin Fuji, Wasiu Ayinde, wanda aka fi sani da Kwam 1.

Malamin Ondo Ya Yi Ta'aziyya

Ofishin Babban Limamin Masarautar Akure, Sheikh Abdulhakeem Akorede, ya fitar da sakon ta'aziyya, inda ya bayyana rasuwar a matsayin abin bakin ciki matuka.

Sheikh Akorede ya ce:

"Muna rokon Allah Madaukakin Sarki (SWT) Ya gafarta masa dukkan kura-kuransa, Ya karbi kyawawan ayyukansa, Ya yalwata kuma Ya haskaka kabarinsa, Ya kuma ba shi matsayi mafi daukaka a Aljannar Firdausi."
"Muna kuma rokon Allah Ya ba iyalansa da masoyansa da iyalan Hizbullah da daukacin al'ummar Musulmi karfi da hakuri da juriyar jure wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba. Hakika, daga wajen Allah muke, kuma gare Shi za mu koma."

Kara karanta wannan

Rai baƙon duniya: Tsohon alkalin Babbar Kotun Tarayya ya rasu a Borno

Matar Kwam 1 Ta Yi Alhini

A nata bangaren, Emmanuella Ropo, matar Kwam 1, ita ma ta yi ta'aziyyar marigayin malamin a j a ranar Laraba, 29 ga Yulin 2026.

Ta bayyana Arizukuna a matsayin tamkar uba a gare ta, inda ta rubuta:

"Ka huta lafiya, Sheikh Surajudeen Arizukuna, 'babana' kamar yadda na saba kiranka. Rasuwar babban mutum irinka ta zo mana da matukar kaduwa."
"Ka kasance fiye da abin koyi a gare ni. Ka rungume ni tamkar 'yarka, kuma ka bar wani tarihi da ba zan taba mantawa da shi ba a rayuwata. Duk da cewa rasuwarka ta taba zuciyata sosai, ina samun nutsuwa da kwanciyar rai a cikin ikon Allah Madaukakin Sarki."
"Allah Ya gafarta maka kura-kuranka, Ya ba ka Aljannar Firdausi, Ya kuma ba mu, masoyanka, ikon jure wannan rashi. Za ka ci gaba da kasancewa a cikin addu'o'ina har abada."
Sheikh Arizikunna ya bar duniya
Taswirar jihar Oyo, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ropo ta kara da cewa:

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Allah Ya ba shi matsayi mafi daukaka a Aljanna, Ya kuma sanyaya zuciyar kowa da ke alhinin wannan babban rashi."

Kara karanta wannan

Netanyahu zai gana da Trump bayan tsagaita wuta, an ji abin da za su tattauna

Tsohon alkalin babbar kotu ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon alkalin Babbar Kotun Tarayya, mai shari'a Babagana Ashigar, ya rasu a garin Maiduguri da ke Borno bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Babbar Kotun Tarayya ta mika ta'aziyya ga iyalan Babagana Ashigar da ya rasu tare da addu'ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com