Daga Haduwa da Wasu a Wurin Bauta, Jarumar Fim a Najeriya Ta Zama Sojar Amurka
- Jarumar fina-finan Nollywood ta bayyana cewa wasu ‘yan Kamaru da ta haɗu da su a coci ne suka ƙarfafa mata gwiwar shiga aiki soja
- Ta ce kasancewarta sojan Amurka na fuskantar ƙalubalen sauyin al’ada, amma tana alfahari da asalin Najeriya
- Matashiyar ce idan yaƙi ya ɓarke tsakanin Najeriya da Amurka, za ta kasance cikin mawuyacin hali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohuwar jarumar Nollywood da ta koma sojan Amurka, Princess Chineke, ta bayyana kalubalen da ta fuskanta.
Ta bayyana cewa wasu ‘yan Kamaru da ta haɗu da su a coci ne suka shawo kanta shiga aikin soja.

Source: Facebook
Chineke ta ce kafin ta koma Amurka, ta kasance ‘yar kasuwa kuma kwararriyar ma’aikaciyar kafafen yaɗa labarai, inda ta kafa ƙungiya mai zaman kanta da kamfanin sarrafa harkokin nishaɗi, cewar The Nation.
Ta kuma kasance ‘yar fim kuma ta halarci makarantar New York Film Academy a shekarar 2010, inda ta samu ƙarin ilimi da ƙwarewa a harkar wasan kwaikwayo.
Ta bayyana cewa ta fara samun kuɗin farko har naira miliyan ɗaya tun tana matashiya, bayan da ta shiga harkar tallace-tallacen kayayyaki da lashe gasar Miss UNIBEN.
Chineke ta ce ta taɓa kasancewa fuskar wasu manyan kamfanoni, inda ta yi tallace-tallacen talabijin, allunan talla da ayyukan buga hoto ga kamfanoni daban-daban.
A cewarta, harkar tallace-tallace ce ta kai ta cikin masana’antar fina-finai, inda ta taka rawa a shirye-shiryen talabijin da fina-finai, tare da gudanar da ƙungiyarta da kamfaninta.
Ta ce ta bar Najeriya ne a lokacin da ta ji ta cimma abubuwa da dama, amma har yanzu tana son ƙara haɓaka ƙwarewarta da neman sababbin damar rayuwa.
Chineke ta jaddada cewa barin Najeriya ba yana nufin ta yi watsi da asalinta ba, sai dai ta so faɗaɗa tunaninta da ƙara ƙwarewa.
Ta bayyana rayuwar jaruma a matsayin abin farin ciki da gamsarwa, domin wasan kwaikwayo na ba mutum damar shiga rayuwar wasu da ba da labarinsu.
A cewarta, ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi burge ta shi ne yadda labari ke sauyawa daga rubutaccen shiri zuwa fim mai jan hankalin jama’a.
Chineke ta ce ba ta cika kewar abubuwan duniya daga Najeriya ba, sai dai tana kewar wasu mutane, abubuwan tunawa da wasu al’adun ƙasar.
Ta ce har yanzu Najeriya na da dimbin dama, ƙwararrun mutane da al’adu masu tarin yawa, amma ƙasar na fuskantar matsalolin tsaro, yunwa da tsadar rayuwa.
Ta kuma ce matsin lambar neman arziki cikin gaggawa ya ƙaru, yayin da tunanin samun kuɗi cikin sauƙi ya fi bayyana fiye da lokacin da ta bar Najeriya.
Duk da matsalolin, ta ce har yanzu tana da yakinin cewa ‘yan Najeriya na da juriya, ƙwarewa da basirar da za su iya kawo ci gaba.
Chineke ta ce ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da take fuskanta a matsayin ‘yar Najeriya a sojojin Amurka shi ne daidaita rayuwa da sabuwar al’ada.
Ta ce tana koyon sabuwar al’ada, tsarin sojan Amurka da salon rayuwa daban, yayin da take ƙoƙarin kare asalin da ya tsara rayuwarta.

Kara karanta wannan
Mabiyan Kwankwaso sun ɓullo da wasu dabaru da ka iya zama matsala ga Tinubu a zaben 2027
Yar fim din batsa ta zama sanata
An ji cewa Deyci Alejandra Omaña Ortiz, wadda aka fi sani da Amaranta Hank a harkar fina-finan batsa ta shiga siyasa.
A makon nan ta zama sanata a Colombia karkashin jam'iyyar Pacto Histórico, za ta wakilci Norte de Santander.
Ortiz ta samu nasara ne a zaben watan Maris na 2026, za ta yaki zaluncin da ake yi wa tsofaffin abokan aikinta.
Asali: Legit.ng

