'Yan Ta'adda Sun Yi Wa Dattijuwar Yankan Rago a Gidanta Da Ke Jihar Gombe

'Yan Ta'adda Sun Yi Wa Dattijuwar Yankan Rago a Gidanta Da Ke Jihar Gombe

  • Rundunar 'yan sanda sun tabbatar da mutuwar wata dattijuwa a Unguwar Jekadafari da ke birnin Gombe
  • Marigayiyar mai suna Aishatu Abdullahi yayin da 'yan ta'adda su ka mata yankan rago a daren jiya Juma'a
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Mahid Mu'azu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni aka fara bincike kan kisan gillar

Jihar Gombe - Wasu 'yan ta'adda sun yi ajalin wata dattijuwa a Unguwar Jekadafari da ke cikin garin Gombe.

Marigayiyar mai suna Aishatu Abdullahi da aka fi sani da 'Adda Damori' ta rasa ranta ne bayan 'yan ta'addan sun yi mata yankan rago.

Yan Kalare sun yi wa wata mata yankan rago a Gombe
'Yan sanda sun fara binciken kisan gillar da aka yi a dattijuwa a Gombe. Hoto: Inuwa Yahaya.
Asali: Twitter

Yaushe aka yi ajalin dattijuwar a Gombe?

Lamarin ya faru ne a daren jiya Juma'a 20 ga watan Oktoba a unguwar da misalin karfe biyu na dare.

Kara karanta wannan

Mista Ibu: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Da Ke Jinya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Mahid Mu'azu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce kwamishinan 'yan sanda ya kafa kwamitin bincike kan kisan.

Mahid ya tabbatar da cewa an dauki gawar matar zuwa asibitin kwararru na jihar inda likitoci su ka tabbatar da mutuwarta nan take.

Ya ce har yanzu ana kan bincike don sanin dalilin wannan kisan gilla da aka yi wa dattijuwar.

Wane martani gwamnatin jihar Gombe ta yi?

An sanar da cewa za a yi sallar jana'izar marigayar da misalin karfe 1:30 na rana a masallacin Daurawa da ke birnin Gombe.

Aminiya ta tabbatar da cewa hadimin Gwamnan jihar kan harkar tsaro, Ambasada Yusuf Musa Danbayo, ya ce ana zargin turo su aka yi su yi wa matar kisan gilla.

Danbayo ya bayyana cewa maharan sun shiga gidan ne da misalin karfe biyu na dare inda su ka yi mata kisan gilla su ka kuma tsere da wayar salularta.

Kara karanta wannan

Mutane Sun Yi Takansu Yayin da 'Yan Fashi Suka Farmaki Bankuna 2, Jami'an Tsaro Sun Mutu

Kakakin rundunar ya ce kwamishinan ’yan sanda mai kula da ayyuka, Hayatu Usman a madadin kwamishinan ’yan sanda, ya ba da umarnin a gagguata fara bincike.

Ya ce rundunar ba za ta zauna ta nade hannu kan wannan lamari ba inda ya ce za su zakulo wadanda suka aikata laifin don fuskantar shari’a.

Barayi sun yi ajalin babban malami a Gombe

A wani labarin, wasu da ake zargin barayi ne sun yi ajalin babban malamin addinin Musulunci a Gombe.

Marigayin Sheikh Ibrahim da aka fi sani da Albanin Kuri ya rasa ransa ne a gidansa yayin da 'yan ta'addan su ka kai masa hari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel