"Ban Yabo don a So Ni"; Gwamna Sule Ya Tsire Tsoro Ya Ragargaji Shugaba Tinubu
- Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa ya fito fili ya soki tsarin VAT na farko da ke cikin gyaran harajin Shugaba Bola Tinubu
- Sule ya ce ya yi gargadin cewa karin VAT a lokacin da hauhawar farashi ta yi kamari zai kara wa talakawa wahala
- Gwamnan ya ce Tinubu ya saurari damuwar gwamnonin tare da sauya wasu abubuwan da ke cikin kudirin harajin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Nasarawa - Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana a ranar Asabar cewa ya fito fili ya soki tsarin harajin VAT na farko da ke cikin gyaran harajin Shugaba Bola Tinubu.
Gwamna Sule ya yi gargadin cewa karin harajin a lokacin da hauhawar farashi ta yi kamari zai cutar da talakawa.

Source: Facebook
Sule ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin Bayo Onanuga tare da tawagar Renewed Hope Ambassadors National Media Tour a gidan gwamnatin Nasarawa da ke Lafia, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan
Tinubu ya aika saƙo cikin kaɗuwa da aka tabbatar da rasuwar babban malami a Najeriya
Ziyarar ita ce karo na biyu na rangadin kasa baki daya domin duba ayyukan gine-ginen ababen more rayuwa na gwamnatin tarayya da jihohi, bayan tawagar ta kammala ziyara a Jihar Benue.
Tinubu ya saurari gwamnonin
Sule ya ce Shugaba Tinubu ya saurari damuwar gwamnonin da suka hada da shi, daga bisani aka yi gyare-gyare kan sauye-sauyen da ke cikin kudirin harajin.
"Ba na yin yabon banza. Lokacin da aka batar da Shugaban Kasa game da haraji, na soki lamarin a fili. Mutane sun fahimci batun ba daidai ba, kuma lokacin da muka ziyarci Shugaban Kasa, ya ce, ‘Sule, ka je ka gana da Zacch Adedeji da ministan kudi na yanzu, Taiwo Oyedele. Idan ka yi sauye-sauyen kuma suka amince, to babu matsala.’
“Na ce, ‘Mai girma Shugaban Kasa, wannan shi ne abin da muke so daga gare ka.’ Gwamnonin suna matsa min cewa ni ne ya kamata na yi magana, kuma na yi magana. Da muka je, sai muka yi sauye-sauyen.” In ji shi
Dalilin sukar karin VAT
Sule ya bayyana cewa dalilin adawarsa da tsarin shi ne yanayin hauhawar farashin kayayyaki da ake ciki a lokacin da aka fara gabatar da gyaran harajin.
“Mun yi sauye-sauyen ne saboda a ranar 1 ga Janairu, 2025, VAT zai kai 10% a lokacin. Hauhawar farashi ta kai kusan 30%. Yanzu kuma hauhawar farashi na gab da koma wa kasa da 10%. Don haka yanzu za ka iya karbar karin haraji.” In ji shi
Ya ce ya fito ne daga bangaren kasuwanci, don haka ba zai bari jam’iyyarsu ta yi kuskure ba, yana mai cewa sun yi sa’a saboda suna da Shugaban Kasa mai sauraron ra’ayoyin mutane.
“Ya saurara. Mun yi sauye-sauyen. Suna da amfani, kuma suna kawo karin kudi ga jihohi; hakan ya sa Shugaban Kasa ya kara samun karbuwa,” in ji shi.

Source: Facebook
Sule ya ce ba ya makauniyar biyayya
Sule ya ce a shirye yake ya kalubalanci Shugaban Kasa a bainar jama’a idan hakan ya zama dole, domin hakan na cikin falsafarsa ta yin magana cikin gaskiya maimakon nuna biyayya ba tare da tunani ba.
“Akwai hanyar da ya kamata ka bi wajen yabawa shugabanninka idan sun yi abin da ya dace. Haka yake kuma idan sun kauce layi.” In ji shi
Gwamna Sule ya kori kwamishinoni
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya amince da yin wani karamin sauyi a majalisar zartarwar jihar, inda ya sauke kwamishinoni shida daga mukamansu.
Gwamnatin Nasarawa ta bayyana cewa wannan matakin zai taimaka wajen kara inganta aikin gwamnati gabanin babban zaben shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

