Rigima Ta Barke bayan Zaben Fitar da Gwanin APC, An Kashe Mutum 1 a Jihar Kaduna

Rigima Ta Barke bayan Zaben Fitar da Gwanin APC, An Kashe Mutum 1 a Jihar Kaduna

  • An kashe matashi a rigimar da ta biyo bayan zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC a mazabar Sabon Gari da ke jihar Kaduna
  • Mahaifin wanda aka kashe, Malam Yusuf Abdullahi ya bukaci a gudanar da bincike tare da kama wadanda suka aikata wannan aika-aika
  • Babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar yan sandan jihar Kaduna ko gwamnati kan abin da ya faru bayan zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Rigingimu na ci gaba da dabaibaye wuraren zabukam fitar da gwanin jam'iyyar APC mai mulki, lamarin har ya kai ga rasa rai a jihar Kaduna.

Rahoto ya nuna cewa an kashe mutum daya tare da raunata wasu mutane 12 sakamakon rigimar da ta biyo bayan zaben fitar da gwanin APC a mazabar Sabon Gari, Kaduna.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya gana da Bola Tinubu yayin da rigingimu suka dabaibaye jam'iyyar

Kaduna.
Taswirar jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Aminiya ta kawo rahoton da ke nuna cewa zaben fitar da gwanin APC a mazabar Sabon Gari ya gudana ne tsakanin manyan yan takara biyu, Nasiru Idris da Bashir Zango.

Bayan kammala kada kuri'u kamar yadda APC ta tsara, kwamitin shirya zaben ya sanar da cewa Idris ya samu nasara da ƙuri’u 853, yayin da Zango ya samu ƙuri’u 213.

Yadda rikicin ya ɓarke a Kaduna

Bayanai sun nuna cewa rikicin ya ɓarke ne tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu bayan bayyana sakamakon zaɓen.

An ce wannan rigima ce ta yi sanadin mutuwar wani matashi mai suna Abdulmutallab Yusuf daga Unguwar Gwado, tare da jikkata wasu da dama.

Wannan lamari ya girgiza iyalan wanda ya kashe, inda mahaifin matashin mai suna Malam Yusuf Abdullahi, ya ce yana gida lokacin da aka sanar da shi cewa an harbi ɗansa a ƙirji.

Magidancin ya ce:

"Ban bata wani lokaci ba, na kama hanya domin zuwa na ga halin da yake ciki, sai aka fada miki cewa an wuce da shi asibiti, ina isa can aka nuna mini gawarsa,"

Kara karanta wannan

Ribas: Mutumin Wike na dab da zama 'dan takarar gwamnan APC bayan Fubara ya janye

Mahaifin mamacin ya nemi adalci

Malam Yusuf Abdullahi ya bayyana cewa marigayin ba ɗan siyasa ba ne, kuma yana taimaka masa wajen sayar da magungunan gargajiya a kasuwannin da ke kewaye da Zariya.

Ya ce an harbe ɗansa ne a Mahaɗar Unguwar Gwado, wuri da ba a gudanar da zaɓen fitar da gwanin ba, yana mai cewa har yanzu babu wani dan siyasa ko jami'in gwamnati da ya zo masa ta'aziyya.

Magidancin ya roƙi hukumomin tsaro da su gano tare da kamo duka waɗanda suka aikata kisan domin a yi wa ɗansa da aka kashe haka kurum adalci, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Tutar ApC.
Tutar jam'iyya mai mulkin Najeriya Hoto: APC Nigeria
Source: Twitter

Da aka tuntubi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce yana cikin taro kuma ba zai iya yin magana kan lamarin ba a lokacin da ake tattara rahoton.

Dan Majalisa ya sha da kyar a Taraba

A wani labarin, kun ji cewa 'dan Majalisar wakilai daga jihar Taraba, Hon. Sadiq Tafida ya sha da kyar a hannun matasa lokacin da ya koma mazabarsa don neman goyon baya.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya hakura da takara, ya janye daga zaben fitar da gwanin APC

Lamarin ya faru ne a makarantar Raddai Metropolitan School da kebrinin Jalingo a yammacin ranar Asabar yayin gudanar da zaben fitar da gwanin APC.

Sai dai wasu majiyoyi sun ce an samu kwantar da tarzomar ne bayan shugaban karamar hukumar Jalingo, Hon. Nura Dantsoho, ya shiga tsakani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262