Rikici Ya Barke a Zaben Fitar da Gwani na APC, An Tarwatsa Masu Kada Kuri'a
- Rikici ya barke yayin zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC a Legas kafin fara kada kuri’a domin zaben tikitin majalisar tarayya
- Magoya bayan wasu ‘yan takara ne suka tayar da tarzoma tare da tilasta masu kada kuri'a guduwa domin tsira da rayukansu
- Mambobin jam’iyyar sun bukaci shugabanni da jami’an tsaro su tabbatar da zaman lafiya da gudanar da sahihin zabe a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Legas - Rikici ya barke ranar Asabar yayin gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Mushin da ke jihar Legas.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne kafin a fara kada kuri’ar zaben fidda gwani na kujerar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Mushin Constituency II.

Source: Twitter
Mutane sun tsere daga wajen taro

Kara karanta wannan
An kama dattijo da ya shiga asibitin Funtua da niyyar satar mahaifar sabon jariri
Wakilin kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) da ke wurin taron ya ce an shiga rudani ne bayan samun sabani tsakanin magoya bayan wasu daga cikin ‘yan takarar.
Rikicin ya haddasa turmutsitsi yayin da wakilai da magoya bayan jam’iyyar suka rika guduwa domin neman tsira daga hare-haren 'yan bangar siyasar.
Har zuwa lokacin da kamfanin dillancin labaran ya fitar da rahoton, ba a fara gudanar da zaben ba yayin da hankula suka ci gaba da tashi a wajen taron.
Manyan ‘yan takara a zaben APC
Daga cikin fitattun ‘yan takarar da ke neman tikitin jam’iyyar akwai Hon. Seye Oladejo da kuma dan majalisa mai ci, Hon. Oluwatoyin Fayinka, wanda ke neman sake komawa kujerarsa.
Sauran ‘yan takara ma sun halarci zaben fidda gwanin domin neman wakiltar jam’iyyar APC a babban zaben shekarar 2027.
Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun nuna damuwa kan rikicin tare da kira ga shugabannin jam’iyyar da jami’an tsaro su tabbatar da zaman lafiya da gudanar da sahihin zabe.

Source: Twitter
Jam’iyyar APC ba ta yi magana ba
Sun ce wajibi ne jam’iyyar ta tabbatar da adalci da gaskiya domin kaucewa rikice-rikice yayin shirye-shiryen babban zaben kasa mai zuwa.

Kara karanta wannan
2027: Tsohon shugaban a INEC ya samu tikiti, zai tsaya takarar gwamnan Yobe a ADC
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, jami’an APC ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da abin da ya faru.
Jam’iyyar APC na gudanar da zabukan fitar da gwani a sassa daban-daban na Najeriya domin tantance wadanda za su tsaya mata takara a babban zaben shekarar 2027.
Rigima ta barke a zaben APC Kaduna
A wani labari, mun ruwaito cewa, jam’iyyar APC ta shiga rikici a Igabi bayan fusatattun matasa sun nuna rashin amincewa game da zaben fitar da gwani a Kaduna.
Matasan sun tilasta wa shugaban jam’iyyar Bashir Jibrin Jaji shiga mota saboda zargin magudin zaɓe.
Sun ce ba a tantance masu kaɗa ƙuri’a ko ƙirga ba kafin jami’an jam’iyya su bayyana Hussaini Jalo a matsayin wanda ya yi nasara.
Asali: Legit.ng