Babban Sarki Ya Kama Layi, Ya Ce Ya Kamata a Hana Kowa Kamfe a Jihar Ban da Tinubu
- Wani lauya, Damilare Adenola, ya ce Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi, ba shi da ikon hana ’yan takarar shugaban ƙasa yakin neman zaɓe a Osun
- Adenola ya ce Kundin Tsarin Mulkin 1999 ya ba ’yan ƙasa ’yancin faɗar albarkacin baki, taro, ƙungiya da zirga-zirga, don haka dokar sarkin ta saba wa doka
- Lauyan ya buƙaci INEC da jami’an tsaro su tabbatar da cewa Peter Obi, Atiku Abubakar, Omoyele Sowore, Seyi Makinde sun gudanar da yakin neman zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Iwo, Osun -Wani lauya, Damilare Adenola, ya soki sanarwar Oluwo na Iwoland, Oba Abdulrosheed Akanbi kan yakin neman zaben shugaban kasa.
An ji Sarkin na cewa babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa da ya kamata ya yi yakin neman zaɓe a Osun kafin babban zaɓen 2027, sai Shugaba Bola Tinubu.

Source: Twitter
Lauya Adenola ya bayyana sanarwar a matsayin wadda ta saba wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, cewar rahoton Punch.
Kamfen 2027: Lauya ya dura kan Sarki
Ya bayyana cewa ba za a iya takaita ’yancin ’yan takarar siyasa na gudanar da yakin neman zaɓe a faɗin ƙasar ta hanyar wani basarake ba.
Ya ce sanarwar na nufin hana wasu ’yan takarar shugaban ƙasa, ciki har da ɗan takarar African Action Congress, Omoyele Sowore, Atiku Abubakar, ɗan takarar Labour, Peter Obi, da Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, gudanar da yakin neman zaɓe a Osun.
Ya ce babu wata hanyar doka da za a iya aiwatar da irin wannan takunkumi kan ’yan takara.
A cewar sa, Sashe na 39, 40, 41 da 42 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 sun tabbatar da ’yancin ’yan ƙasa na faɗar albarkacin baki, yin taro cikin lumana da kafa ƙungiyoyi, zirga-zirga cikin ’yanci da kuma kariya daga nuna wariya.
Lauyan ya ce babu wani mutum, komai matsayinsa, da zai iya hana ’yan takarar siyasa amfani da haƙƙinsu na kundin tsarin mulki wajen gudanar da yakin neman zaɓe a kowace irin jiha ko yanki na Najeriya.
Ya ce:
"Ko ShuRgaban Ƙasa ko kotu ba za su iya hana ɗan takara yin yakin neman zaɓe a ko’ina cikin ƙasar ba ba tare da bin doka da ƙa’ida ba, sai dai idan an samu umarnin doka bayan an bi dukkan matakan shari’a da suka dace.”

Source: Twitter
Sanarwar da Sarkin Iwo ya fitar
Rikicin ya samo asali ne daga sanarwar Oluwo na Iwoland, Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi, Telu I, a lokacin bikin ƙaddamar da aikin sake gina hanyar Osogbo-Iwo-Ibadan da Shugaba Bola Tinubu ya gudanar a kasuwar Aje International Market da ke Osogbo.
Basaraken ya nuna cikakken goyon bayansa ga Tinubu, sannan ya bayyana cewa bai kamata a bar sauran ’yan takarar shugaban ƙasa su gudanar da yakin neman zaɓe a fadarsa ko a Osun ba.
Oluwo ya ce:
“Babu wanda ya kamata ya tallata ko ya kawo wani ɗan takarar shugaban ƙasa domin yakin neman zaɓe a fadana da Osun.”
Basaraken ya kuma nuna cewa yana da kwarin gwiwar Tinubu zai samu damar lashe wani wa’adi na mulki, inda ya buƙaci mazauna yankin su goyi bayan Shugaban Ƙasar, cewar Vanguard.
An buƙaci gwamna ya tumbuke Sarkin Iwo
Mun ba ku labarin cewa an bukaci gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke da ya tuge sarkin Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi daga sarautar garin.
Malamin addinin gargadiya, Satguru Maharaj Ji shi ya bukaci hakan daga gwamnan saboda yadda sarkin ke zubarwa masarauta mutunci.
Maharaj ya bukaci Gwamna Adeleke ya yi gaggawar daukar mataki kan Akanbi saboda barinsa kan kujerar hatsari ne.
Asali: Legit.ng


