Fact Check Africa Ta Yi wa Matasa Horo a Arewa domin Tunkarar Karyayyaki a Zabe
- Kungiyoyin FIAP da FactCheckAfrica sun gudanar da horo ga masu fada - a ji a kafafen sada zumunta a Arewa
- Taron yana da nufin yaki da labaran karya saboda ganin an gudanar da babban zaben shekarar 2027 cikin lumana
- Matasa da mata 30 daga Arewacin Najeriya aka koya wa dabarun amfani da fasahar zamani wajen tantance bayanai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Fundación para la Internacionalización de las Administraciones Públicas da aka fi sani da FIA ta shirya horo na musamman a Arewacin Najeriya.
Cibiyar da hadin-kan abokiyar mu’amalarta, FactCheckAfrica ta horar da matasa na tsawon kwanaki uku domin ganin an yaki yada karyayyaki lokacin zabe.

Source: Twitter
FactCheck Africa ta horar da mutane a Kano
Legit Hausa tana da labarin FactCheckAfrica ta tara masu fada-a ji a kafafen zamani a garin Kano, ta fadakar da su, ganin an fara shirin tunkarar zaben 2027.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: An hango yadda malaman makaranta masu yawa za su ajiye aiki a Borno
Ganin yadda yada labaran bogi ya zama ruwan dare, an horar da mutane 30 game da yadda za a dage da tantanc labarai da bankado bayanan da ba su tabbata ba.
An zakulo wadannan mutane da suka yi fice a shafukan Facebook, X (Twitter), Tik Tok, Instagram har da LinkedId ganin irin tasirin da suke da shi a kafofin nasu.
Kafin nan cibiyar ta shirya irin wannan taro na musamman a garin Enugu ga takwarorinsa a Kudancin Najeriya saboda a iya inganta harkar zabe a kasar nan.
Hadarin labaran bogi da na kiyayya a Najeriya
Manufar taron ita ce ganin an tsabtace labaran da suke yawo kuma a yi zabe cikin lumana.
A yau, labarai na karya da na kiyayya sun karade shafukan sada zumunta kuma ana amfani da su wajen hargitsa gari da haifar da rashin zaman lafiya.
Maimakon a yi amfani da kirkirarriyar fasaha ta AI yadda ya dace, ana cin moriyarsu wajen kirkirar bidiyoyi, sauti da hotuna na karya sosai a Najeriya.
Mahalarta zaman da aka shirya sun samu karin kwarewa wajen tantance labarai, yin bincike a kafofin zamani da amfani da fasahar AI wajen gano gaskiya.
A karshe kuwa, wadanda suka halarci taron na kwanaki a jere sun kirkiri bidiyo da za a yada a yankin Arewacin Najeriya da nufin inganta sha’anin zabe.
Cibiyar Fact Check Afrika ta tattaro kwararru a bangaren tantance bayanai, ilmin sadarwa, aikin jarida da yada labarai da aikin wanzar da zaman lafiya.
Bayan haka an koya wa mahalartan sanin yadda sakonni suke karada shafukan da sada zumunta da kuma irin salon da za a bi wajen bada labari da kyau.
Dukkan masu fada-a jin sun yi alwashi za su bi ka’ida da sharudan yada labarai a shafukansu.
Kokarin da Fact Check Africa take yi
An yi wa taron take da #CheckBeforeYouPost wanda yake nufin a tantance bayanai kafin a yada su kuma tuni sakon ya fara zagaya shafukan sadarwa.
Abideen Olasupo, wanda shi ne ya assasa FactCheckAfrica ya ce an shirya taron ne ganin yadda al’umma suka yi amanna da mahalartan.
Mista Abideen Olasupo ya ce baya ga Kano, za a shirya irin wannan horo karo na uku da zai tattaro mutane daga Najeriya da kasashen ketare.

Source: Facebook
Baya ga wannan shiri ta karkashin gudumuwar da EU ta ke ba kungiyar ECOWAS, FIAP da ke kasar Sifen tana aiki da kasashen fiye da 120.
Abin da mahalarta taron suka fada
Hannatu Bilyaminu wanda ta zo daga Jigawa ta halarci taron, ta bayyana cewa ta karu sosai musamman wajen sanin yadda karya ta ke yawo.
Ta ce ta ji dadin salon da aka bi wajen koyar da su a aikace kuma ta fahimci dabarun tantance bayanai da yadda za a rika kirkirar masu inganci.
Ganin yadda aka jawo mutane daga Kaduna, Sokoto, Kwara, Neja, Nasarawa, Filato da sauran jihohi yana cikin abubuwan da suka kayatar da ita.
Dr. Hadiza Shettima Lawan ta samu masaniya game da nau’o’in bayanan karya, kuma ta ce:
"Aiki da mahalarta daga fadin jihohin Arewacin Najeriya ya sa abin ya kara armashi.
"Yin aiki da mutanen da ke sha’awar amfani da kafofin sada zumuntarsu wajen yada gaskiya, zaman lafiya da yadda sakonni yadda ya kamata musamman da zabe ya gabato ya ba ni kwarin guiwa."
Gwamnatin Kano za ta sallami mutane 1, 400
Rahoto ya zo kafin yanzu cewa Gwamnatin Jihar Kano ta amince da biyan mutane fiye da 1,400 tsabar kudi saboda aiki ya shafi kadarorinsu wajen ginin hanyoyi.
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta amince da biyan ƙudin diyya ga mutane sama da 1,300 da ayyukan fadada tituna suka shafi wurarensu.
Haka zalika, gwamnatin za ta tura ƙuɗaɗen diyyar ƙai tsaye zuwa asusun bankunansu gami da ba su filaye kyauta domin sake gina muhallansu da za a ruguza
Asali: Legit.ng


