Juyin Mulki: Abin Ɓoye Ya Fito Fili, an Gano dalilin Tinubu na Ƙara Rundunar Sojoji

Juyin Mulki: Abin Ɓoye Ya Fito Fili, an Gano dalilin Tinubu na Ƙara Rundunar Sojoji

  • Wasu rahotanni sun fara bayyana kan dalilin Shugaba Bola Tinubu ya amince da ƙarin rundunonin soji guda huɗu
  • Sababbin rundunonin za su ƙara yawan rundunonin Sojojin Najeriya daga takwas zuwa 12, tare da ɗaukar sababbin jami’an soja 28,000
  • Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta cewa faɗaɗa rundunonin na da alaƙa da tsoron juyin mulki inda ta ba al'umma shawara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An fara magana da zargi game da amincewar Bola Tinubu na fadada rundunar sojoji a Najeriya.

Wani gagarumin nazarin tsaro da aka gudanar bayan yunƙurin juyin mulki da ya gaza na iya tasiri kan matakin Tinubu na faɗaɗa Sojojin Najeriya.

Ana zargin Tinubu ya fadada sansanonin sojoji saboda tsoron juyin mulki
Ministan tsaro, Christopher Musa da Bola Tinubu. Hoto: HQ Nigerian Army, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Majiyoyi daga manyan jami’an soja sun ce sauye-sauyen an tsara su ne domin ƙarfafa tsarin mulkin dimokuraɗiyya da kuma hana duk wani yunƙurin kwace mulki, cewar Punch.

Kara karanta wannan

An ji dalilin Saudiyya da ta garkame wasu 'yan Najeriya a gidan yari

Ana zargin Tinubu kan fadada rundunar sojoji

Faɗaɗawar za ta ƙara yawan rundunonin Sojojin Najeriya daga takwas zuwa 12, tare da samar da guraben ɗaukar sababbin jami’an soja 28,000.

Wani babban jami’in leƙen asirin soja ya bayyana cewa nazarin bayanan sirri bayan yunƙurin juyin mulkin Satumba 2025 ya yi tasiri sosai.

Ya ce masu tsara tsaro sun fahimci cewa hana sake samun yunƙurin kwace mulki ba bisa ƙa’ida ba na buƙatar inganta ƙarfin aikin sojoji.

Ya ce:

“Ganin irin girman barnar da hukumomin tsaro suka yi imanin cewa yunƙurin juyin mulkin zai iya haifarwa idan ya yi nasara, abin fahimta ne.
“Saboda haka gwamnati za ta nemi kawar da duk wata kafa da za ta iya taimakawa wajen sake samun wani yunƙurin kwace mulki ba bisa ƙa’ida ba.”
Ana samun karin bayanai kan yunkurin juyin mulki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Yadda yunkurin juyin mulki ya samu sojoji

Wani jami’in Sojan Sama ya ce shugabannin sojoji da dama sun damu matuƙa da yunƙurin juyin mulkin da ya gaza.

Kara karanta wannan

Dalilin Najeriya na bude ƙofar tuba ga 'yan bindiga a Najeriya

Ya ce tun daga lokacin suka tsara matakan da za su kawar da yiwuwar sake samun yunƙurin kifar da gwamnatin da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya.

Ya bayyana cewa faɗaɗa rundunonin sojoji na daga cikin matakan da ake tunanin ɗauka domin cimma wannan buri, cewar Daily Post.

Jami’in ya ƙara da cewa yadda jama’a suka mayar da martani bayan rahotannin yunƙurin juyin mulkin ma ya yi tasiri kan lissafin tsaron gwamnati.

A cewarsa, hukumomi sun yi imanin cewa martanin jama’a bai nuna cewa akwai gagarumin shirin da 'yan ƙasa za su yi na dakile canjin gwamnati ba.

Wannan ne ya ƙara tabbatar wa gwamnati cewa akwai buƙatar ƙarfafa matakan kariya domin hana duk wani yunƙurin kifar da tsarin mulki.

Majiyar ta ce sauye-sauyen da ake samu a hukumomin tsaro, ciki har da shirin ƙara rundunonin Sojoji, ya kamata a duba su cikin wannan babban tsarin.

“Daga mahangar gwamnati, hanya mafi aminci ita ce tabbatar da cewa duk wani yunƙurin nan gaba ba zai samu damar shirya kansa ba.
“Sauye-sauyen na iya inganta ayyukan tsaron cikin gida, sannan su ƙara juriya ga tsarin mulki ta hanyar ƙarfafa tsarin tsaro da sanya shi wahalar lalacewa.”

Kara karanta wannan

Dara ta ci gida: Wani bam ya fashe da ƴan ƙungiyar ISWAP yayin da suke hada shi

- Cewar majiyar

Bincike kan juyin mulkin Tinubu na kara fadi

An ji cewa an zargi fitaccen jarumin Nollywood, Stanley Amandi, da amincewa da aikin shirya farfaganda domin tallafa wa wadanda suka shirya juyin mulki.

Bincike ya ce an bukaci ya tsara yadda za a tara jama'a da kuma shirya bukukuwan nuna goyon baya a jihohin Kudu maso Gabas.

Amandi ya shaida wa masu bincike cewa ya karɓi N100,000 daga wani jami'in soja bayan wata ganawa a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.