Gwamnan Katsina Zai Hukunta Sarakunan Gargajiya Masu Taimakawa Yan Bindiga a Jihar

Gwamnan Katsina Zai Hukunta Sarakunan Gargajiya Masu Taimakawa Yan Bindiga a Jihar

  • Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Dikko Umaru Radda ya sha alwashin hukunta masu taimakawa ƴan bindiga a jihar
  • Gwamnan ya yi nuni da cewa akwai wasu sarakunan gargajiya da aka gano, waɗanda tuni aka fara bincikarsu
  • Dikko ya yi nuni da cewa matsalar rashin tsaro da ake fama ɗa ita a jihar na matuƙar ci masa tuwo a ƙwarya

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi barazanar ɗaukar mataki mai tsauri kan duk wani kwamishina, basaraken gargajiya ko muƙarrabansa da aka kama yana taimakawa ƴan bindiga a jihar.

Gwamnan ya jaddada cewa duk da cewa matsalar rashin tsaro ta zama wata annoba da ta ƙi ƙarewa, ba zai tattauna da ƴan bindiga ba ko wasu gungun masu laifi a jihar.

Gwamnan Katsina zai hukunta masu taimakon yan bindiga
Gwamna Dikko Radda zai hukunta masu taimakon yan bindiga a Katsina Hoto: Dikko Umaru Radda
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta rahoto cewa Radda ya shaida wa manema labarai a Abuja ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba, cewa an yi ƙoƙari sosai domin ganin an daƙile kutsen da ƴan bindiga da suka yi a jihar inda ya ragu sosai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Shugaba Tinubu Ta Fara Kukan Babu Kuɗi a Ƙasa, Ta Ce da Kame-Kame Ake Biyan Albashi

Gwamnan ya gano wasu sarakuna masu laifi

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A yanzu haka da muke magana, akwai wasu sarakunan gargajiya da aka gano waɗanda kuma tuni aka fara binciken su. Babu wanda za mu ƙyale. Ina gaya muku cewa hatta kwamishinoni na ko duk wanda aka samu yana da hannu a cikin wani laifi ba zai tsira ba."
"Muna magana ne a kan rayuwar mutanen jihar Katsina, ba mutum ɗaya ba. Babu wani mutum daya da ya fi mutane miliyan 10 muhimmanci, musamman ma rayukan waɗanda ba su ji ba ba su gani ba a ƙauyuka."
"Tun zama na gwamna, babu ranar da ba zan samu rahoton sace-sace ko kashe mutane ko wani abu da ya danganci irin hakan ba. Hakan na damu na. Wani lokacin buɗe wayata yana da wahala saboda na san abin da zan fuskanta.”

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabuwar Rundunar Tsaro Ta Jihar Katsina

Gwamnan ya bayyana cewa a farkon gwamnatinsa ya ɗauki aƙalla jami'an tsaro na community watch corps guda 1,500 da aka zabo daga ƙananan hukumomi takwas da ke fuskantar matsalar tsaro domin yaƙi da rashin tsaro a jihar.

Gwamna Dikko ya taka rawar gani

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani ɗan jihar Katsina mai suna Aliyu Idris, wanda ya yaba da hanyar da gwamnan ya ɗauko domin murƙushe ƴan bindiga a jihar.

Aliyu ya yi nuni da cewa gwamnan ya taka rawar gani sosai a wajen harkar tsaro tun bayan da ya ɗare kan karagar mulkin jihar.

"Yana taka rawar gani wacce ba a taɓa tunanin zai yi ta ba. Ya nuna da gaske yake yi. Kuma a shirye yake ya ga ya kawar da matsalar tsaro a jihar. Abin da kawai za mu cigaba da yi masa shi ne addu'a." A cewarsa.

Gwamna Radda Ya Sha Alwashin Karar da Yan Bindiga

Kara karanta wannan

Katsina: Bayan Kafa Rundunar Tsaro, Gwamnatin Radɗa Ta Yi Magana Kan Yiwuwar Tattaunawa da 'Yan Bindiga

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa domin kawo ƙarshen ƴan bindiga.

Gwamnan ya yi nuni da cewa tsaro yana da matuƙar muhimmanci ga al'umma, kuma gwamnatinsa ba za ta yi wasa da shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel