"Jarumar Fina Finan Najeriya Ta Mutu a Ofishin Ƴan Sanda," Saurayinta Ya Yi Zargi

"Jarumar Fina Finan Najeriya Ta Mutu a Ofishin Ƴan Sanda," Saurayinta Ya Yi Zargi

  • An ce marigayiyar jarumar Nollywood, Temitope Osoba, ta rasu a wani ofishin ’yan sanda da ke Ikorodu a Legas, sabanin rade-radin cewa ciwon kansar nono ne ya yi sanadin mutuwarta
  • Wanda za ta aura, Annabi Itunu Onadeko, ya ce wani mutum da ba a san ko wanene ba ne ya kira shi da tsakar dare ya sanar da shi mutuwar jarumar
  • Onadeko ya musanta zargin cewa an saka wa Osoba guba ko kuma an wulakanta ta kafin rasuwarta, tare da cewa ciwon kansa da ta yi fama da shi ba shi ne ya kashe ta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Lagos – Prophet Itunu Onadeko, angon marigayiyar jarumar Nollywood, Temitope Osoba, ya yi zargin cewa jarumar ta rasu a wani ofishin ’yan sanda da ke Ikorodu a Jihar Legas.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: An rufe makarantu 65 a Sokoto, Katsina da wasu jihohin Arewa

Onadeko ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Celestial Reality Check, sashen bincike na kafar yaɗa labarai ta cocin Celestial Church of Christ, a ranar Asabar.

Wanda Temitope Osoba za ta aura ya yi zargin cewar jarumar ta mutu ne a ofishin 'yan sanda.
Jarumar fina finan Nollywood, Temitope Osoba da ake zargin ta mutu a ofishin 'yan sanda. Hoto: Temitope Osoba
Source: Instagram

Bayani kan mutuwar jarumar Nollywood

Zargin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan musabbabin mutuwar jarumar, inda wasu rahotanni da saƙonnin kafafen sada zumunta suka danganta rasuwarta da matsalolin da ta fuskanta sakamakon cutar kansar nono, in ji rahoton Punch.

Sai dai Onadeko ya musanta cewa ciwon kansar nono ne ya yi sanadin mutuwar Osoba, duk da cewa ya tabbatar da cewa ta taɓa fama da cutar tare da yin tiyata.

Onadeko, wanda shi ne jagora a cocin CCC Onibuore Cathedral da ke Bogije, yankin Ibeju-Lekki a Legas, ya ce wani mutum da ba ya iya tantance ko wanene ba ne ya kira shi da misalin ƙarfe 12 na dare domin sanar da shi mutuwar jarumar.

Ya ce:

“Wani mutum kawai ne ya kira ni da misalin ƙarfe 12 na dare ya ce ta rasu a wani ofishin ’yan sanda da ke Ikorodu.”

Sai dai faston ya ce bai san takamaiman ofishin ’yan sandan da Osoba ta rasu a cikinsa ba. Ya bayyana cewa bayan samun labarin, sai ya kai kansa wani ofishin ’yan sanda da ke kusa da shi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, an kashe fiye da 65 yayin da aka ceto mutane 360

Osoba ta je ganin wata mata

Onadeko ya ce Osoba ta dage sai ta je ganin wata mata mai suna Kehinde Osoba, wadda ya ce ita ma tana gudanar da coci, jim kaɗan kafin mutuwarta.

Ya ce jarumar ta kuma yi niyyar ganinsa, amma ya kasa zuwa saboda wasu shirye-shiryen coci da yake da su a lokacin.

“Ta dage sai ta ga Mrs Kehinde Osoba, ita ma tana da coci, duk da cewa ta ce tana son ganina ni ma. Da suka tafi wurin, na gaya musu cewa ba zan samu damar zuwa ba a ranar saboda shirye-shiryen coci.”

Onadeko ya ƙara da cewa wata mai gyaran gashi da Osoba ke kwana a gidanta ce ta raka ta zuwa wurin.

Ya ce sun ci gaba da sadarwa da ita, har ma ta wallafa wani saƙo mai cewa “Ogo tun tun” kafin daga bisani ya ji labarin mutuwarta.

An musanta wasu zarge-zarge

Prophet Onadeko ya kuma musanta wasu zarge-zarge da suka biyo bayan mutuwar Osoba, ciki har da ikirarin cewa an saka mata guba ko kuma an wulakanta ta kafin rasuwarta.

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan TikTok 3 sun fara ganin sakamako bayan sun taɓa mutuncin shugaban ƙasa

Ya kuma ƙaryata zargin cewa ya samu damar mallakar kuɗaɗen da aka tara domin taimaka wa jarumar wajen biyan kuɗin tiyatar kansar nono, ko kuma ya yi amfani da kuɗin wajen gina cocinsa.

Saurayin jarumar Nollywood Osoba ya ce ba kansa ce ta kashe ta ba
Jarumar fina finan Nollywood, Temitope Osoba da ake zargin ta mutu a ofishin 'yan sanda. Hoto: Temitope Osoba
Source: Instagram

Osoba ta taɓa bayyana a bainar jama'a cewa ta yi fama da cutar kansar nono tare da samun magani da tiyata.

A shekarar 2024, jarumar ta sanar da komawarta cikin harkokin jama'a bayan shafe wani lokaci tana fama da matsalar, inda ta bayyana cewa wannan lokaci ya taimaka mata wajen samun waraka, ƙaruwa da ƙarfin gwiwa.

Sai dai sabuwar ikirarin da angonta ya yi ya ƙara jefa haske kan yanayin da ya dabaibaye mutuwar jarumar, yayin da har yanzu ba a samu cikakken bayani mai zaman kansa kan takamaiman musabbabin mutuwarta ba.

Kalli bidiyon tattaunawar a nan kasa:

Jarumar Nollywood ta mutu

A wani labari, mun ruwaito cewa, wata fitacciyar jarumar Nollywood da ke tashe, Omotola Odunsi ta riga mu gidan gaskiya.

Abokan aiki da jarumai a masana'antar shirya fina-finan da ke Kudancin Najeriya sun tabbatar da mutuwarta a sakonni daban-daban.

Sun bayyana alhini da jimaminsu bisa wannan rashi da suka yi tare da addu'ar Allah Ya ba iyalanta haƙuri da juriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com