Rundunar Soji Ta Nada Sababbin Kwamandoji domin Yakar Rashin Tsaro
- Babban Hafsan Sojin Kasa ya amince da nada sabbin manyan kwamandoji bayan gwamnatin Tinubu ta amince da kirkirar rundunonin soja guda hudu
- Sabbin rundunonin za su fara aiki nan take domin fadada ayyukan soja, inganta tsaro da kuma kara karfin mayar da martani kan barazanar tsaro
- Sabon tsarin ya sake raba yankunan da rundunonin soja za su kula da su a fadin Najeriya domin inganta jagoranci da gudanar da ayyuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya amince da nada sababbin kwamandojin rundunonin soja bayan amincewar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na kirkirar rundunonin soja guda hudu.
An bayyana cewa matakin na daga cikin kokarin fadada karfin rundunar sojin kasa, inganta jagoranci da kuma kara karfin mayar da martani kan kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta.

Kara karanta wannan
'Ba Abuja ba ne,' 'Yan sanda sun gano jihar da 'yan ta'adda suka kashe babban soja

Source: Twitter
A cikin wata sanarwa da mukaddashiyar daraktar hulda da jama'a ta rundunar soja, Kanal Appolonia Anele ta fitar a Facebook, ta ce rundunonin za su fara aiki da zarar sun kai matakin farko na shirye-shiryen gudanar da aiki.
Rundunonin da aka kirkira
Sanarwar ta bayyana cewa an sake tsara yankunan da kowace rundunar soja za ta kula da su domin inganta ayyukan tsaro a fadin kasa.
Runduna ta 1 mai hedikwata a Kaduna za ta kula da jihohin Kaduna, Kano, Katsina da Jigawa, yayin da Runduna ta 2 da ke Ibadan za ta kula da Oyo, Osun, Ekiti da Ondo.
Runduna ta 3 da ke Jos za ta kula da Plateau, Bauchi da Gombe, yayin da sabuwar Runduna ta 5 da ke Makurdi za ta kula da Benue, Nasarawa da Kogi.
Haka kuma Runduna ta 6 da ke Fatakwal za ta kula da Rivers, Akwa Ibom da Cross River, Runduna ta 7 da ke Maiduguri za ta kula da Borno da Yobe, yayin da Runduna ta 8 da ke Sokoto za ta ci gaba da kula da Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: An hango yadda malaman makaranta masu yawa za su ajiye aiki a Borno
Sabuwar Runduna ta 9 da ke Ilorin za ta kula da Kwara da Neja, Runduna ta 10 da ke Jalingo za ta kula da yankunan kan iyakar Taraba da Adamawa, yayin da Runduna ta 81 da ke Legas da Runduna ta 82 da ke Enugu za su ci gaba da kula da yankunansu.
An kuma bayyana cewa Runduna ta 83 mai hedikwata a Benin za ta fara aiki daga baya a wannan shekara domin kula da Edo, Delta da Bayelsa.

Source: Facebook
An nada sabbin kwamandoji
Vanguard ta rahoto cewa babban Hafsan Sojin Kasa ya kuma amince da nada manyan hafsoshi domin jagorantar sababbin rundunonin.
Manjo Janar Yakubu Yahaya zai jagoranci Runduna ta 9 da ke Ilorin tare da zama kwamandan Operation SAVANNA SHIELD, yayin da Manjo Janar Chinedu Ralph Nnebeife zai jagoranci Runduna ta 10 da ke Jalingo.
Haka kuma Manjo Janar Moses Gara zai jagoranci Runduna ta 5 da ke Makurdi tare da zama kwamandan Operation WHIRL STROKE, yayin da Manjo Janar Auwalu Mahmuda zai jagoranci Runduna ta 2 da ke Ibadan.
Babban Hafsan Sojin Kasa ya taya sabbin kwamandojin murna tare da bukatarsu su jagoranci rundunoninsu da kwarewa, su tabbatar da da'a da inganta ayyukan tsaro.
Maganar kashe sojan Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya ta musanta rahotannin da ke cewa an kai hari kan wani Kanal na soja a Abuja.
Rundunar ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a garin Badna da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa, ba a cikin Abuja ba.
Ta kuma gargadi kafafen yada labarai da masu amfani da shafukan sada zumunta da su rika tantance bayanan tsaro kafin wallafawa domin kauce wa jefa jama'a cikin firgici.
Asali: Legit.ng
