Kotun Abuja Ta Raba Auren Shekara Hudu Saboda Rashin Kaunar Juna

Kotun Abuja Ta Raba Auren Shekara Hudu Saboda Rashin Kaunar Juna

  • Wata Kotu a babban birnin tarayya Abuja ta raba auren mata da miji, ta umarci matar ta fara idda kamar yadda Musulunci ya koyar
  • Kotun ta kawo karshen zaman aure tsakanin Hafsat Abdullahi da Rufai saboda matar ta ce ta daina sha'awar zama da mijin
  • A cewarta, sun yi aure tun shekarar 2019 kuma a wannan lokacin ba a samu matsala, yanzu kuma ba ta ƙaunar ci gaba da zama

FCT Abuja - Babbar Kotun yanki mai zama a Kubwa a birnin tarayya Abuja ta datse igiyoyin auren da ke tsakankn Hafsat Abdullahi da mijinta, Adesegun Rufai.

Kotun ta raba ma'auratan waɗan da suka shafe shekaru huɗu suna tare da juna saboda matar ta daina ƙaunar mijinta, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kotu ta raba mata da miji a Abuja.
Kotun Abuja Ta Raba Auren Shekara Hudu Saboda Rashin Kaunar Juna Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Alkalin Kotun mai shari'a Muhammad Wakili ya raba auren ne ta hanyar "Kul'i" kamar yadda addinin Musulunci ya tanada bayan matar ta roƙi a raba su saboda ta daina sha'awar zama da shi.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Kwantena Mai Tsayin 40 Ta Faɗo Daga Bayan Tirela, Ta Murƙushe Wata Mata Har Lahira

Sai dai magidancin bai bayyana a gaban Kotun ba duk da an aika masa da takardar sammaci bayan matarsa ta shigar da ƙarar neman saki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da haka mai shari'a Wakili ya rushe auren da ke tsakaninsu karkashin oda ta 9, doka ta 3 na kundin dokokin Kotun yanki, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

Bayan haka ya umarci Hafsat ta fara iddah na tsawon watanni uku da kwanaki 10 kamar yadda shari'ar addinin Musulunci ta tanada kafin ta sake yin wani auren.

Ƙarar ta matar ta kai Kotu kan mijinta

Tun da farko, Hafsat ta shaida wa alkalin Kotun cewa ta auri mijinta ne a shekarar 2019 kamar yadda Addinin Musulunci ya shar'anta kuma babu wata matsala.

Matar ta ƙara da cewa a halin yanzu ba ta da sha’awar auren, don haka ta roki kotu da ta raba auren saboda rashin soyayya da rashin jituwar da ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa.

Kara karanta wannan

Daga Blessing Ta Zama Khadija: Matashiyar Budurwa Ta Karbi Addinin Musulunci

Kotu Ta Raba Auren da Ya Shafe Shekara 9 Kan Buƙatar Matar a Kwara

A wani rahoton kuma Ƙotu ta raba auren shekaru tara tsakanin Balkisu Imam da Nasir Imam kan buƙatar da matar ta nema a jihar Kwara.

Alkalin Kotun ya kuma damƙa amanar kula da ɗan da suka haifa ɗan shekara 8 a hannun matar, kuma mijin ya riƙa daukar nauyinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel