Yusuf Buhari Ya San Matsayarsa bayan Kammala Zaben Fitar da Gwani na APC a Katsina

Yusuf Buhari Ya San Matsayarsa bayan Kammala Zaben Fitar da Gwani na APC a Katsina

  • Jam'iyyar APC ta gudanar da zaben fitar da gwani a mazabar tarayya ta Sandamu/Daura/Mai'Adua a jihar Katsina
  • Dan tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadi Buhari, Yusuf Buhari ya fafata da dan tsohon shugaban hukumar DSS, Auwal Lawal Musa
  • Bayan kammala zaben fitar da gwanin, an sanar da Yusuf Buhari a matsayin wanda ya yi nasara inda ya ba abokin hamayyarsa tazara mai nisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Yusuf Muhammadu Buhari, ɗan marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya samu nasara a zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC.

Yusuf Buhari ya doke Auwal Lawal Musa, ɗan tsohon shugaban hukumar DSS, Lawal Musa Daura, inda ya lashe tikitin takarar jam’iyyar APC na mazaɓar tarayya ta Daura/Sandamu/Mai’Adua a jihar Katsina.

Yusuf Buhari ya samu tikitin APC
Yusuf Buhari na jawabi a wajen taro Hoto: Yusuf Buhari
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa an gudanar da zaben fitar da gwanin ne a ranar Asabar, 16 ha watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Jamila Abdu Mani: Mace ta tika namiji da kasa, ta lashe tikitin takarar APC a jihar Katsina

APC ta gudanar da zaben fitar da gwani

An gudanar da zaɓen fitar da gwani na APC cikin lumana, inda masu ruwa da tsaki suka jinjina wa yadda aka gudanar da aikin cikin tsari.

Kwamitin APC na mazaɓar tare da shugabannin jam’iyyar sun sanya idanu akai daidai da ƙa’idodin dimokuraɗiyya na cikin gida na jam’iyyar.

Babban jami’an zaɓe, Hon. Lawal Garba, wanda ya sanar tare da tabbatar da sakamakon, ya bayyana cewa tsarin ya bi hanyoyin zaɓe da aka kafa.

Bisa ga alkaluma na hukumar, mazaɓar ta yi rajistar masu zaɓe guda 35,825, inda aka tantance mutum 18,263, kuma aka kaɗa ƙuri’u 17,832.

Yusuf Buhari ya samu kuri'u masu yawa

A karamar hukumar Daura, Yusuf Buhari ya samu ƙuri’u 6,386 daga cikin ƙuri’u 6,708 masu inganci, yayin da Auwal Lawal Musa ya samu ƙuri’u 322.

Sannan a karamar hukumar Mai’Adua, Yusuf Buhari ya samu ƙuri’u 5,102 yayin da abokin hamayyarsa ya samu ƙuri’u 137.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin gwamna ya samu tikitin takara, zai kara da Gwamnan Sokoto

Hakazalika, a karamar hukumar Sandamu kuma, ya tattara ƙuri’u 5,849, yayin da Auwal Lawal Musa ya samu ƙuri’u 21, jaridar The Punch ta kawo rahoton.

Yusuf Buhari ga samu nasara a zaben fitar da gwani
Yusuf Buhari na dagawa jama'a hannu Hoto: Yusuf Buhari
Source: Facebook

An bayyana Yusuf a matsayin wanda ya yi nasara

A ƙarshen tattara sakamakon, Hon. Lawal Garba ya bayyana Yusuf Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na APC da jimillar ƙuri’u 17,342, yayin da Auwal Lawal Musa ya samu ƙuri’u 480 a faɗin ƙananan hukumomin guda uku.

Wannan mataki ya nuna yadda APC ta yi amfani da tsarin zaɓen fiyar da gwani na kato bayan kato a mazaɓun da ba a cimma matsaya ta maslaha ba, daidai da tsarin mulkin jam’iyyar da kuma dokar zaɓe.

Yusuf Buhari ya gana da Abbas Tajudeen

A wani labarin kuma, kun ji cewa Yusuf Muhammadu Buhari ya gana da shugaban majalisar wakilan Najeriya, Abbas Tajudeen.

Yusuf Buhari ya ce ya samu damar kai ziyarar ne da wasu abokansa, inda ya bayyana tattaunawar da suka yi a matsayin mai armashi, cike da fahimtar juna da kuma amfani.

Bayan kammala ganawa da shugagaban majalisar wakilan, Yusuf Buhari ya yaba masa bisa kyakkyawar tarba, karamci da kuma shawarwari masu amfani da ya ba su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng