An Fadi Sunayen 'Yan Ta'adda 5 da aka Kama Suna Sace Dalibai da aka Je Kotu
- Hukumar DSS ta gurfanar da wasu mutum biyar da ake zargi mambobin ƙungiyar Ansaru ne kan sace ɗalibai da malaman Oyo
- Gwamnatin tarayya ta zarge su da laifuffukan ta'addanci, haɗa baki, taimaka wa ta'addanci da kuma ɓoye bayanan hare-hare
- Kotun tarayya da ke Abuja ta umarci a ci gaba da tsare waɗanda ake zargin a hannun DSS har zuwa ranar fara shari'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da wasu mutum biyar da ake zargi mambobin ƙungiyar Jama’atu Ansarul Muslimina fi-Biladis Sudan (Ansaru) ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Ana tuhumar mutanen ne da hannu a harin da aka kai makarantu a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo a ranar 15 ga watan Mayun 2026, wanda ya yi sanadin sace ɗalibai da malamai tare da kashe mutum biyu.

Source: Getty Images
Punch ta rahoto cewa dukkan waɗanda ake tuhumar sun musanta laifuffuka shida da suka haɗa da ta'addanci, haɗa baki domin aikata ta'addanci, taimaka wa ta'addanci da kuma ɓoye muhimman bayanai.
Su waye ake tuhuma?
Waɗanda aka gurfanar sun haɗa da Mahmud Muhammad wanda aka fi sani da Abu Bara'a da Abbas Mukhtar, Abubakar Abbas wanda aka fi sani da Isah Adam da Malam Mahmuda Al-Nigeri.
Sauran sun hada da Abdulrazak Umar (Abu Khalifa ko Abu Khalid), Yunusa Musa (Abu Yunusa Bin Musa) da Shamsu Adamu Sani (Abu Itisar).
Takardar tuhumar ta ce:
"Kun ba mambobin ƙungiyar Ansaru umarni cewa idan gwamnati ta kama ku, su riƙa yin garkuwa da mutane tare da kashe su domin tilasta gwamnati ta amince da buƙatunku."
An zarge su da kisa
Masu gabatar da ƙara sun kuma bayyana cewa harin da aka kai makarantu a Oriire ya yi sanadin mutuwar Michael Oyedokun da Deacon John Olaleye.
A cewar takardar tuhuma, an kashe mutanen biyu ne ta hanyar sare musu kai bayan an yi garkuwa da su a ranar 15 ga Mayu, 2026.
Haka kuma DSS ta zargi waɗanda ake tuhumar da ɓoye bayanai kan shirin kai harin ta'addanci da kuma kin sanar da jami'an tsaro, yayin da aka ƙara tuhumar Umar, Musa da Sani da haɗa baki da taimakawa wajen sace mutanen da kashe su.
Kotu ta umarci a tsare su
Bayan sun musanta zarge-zargen, lauyan gwamnati, Dr. Caliatus Eze, ya roƙi kotun ta ba da umarnin ci gaba da tsare su a hannun DSS har zuwa lokacin fara shari'a.
Vanguard ta rahoto cewa mai shari'a Salim Ibrahim ya amince da buƙatar, tare da umartar a ci gaba da tsare su a hannun DSS.

Source: Twitter
Daga nan kotun ta ɗage sauraron shari'ar zuwa ranar 25 ga Satumban shekarar 2026 domin fara shari'a.
Rundunonin sojin Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar sojin Najeriya ta sanar da naɗin sabbin Janar-Janar masu jagorantar sababbin rundunonin soja da aka kafa a sassa daban-daban na ƙasar.
Matakin ya biyo bayan amincewar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ƙara yawan rundunonin sojin Najeriya daga takwas zuwa 12 domin ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro.
Babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ce rundunonin za su fara aiki nan take bayan sun kai matakin farko na shirye-shiryen gudanar da ayyukansu.
Asali: Legit.ng


