Alfarmar da Amurka ke Nema wajen Iran kan Mashigar Hormuz
- Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ya ce Amurka na neman Iran ta yi alkawarin ba za ta kara harbin jiragen ruwa na kasuwanci ba
- Vance ya ce dole a kwashe nakiyoyin da Iran ta dasa a mashigar ruwan Hormuz domin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin tsaro
- Adadin jiragen ruwa da ke ratsa mashigar ya yi matukar raguwar bayan takaddama da hare-haren da suka shafi Iran da Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya bayyana abin da Amurka ke nema daga wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Vance ya ce Amurka na neman Iran ta yi alkawarin cewa ba za ta harbi jiragen ruwa na kasuwanci ba, yayin da ake kokarin dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar ruwan Hormuz.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta ce JD Vance ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Fox News a ranar Asabar, 8 ga watan Agustan 2026.
Mataimakin shugaban kasar ya ce akwai bukatar a share nakiyoyin da aka dasa a mashigar tare da tabbatar da cewa jiragen kasuwanci za su iya wucewa cikin tsaro domin zirga-zirga ta farfado.
“Abin da ke faruwa a cikin mako guda ko makamancin haka shi ne Iran da kasashen Gulf, musamman Oman, suna tattaunawa kan yadda za a tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin tsaro.” In ji shi
Ana neman tsabtace mashigar Hormuz
Mataimakin shugaban kasar na Amurka, Vance ya ce babbar matsalar ita ce Iran ta dasa nakiyoyi masu yawa a farkon yakin.
“Abin da muke kokarin warwarewa a yanzu shi ne yadda za a samar da tsarin zirga-zirga da zai ba jiragen da ke wucewa damar wucewa cikin tsaro. Hakan ya hada da kwashe nakiyoyin,” in ji shi.
Ya kara da cewa Amurka na kuma neman “alkawari daga Iran cewa ba za ta harbi jiragen ruwa na kasuwanci ba”.
An takaita zirga-zirgar jiragen ruwa
A baya, mashigar ruwan Hormuz na da muhimmiyar rawa wajen safarar makamashi, inda jiragen dakon iskar gas mai narkewa (LNG) ke ratsa ta, cewar rahoton Aljazeera.
Sai dai tsawon fiye da watanni biyar, zirga-zirgar makamashi a mashigar ta samu tangarda sosai yayin da Iran ke kokarin kara iko da hanyar ruwan, ciki har da kai hare-hare kan jiragen da take zargi da karya ka’idojinta.
Iran ta fara sanar da rufe mashigar ne bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai mata a ranar 28 ga Fabrairu.
Ko da yake an sake bude hanyar na dan lokaci a tsakiyar watan Afrilu, Iran ta sake sanya takunkumi bayan Amurka ta killace tashoshin jiragen ruwa na Iran.
Bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran a ranar 17 ga Yuni, an yi niyyar sake bude mashigar. Sai dai zirga-zirga ta ci gaba da kasancewa kadan yayin da Iran ta ce jiragen da ke wucewa har yanzu dole su tuntubi hukumominta.
A cewar bayanan PortWatch, jiragen ruwa 513 ne kawai suka ratsa mashigar a cikin kwanaki 18 na farko bayan sake bude ta, tsakanin 18 ga Yuni zuwa 5 ga Yuli. Wannan ya yi daidai da matsakaicin jirage 28 a rana, sabanin matsakaicin jirage 140 kafin yakin.

Source: Getty Images
Babban soja na son Amurka ta daina yakin Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban hafsan sojojin Amurka, Janar Dan Caine, na neman wata hanyar da za ta ba Amurka damar fita daga yaƙin da take yi da Iran.
Majiyoyin da suka san halin da ake ciki sun bayyana cewa Caine ya yi imanin cewa wasu matakan soji na iya jefa Amurka cikin ƙarin matsala.
Asali: Legit.ng


