Mamaki Ya Kama Ƴan Najeriya bayan Ganin Kwamishinan Yan Sanda a Taron Tinubu, APC

Mamaki Ya Kama Ƴan Najeriya bayan Ganin Kwamishinan Yan Sanda a Taron Tinubu, APC

  • Wani bidiyon da ya bazu a kafofin sadarwa ya jawo maganganu bayan ganin Kwamishinan 'Yan Sandan a taron APC
  • An gano kwamishinan yan sandan jihar Legas, CP Tijani Fatai, ya halarci bikin rantsar da shugabannin City Boy Movement a Ikeja, lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce
  • Jam'iyyar NDC ta soki halartar kwamishinan, tana zargin hakan na iya nuna son kai, tare da neman a dakatar da shi kafin zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya jawo magana yayin bikin ƙungiyar City Boy a jihar Lagos.

Bidiyon ya haddasa muhawara bayan ya nuna Kwamishinan 'Yan Sandan Legas, CP Tijani Fatai, yana halartar bikin rantsar da kwamitin zartarwar ƙungiyar reshen Lagos.

An gani kwamishinan yan sanda a taron goyon bayan Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da kwamishinan yan sanda a Lagos. Hoto: Bayo Onanuga, City Boy Movement.
Source: Facebook

A cikin bidiyon, an ga CP Tijani yana isa wurin taron da ke Ikeja, yana gaisawa da manyan baki tare da zagayawa cikin taron tare da jami'an tsaro da sauran mahalarta, cewar Punch.

Kara karanta wannan

"Dole mu yi nasara," APC ta dauki babban mataki kan zaben gwamnan jihar Osun

A wani bidiyon kuma, an ga kwamishinan cikin cikakken kayan aikinsa yana tattaunawa da mahalarta taron da ke sanye da hula mai tambarin yakin neman zaben Shugaba Bola Tinubu da kuma haruffan ST, da ake dangantawa da Seyi Tinubu.

Mai gabatar da taron ya yi maraba da kwamishinan inda ya ce, "Ga CP Tijani Fatai tare da tawagarsa. Muna yi musu maraba."

City Boy Movement wata kungiyar matasa ce da ke goyon bayan manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu.

Kungiyar na mayar da hankali kan wayar da kan matasa da tattara goyon baya ga 'yan takarar APC gabanin babban zaben 2027.

An ruwaito cewa, a wajen kaddamar da reshen Legas, mambobin kungiyar sun yi alkawarin tattara miliyoyin kuri'u daga yankin Kudu maso Yamma domin marawa jam'iyyar baya.

Jam'iyyar adawa ta NDC ta fitar da sanarwa tana Allah wadai da halartar CP Tijani a taron, tana cewa hakan ya tayar da tambayoyi kan rashin nuna tsaka-tsaki da kuma yiwuwar son kai yayin gudanar da ayyukansa a lokacin zabe.

Jam'iyyar ta bukaci rundunar 'yan sandan Najeriya ta dakatar da kwamishinan tare da daukar matakin ladabtarwa a kansa.

Kara karanta wannan

Iyalin El Rufai sun yi magana kan wasikar da aka ce ya aika wa jam’iyyar ADC

Haka kuma ta nemi rundunar ta tabbatar da cikakken adalci a zaben 2027 da kuma kare masu kada kuri'a da magoya bayan sauran 'yan takara.

Lamarin ya jawo muhawara a kafafen sada zumunta, inda wasu suka ce bai dace jami'in dan sanda mai mukami ya halarci taron da ake dangantawa da jam'iyya mai mulki ba.

Sai dai wasu sun kare kwamishinan, suna cewa halartarsa na da alaka da tabbatar da tsaro da zaman lafiya. Jigon APC Bashir Ahmad ya ce idan aka gayyace shi kuma yana da lokaci, zai iya halarta domin tabbatar da doka da oda, ba wai don shiga harkokin kungiyar ba.

Har zuwa safiyar Laraba, rundunar 'yan sandan Legas da hedikwatar rundunar 'yan sandan Najeriya ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan bidiyon ko bukatun da jam'iyyar NDC ta gabatar ba.

Akpabio ya fadi yadda Tinubu zai ci zaɓe

Mun ba ku labarin cewa shugaban majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya ce kungiyar City Boy za ta taka rawa wajen tabbatar da sake zaben.

Shugaba Bola Tinubu a 2027 Akpabio ya ce kungiyar za ta tabbatar shugaban kasa ya samu wakilai a dukkan rumfunan zabe domin kare kuri'un da za a kada masa a fadin Najeriya.

Ya bukaci mambobin kungiyar su ci gaba da wayar da kan masu zabe tare da yin watsi da duk zarge-zargen da za su biyo bayan sakamakon zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.