Tashin Hankali da Jami'an Tsaro Suka Gwabza Fada a Kogi, an Samu Asarar Rayuka
- An tabbatar da mutuwar mutane bayan rikici ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan sa-kai biyu a Karamar Hukumar Yagba ta Gabas da ke Jihar Kogi
- An ce rikicin ya samo asali ne bayan wani dan kungiyar 'yan sa-kai ya harbe wani makiyayi da ba shi da makami bisa zargin satar shanu
- Gwamnatin Kogi ta ce za ta cafke tare da gurfanar da duk wadanda ke da hannu a kashe-kashen da suka faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kogi - Mutane tara sun mutu bayan wani rikici tsakanin kungiyoyin 'yan sa-kai biyu a Karamar Hukumar Yagba ta Gabas da ke Jihar Kogi.
Rahotanni sun ce arangama ta barke tsakanin wasu ’yan kungiyar 'yan sa-kai a yankin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dan wani shugaban kungiyar 'yan sa-kai ta Fulani.

Source: Original
Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa mummunan lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Agustan 2026.
Mutuwar dan shugaban Fulanin ta janyo ramuwar gayya daga kungiyar da ta fusata, inda aka kashe wasu mazauna garuruwa uku.
An kwashe wadanda suka samu raunuka zuwa Babban Asibitin Bida domin yi musu magani.
Yadda Rikicin Ya Fara
Kingsley Fanwo, kwamishinan yada labarai na Jihar Kogi, ya ce kashe-kashen ramuwar gayya sun faru ne a garuruwan Abugi, Kuchinda da Mikugi da ke masarautar Kupa, a Karamar Hukumar Lokoja ta jihar.
Fanwo ya ce rahotannin farko sun nuna cewa rikicin ya fara ne bayan wani dan kungiyar 'yan sa-kai ta yankin ya harbe wani makiyayi da ba shi da makami bisa zargin cewa yana satar shanu.
Ya ce gwamnatin jihar ta kuduri aniyar cafke duk wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Kwamishinan ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, maras ma’ana kuma wanda ba za a amince da shi ba, yana mai jaddada cewa babu wani rashin fahimta da ya kamata ya kai ga rasa rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
Fanwo ya kara da cewa Ahmed Ododo, gwamnan Kogi, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu da kuma daukacin masarautar Kupa.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikansu da rahama, ya kuma bai wa wadanda suka bari hakurin jure rashinsu.
Gwamnati ta san wadanda suka kai hari
Kingsley Fanwo ya ce gwamnati ta gano manyan mutanen da ke da hannu a harin da ya jawo asarar rayuka.
“Maimakon a sasanta lamarin, daya daga cikin shugabannin kungiyar 'yan sa-kan ya shirya harin ramuwar gayya, wanda ya kai ga kashe mutanen. Muna da cikakken bayani kan abin da ya faru. Mun san manyan mutanen da ke da hannu, kuma muna bin sawunsu. Za a cafke su, kuma za su bayyana irin rawar da suka taka.”
Ya kara da cewa kwamandan Brigade ta 12 ya tura sojoji yankin, yayin da kwamishinan ’yan sanda shi ma ya tura jami’ansa zuwa garuruwan da lamarin ya shafa.

Source: Facebook
’Yan Sanda Ba Su Samu Rahoto Ba
Da aka tuntubi Saliu Oyiza Afusat, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kogi, ta ce har yanzu ba ta samu cikakken bayani a hukumance kan lamarin ba.
“Kamar yadda na fada a baya, har yanzu ban samu rahoto a hukumance kan wannan batu ba.” In ji ta.
'Yan bindiga sun kashe 'yan sa-kai
A wani labarin kuma, kun ji cewa Yan bindiga masu ɗauke da makamai sun kashe jami'an tsaro na 'yan sa-kai guda biyu a jihar Plateau.
'Yan bindigan sun kashe jami'an tsaron na 'yan sa-kai ne a garin Ta-Hoss da ke karamar hukumar Riyom ta jihar Plateau.
Asali: Legit.ng


