'Yan Bindiga Sun Shiga Kotu Suna Harbi, Alkali Ya Tsere Ta Taga a Katsina

'Yan Bindiga Sun Shiga Kotu Suna Harbi, Alkali Ya Tsere Ta Taga a Katsina

  • Wani alƙalin kotun Shari'a a ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina ya tsallake rijiya da baya bayan 'yan bindiga sun kai hari kotun
  • Rahotanni sun ce alƙalin ya tsere ta taga kafin maharan su shiga kotun, inda suka riƙa harbe-harbe suna neman inda yake
  • Lamarin ya sake ƙara fargaba a Katsina, shekaru biyar bayan da wasu 'yan bindiga suka sace wani alƙalin kotun Shari'a yayin zaman kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Katsina – Wani alƙalin kotun Shari'a mai suna Mohammed Muktar ya tsallake rijiya da baya bayan wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai hari kotun Shari'a da ke ƙauyen Gwarjo a ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai harin ne da tsakar rana a ranar Laraba, inda suka shiga harabar kotun suna harbe-harbe tare da tambayar inda alƙalin yake.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi mutane har cikin masallaci sun bindige su a Sokoto

Taswirar jihar Katsina
Taswirar jihar Katsina a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Daily Trust ta rahoto cewa alƙalin ya hango maharan tun kafin su iso kotun, lamarin da ya ba shi damar tserewa ta taga kafin su shiga cikin kotun.

Yadda alƙalin ya kuɓuta

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa alƙalin ya samu taimakon wani ɗan acaba bayan ya tsallake ta taga.

Majiyar ta ce:

"'Yan bindigar sun shiga kotun suna ta harbe-harbe ba tare da ƙa'ida ba, suna tambayar ina alƙalin yake. Amma cikin sa'a ya riga ya tsere ta taga, sannan wani ɗan acaba ya taimaka masa ya gudu kafin su iso."

Wani shaidar gani da ido kuma ya ce maharan sun fusata bayan sun gano cewa alƙalin ya tsere.

A cewarsa, sun yi barazanar kashe alƙalin idan ya sake dawowa domin ci gaba da zaman kotu a ƙauyen.

An shiga fargaba a yankin

An ce harin ya ƙara jefa mazauna Gwarjo cikin fargaba, kasancewar yankin ya sha fama da hare-haren 'yan bindiga a lokuta da dama.

Kara karanta wannan

An maka shugabannin APC 35 a kotu kan 'ɓata' sunan gwamna da kwamishinarsa

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, bai yi nasara ba, domin bai amsa kira ko saƙonnin da aka tura masa ba.

Gwamna Dikko Umaru Radda
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda a wajen taro. Hoto: Ibrahima Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Wannan lamari ya tuna wa mutane wani hari makamancin wannan da ya faru a shekarar 2021 a ƙauyen Bauren Zakka da ke ƙaramar hukumar Safana.

A wancan lokacin, AIT ta rahoto cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari kotun Shari'a yayin zaman kotu, inda suka sace alƙali Husaini Sama'ila bayan sun shiga kotun suna harbe-harbe.

An kashe 'yan bindiga a Katsina

A wani labarin, mun ruwaito cewa sama da 'yan bindiga 40 ne aka kashe bayan mafarauta da jami'an rundunar KSCWC suka dakile wani gagarumin hari a ƙauyen Guga a Katsina.

Rahotanni sun ce fiye da 'yan bindiga 200 ne suka kai harin ƙarƙashin jagorancin wani shugaban 'yan bindiga mai suna Idi Abasu Aiki tare da haɗin gwiwar wasu mayaƙa daga jihar Zamfara.

Bayanan sirri sun nuna cewa maharan sun yi shirin mamaye Guga kafin daga bisani su kai hari garin Bakori da sauran ƙauyukan da ke makwabtaka da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng