An Ragargaji Tankar Gas Din Amurka Tana Tafiya a Teku, Ta Kama da Wuta

An Ragargaji Tankar Gas Din Amurka Tana Tafiya a Teku, Ta Kama da Wuta

  • Wani hari da jirgin mara matuƙi ya rutsa da wani jirgin ajiyar gas mallakin kamfanin Amurka a tashar ruwan Damietta da ke ƙasar Masar
  • Rahotanni sun ce harin ya haddasa gobara da ta bazu zuwa wani jirgin gas na daban, sai dai ba a samu asarar rayuka ko jikkataba
  • Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ke ƙara ta'azzara a yankin Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Alkahira, Masar – Wani hari da ake zargin jirgin mara matuƙi ne ya kai ya afku kan wani jirgin ajiyar gas mallakin wani kamfanin Amurka a tashar ruwan Damietta da ke gabar tekun Bahar Rum a ƙasar Masar.

Harin ya haddasa gobara da ta bazu zuwa wani jirgin gas na daban, lamarin da ya ƙara nuna yiwuwar rikicin Gabas ta Tsakiya na ci gaba da yaɗuwa zuwa wasu yankuna.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta shiga tsaka mai wuya, Iran ta matsa mata lamba ta fannoni 3 a yaki da Amurka

Tankar gas da aka kai wa hari
Wata tankar gas da aka kai wa farmaki a teku a 2019. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Reuters ta rahoto cewa ma'aikatar man fetur ta Masar ta tabbatar da aukuwar gobara a tashar ruwan, sai dai ba ta bayyana musabbabin tashin gobarar ba.

Yadda harin ya faru

Kamfanin tsaron harkokin jiragen ruwa na Ambrey ya bayyana cewa wani jirgin mara matuƙi ne ya kai harin kan jirgin Energos Winter, wanda ake amfani da shi wajen adana da sarrafa iskar gas.

Rahoton ND TV ya nuna cewa gobarar da ta tashi daga jirgin ta bazu zuwa wani jirgin gas mai suna Gaslog Salem.

Wasu majiyoyin tsaro biyu sun bayyana cewa binciken farko ya nuna yiwuwar harin jirgin mara matuƙi ne ya haddasa fashewar.

Kamfanin Vanguard da ke sa ido kan haɗurran teku ya ce wani abu da ba a tantance ko mene ne ba ya bugi gefen dama na jirgin Energos Winter, abin da ya haddasa gobara kafin daga bisani aka shawo kanta.

An ƙara tsaurara tsaro

Kara karanta wannan

Yadda Iran ta zagaye, ta sayo makaman kariya na miliyoyin Dala a China

Ma'aikatar man fetur ta Masar ta ce jami'an kashe gobara da na tsaro sun yi gaggawar shawo kan lamarin bisa tsarin da aka tanada na gaggawa.

Ministan man fetur na Masar, Karim Badawi, ya isa wurin domin sa ido kan yadda ake gudanar da ayyukan ceto da tantance barnar da aka yi.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump na magana a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Ma'aikatar ta tabbatar da cewa ba a samu asarar rayuka ko jikkata ba, yayin da ƙungiyoyin fasaha da na gaggawa ke ci gaba da binciken tasirin lamarin.

Harin ya zo ne bayan Iran ta kai harin makamai masu linzami kan sansanonin sojojin Amurka da ke Jordan, yayin da Amurka da Saudiyya suka kai hare-hare kan ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Iran a Iraki.

Iran na ƙarfafa tsarin tsaronta

A wani labarin, mun ruwaito cewa Iran na shirin karɓar kaso na farko daga cikin makamai masu linzami na kariyar sararin samaniya da ta saya daga ƙasar China.

Rahotanni sun nuna cewa Tehran ta kulla yarjejeniyar sayen makaman ne domin ƙarfafa tsaronta bayan yaƙin da ta yi da Amurka da Isra'ila ya nuna akwai gibi a tsarin kare muhimman cibiyoyinta.

An ce yarjejeniyar ta haɗa da sayen makaman kariya tsakanin guda 300 zuwa 400, waɗanda wani kamfani da ke Hong Kong ya shiga tsakani wajen kammala cinikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng