Kungiyar Kiristoci Ta Fadi Abin da Take Nema daga wajen Tinubu a 2027
- Northern Christian Progressive group tana barar kujerar shugaban yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a 2027
- Sakataren ƙungiyar, Rabaren Hayap Musa Danladi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar
- Ya bayyana cewa wannan shi ne lokacin da ya dace Kiristocin Arewa za su nuna ƙarfin siyasarsu da amannarsu da APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Yayin da ake shirye-shiryen zaben 2027, wata kungiyar Kiristoci a Najeriya ta bukaci a taimaka mata da kujerar kamfe.
Wannan kungiya tana so a nada kirista ya zama shugaban yakin neman zaben Bola Tinubu domin ganin APC ta samu nasara.

Source: Getty Images
Kiristoci na son kujerar shugaban yakin zabe
Rabaren Hayap Musa Danladi ya yi wannan kira a madadin kungiyarsu a ranar Alhamis kamar yadda labarin ya zo a jaridar Leadership.
Sakataren kungiyar kiristocin yana so a ba su wannan kujera ne domin su nuna irin nauyinsu a filin zabe da kuma amanarsu da APC.
Northern Christian Progressive group ta ce lokaci ya yi da kiristocin Arewa za su nuna karfinsu a wajen zaben shugaban Najeriya.
Jawabin kungiyar kiristocin Arewa
An rahoto sakataren Northern Christian Progressive group yana cewa:
“Muna rokon shugaban kasa Bola Tinubu ya yi tunanin nada fitaccen ‘dan siyasa daga Arewacin Najeriya, kamar yadda aka yi a zaben 2023 da aka nada tsohon gwamnan Filato, Solomon Lalong, ya jagoranci yakin neman zabe.
“Muna sa rai cewa Lalong, da irin kwarewarsa da farin jininsa da ya ratsa ko ina, ya bada gudumuwa wajen nasarar Bola Tinubu a zabe.
Kungiyar Northern Christian Progressive group ta ce yin hakan zai rufe bakin wasu ‘yan siyasa da ke zargin shugaban kasar da nuna wariya.
The Nation ta ce kiristocin sun tuhumi ‘yan adawar shugaba Bola Tinubu da yada karya su yi masa sharri.
Idan mabiyin addinin kirista ya zama sarkin yakin neman zaben Bola Tinubu, kungiyar ta ce hakan zai sa a kara fahimta da mutunta juna.
"Bada wannan kujera ga kiristan Arewa zai karfafa yakin neman zaben kuma ya warware duk wasu zargi da sharrin da ‘yan adawa a siyasa suke yi wa shugaban kasa na nuna wariya.”

Kara karanta wannan
Sai bango ya tsage: Yadda APC ke ta yi wa Kwankwaso illa sakamakon rikicin NDC a Kano

Source: Getty Images
- Northern Christian Progressive group
Hayap Musa Danladi ya ce kiristoci za su yi aiki tukuru wajen tallata Bola Tinubu, su fito da ayyukan da ya yi wajen sauya kasar nan.
Haka kuma an yi wa kiristocin huduba su ajiye kabilanci da kiyayyar addini a zaben 2027.
Gwamnatin Bola Tinubu ta sha suka a Amurka
Sanata Ted Cruz ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan zargin kisan kiristoci a Najeriya, an rahoto cewa yana nan a kan bakarsa har gobe.
Cruz ya ce a maimakon maganace matsalar, gwamnatin tarayya ta maida abin yakin baka, ba a dage wajen kare rayuka da dukiyar kiristoci ba.
Sanatan Amurkan ya soki jami’an gwamnatin Najeriya, ya dage a batun gallaza wa kiristoci da aka taso da batun a majalisar dokokin kasar.
Asali: Legit.ng
