Rikicin da ke tsakanin Olusegun Obasanjo, da tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar, ya taka rawa wajen rarrabuwar kawuna a cikin gamayyar adawa a ADC.
Rikicin da ke tsakanin Olusegun Obasanjo, da tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar, ya taka rawa wajen rarrabuwar kawuna a cikin gamayyar adawa a ADC.
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa bayyana cewa ya soki shirin kara VAT na farko da gwamnatin Tinubu ta gabatar saboda tsadar rayuwa da hauhawar farashi.
Wata mata da ba a kai ga tantance bayananta ba ta rasa rayuwarta yayin da wata Kwantena ta kutto daga kan tirela, ta murkushe ta ba zato ba tsammani a Anambra.
Gwamnan jihar Ƙatsina, Alhaji Dikko Umaru Radda, ya sha alwashin ɗaukar mataki mai tsauri kan duk wanda aka samu yana taimakon ƴan bindiga a jihar.
Gwamnatin tarayya ta koka kan yadda abubuwa suka taru suka mata yawa ita kaɗai babu mai kama mata, ta ce abu ya kai inda ya kai domin da ƙyar take biyan albashi.
Gwamnatin jihar Sokoto karƙashin gwamna Ahmed Aliyu ta ɗauki nauyin tura ɗalibai 15 'yan asalin jihar zuwa China su karanto kwasa-kwasan injiniyarin.
Daga karshe dai an yi wa marigayi magajin garin Zazzau gatan da ake wa kowane Musulmi idan kwanansa ya ƙare, an masa Sallah kuma an kai shi makwanci.
Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya nada sabbin shugabanni guda biyu da za su ja ragamar ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta tarayya.
Kotu ta jefa wani magidanci mai suna Gambo Adamu a magarkama bayan ya damfari surukarsa kudi naira miliyan 5 da nufin kulla aurenta da tsohon shugaban kasa Buhari.
Yadda ake kukan tashin man fetur, haka komai ya tashi, Man Jet A1 ko ATF da ake amfani da su a jiragen sama sun yi tsada, ‘yan kasuwa su na sayen lita a kan N1000
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya kawo tsarin bai wa dalibai lamunin karatu don inganta harkar ilimi a kasar, dalibai na dakon fara wannan shirin na ba da lamuni.
Labarai
Samu kari