‘Babu Yan Bindiga a Niger’: Gwamnati Ta Gano Yadda Aka Samu Rashin Tsaro

‘Babu Yan Bindiga a Niger’: Gwamnati Ta Gano Yadda Aka Samu Rashin Tsaro

  • Gwamnatin Neja ta ce ta kawar da ayyukan 'yan bindiga da sansanoninsu a jihar, tana danganta hare-haren da masu kutse daga jihohin makwabta ke yi
  • Kwamishina Umar Ahmed Rebe ya ce rikicin manoma da makiyaya ya ragu matuka, yayin da aka yi wa shanu sama da miliyan hudu rajista
  • Rundunar 'yan sanda ta ce ba za ta iya tabbatar da babu sansanonin 'yan bindiga ba, tana mai jaddada cewa ana ci gaba da farmakin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Gwamnatin Jihar Neja ta yi magana game da rashin tsaro musamman saboda ayyukan ta'addanci.

Gwamnatin ta bayyana cewa a halin yanzu ba ta da wata matsalar 'yan bindiga ko sansanonin 'yan bindiga a cikin jihar.

Gwamnatin Niger ta ce babu yan bindiga a jihar
Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Niger yana jawabi a taro. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Source: Twitter

Kwamishinan Harkokin Makiyaya da Nomadawa, Umar Ahmed Rebe, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na ma'aikatar yaɗa labarai da aka gudanar a Minna, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya yi wa sojoji albishir, Tinubu zai sanar da karin albashinsu

Daga inda ake samun matsala a Niger

Rebe ya ce duk wata barazana ta tsaro da ake gani tana fitowa ne daga masu laifi da ke shigowa daga jihohin makwabta.

A cewarsa, rikicin manoma da makiyaya ya ragu sosai, inda ya ce kusan kashi 70 cikin 100 na irin wadannan rikice-rikicen sun daina faruwa, ya kara da cewa abin da ya rage yanzu ya fi shafar rikicin mallakar filaye.

Rebe ya ce gwamnatin jihar ta yi wa sama da shanu miliyan hudu rajista, tare da gano shugabannin makiyaya a dukkan kananan hukumomi.

Haka kuma, an dauki sama da 'ya'yan makiyaya 100 aiki a ma'aikatu daban-daban, cewar The Nation.

An tabbatar da cewa babu yan bindiga a Niger
Taswirar jihar Niger da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Matakan da gwamnatin Niger ke dauka

Kwamishinan ya ce ana kara matakan tsaro ta hanyar toshe hanyoyin shiga da manyan ramuka, ya kara da cewa duk wanda zai shigo ya zauna a jihar dole ne a tantance shi kuma wani mazaunin jihar ya tsaya masa.

Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya kauce wa tabbatar da ikirarin cewa babu sansanonin 'yan bindiga a Neja.

Kara karanta wannan

Tsaro: Tsohon daraktan DSS ta dura kan Pantami, ya faɗi illar naɗa shi minista

Ya ce zai bar wannan batu ga kwamishinan, yana mai mayar da hankali kan ayyukan tsaro.

Kwamishinan ya ce duk dabbar da aka kama ana jigilar ta ba tare da takardar izini ba za a dauke ta a matsayin wadda aka sace.

Ya bayyana cewa rundunar na ci gaba da gudanar da farmaki a dazukan jihar, musamman a Kagara, Mariga da Mashegu, inda jami'an soja, DSS da 'yan sanda ke aiki tare domin dakile barazanar tsaro.

Kakakin 'yan sandan ya kuma tabbatar da cewa har yanzu ana samun rikicin manoma da makiyaya a lokacin noman bana, ciki har da wani rikici da ya yi sanadin rasa rai.

Ya kara da cewa jami'an tsaro na ci gaba da tantance duk sababbin mutanen da ke shigowa jihar.

A cewarsa, hukumomin tsaro da ma'aikatar harkokin makiyaya na aiki tare domin magance matsalolin tsaro da suka shafi makiyaya a fadin jihar.

Abin fashewa ya kashe sojoji a Niger

An ji cewa kyaftin da sojoji biyu sun rasa rayukansu bayan motarsu ta taka wani bam da ake zargin an dasa a kan titi a Borgu ta jihar Neja.

Kara karanta wannan

Matar aure ta kwarawa kishiyarta mai ciki ruwan zafi, ta haihu dan ya mutu

Wasu sojoji biyu sun jikkata sakamakon fashewar bam ɗin, wanda ake zargin 'yan ta'adda ne suka birne shi a kan hanyar da sojojin ke bi.

Har yanzu rundunar soji ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba amma mazauna yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.