An Ji Uwar Bari, An Bada Shawarar Amfani da Man-Ja a Matsayin Man Jirgin Sama

An Ji Uwar Bari, An Bada Shawarar Amfani da Man-Ja a Matsayin Man Jirgin Sama

  • Masana da sauran masu ruwa da tsaki a kan sha’anin jiragen sama sun yi taro na musamman a makon nan a Abuja
  • A wajen taron ne aka kawo shawarar a koma amfani da wasu mai na dabam domin kamfanoni su rage kashe kudi
  • Man Jet A1 ko ATF da ake amfani da su a jiragen sama sun yi tsada, ‘yan kasuwa su na sayen kowace lita a kan N1000

Abuja - Masu ruwa da tsaki wajen harkar jiragen sama sun ce Najeriya ta kai matsayin da za ta fara neman madadin man jirgi.

A rahoton da aka fitar a Daily Trust, hakan ya zama dole ne ganin makudan kudin da ake kashewa wajen shigo da mai daga ketare.

A wajen wani taro da aka shirya a garin Abuja a ranar Laraba, an kawo shawarwari a kan yadda za a rage kashe kudi kan man jirgi.

Kara karanta wannan

Abin Tausayi: 'Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Mataimakin Magatakardar Kwalejin Gwamnatin Tarayya, An Bazama Nemansu

Jirgin sama
Filin jirgin saman MMIA Hoto: @FAAN_Official
Asali: Twitter

Da yake jawabi a madadin Kamfanonin jiragen sama a Najeriya (AON), Kyaftin Roland Iyayi ya ce kasar za ta iya komawa man ja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan har aka koma hako man ja domin amfani da shi a jiragen sama, za a samu sauki a lokacin da kudin kasashen waje su ke ta tashi.

Yadda ake samun man jirgin sama

Masana sun ce man jirgi wanda aka fi sani da Jet A1 ko ATF nau’i ne na tsabtataccen kananziri wanda ake samu daga danyen mai.

Litar man Jet A1 ko ATF da jirage su ke amfani da shi ya kai N1, 000 a halin yanzu, dole masu jirage su ka fara nemawa kan su sauki.

Ganin yadda kasuwa ta ke a yau, Roland Iyayi ya ce ba za ta yiwu a cigaba da sayaen man jirgi a kan N1000, dole a nemi wata mafita.

Kara karanta wannan

Duniya Ta Yi Tir da Israila a Kan Kashe Fiye da Bayin Allah 500 Kwance a Asibiti

Tashar rediyon Trust ta rahoto cewa Ministan harkoki da cigaban jiragen sama, Festus Keyamo muhimmancin neman mai dabam.

Tun da masana su na ganin za a iya amfani da man-ja kuma a samu biyan bukata, kamfanonin sun yarda da wannan shawara.

Shugaban hukumar NCAA na kasa, Kyaftin Musa Nuhu ya samu yin jawabi a wajen taron.

Gwamnatin Tinubu ta gyara zama

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara mulki da lashe amansa wajen nadin mukamai da tsare-tsare, ya na yin tafka ya na warwarewa.

A irin haka aka shirya ba Malam Nasir El-Rufai, Maryam Shetty da injiniya Imam Kashim Imam mukamai, sai aka fasa daga baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel