"Babu Kuɗi a Kasa" Gwamnatin Tinubu da Kyar Take Iya Biyan Ma'aikata Albashi a Wata

"Babu Kuɗi a Kasa" Gwamnatin Tinubu da Kyar Take Iya Biyan Ma'aikata Albashi a Wata

  • Gwamnatin tarayya ta aminta da cewa an shiga cikin yanayi mai wahala ta yadda biyan albashin ma'aikata ya zama mai wahala
  • Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Atiku Bagudu, ya ce babu kuɗi a ƙasar nan ga kuɗin shiga sun ja baya
  • Ya buƙaci kungiyoyi masu zaman kansu su taya FG ta ciccibo ƙasar nan daga manyan kalubalen da suka dabaibaye ta

FCT Abuja - Najeriya ta faɗa yanayi mai wahala na tattalin arziƙi, tana fuskantar manyan kalubale da ƙarancin samun kuɗaɗen shiga yayin da adadin mutane ke ƙaruwa.

Gwamnatin tarayya karkashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta amince da haka, ta ce akwai babban ƙalubale a gabanta, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin tarayya ta ce ta kyar take iya biyan albashi.
"Babu Kuɗi a Kasa" Gwamnatin Tinubu da Kyar Take Iya Biyan Ma'aikata Albashi a Wata Hoto: Presidency
Asali: UGC

FG ta kuma koka kan yadda take faɗi tashi da kame-kamen biyan ma'aikata albashi a kowane ƙarshen wata saboda, "babu kuɗi a baitul mali."

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Bi Sahun Abba Gida-Gida, Ya Ɗauki Nauyin Ɗaliban Jiharsa Zuwa Kasar Waje Karatu

Da yake jawabi a Abuja, Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Atiku Bagudu, ya bukaci kungiyoyi masu zaman kansu su taimaka wa gwamnati wajen tallabo inda ba za ta iya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bagudu, wanda Daraktan hadin gwiwar kasa da kasa na ma’aikatar, Dakta Sampson Ebimaro, ya wakilta, ya koka kan yadda adadin 'yan Najeriya ke karuwa kamar walƙiya.

Ministan ya bayyana cewa yawan masu zaman kashe wando na ƙara ƙaruwa yayin da ake tsaka da fama da hauhawar farashi ba ƙaƙƙauta wa.

Dailypost ta rahoto Ministan na cewa:

"Matsaloli daban-daban sun yi wa gwamnati katutu, musamman a yanzu da ake fama da karancin kuɗin shiga. Babu kudi a ko'ina, gwamnati na kula da biyan albashi ne kawai."
"Ci gaban da ake samu ya yi kaɗan yayin da mutane ke daɗa ƙaruwa kamar kyaftawa da bisimilla. Rashin ayyukan yi na ƙara yawaita ga tashin farashi."

Kara karanta wannan

Albashi: Malamin Firamare N250k, Sakandare N500k, Lakcara N1m? Majalisa Ta Bada Bayani

Hannu ɗaya baya ɗaukar jinka - Alade

Dakta Sarah Alade, tsohuwar mukaddashin gwamnan CBN, ta ce gwamnati ba zata iya cika burinta na tsamo miliyoyin mutane daga ƙangin talauci ba dole sai an kama mata.

Alade, tsohuwar mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin kuɗi da tattalin arziki, ta roƙi gwamnati ta jawo masu zaman kansu a jiki, su haɗa karfi da karfe.

Gwamnatin Sokoto Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibai 15 a Kasar China

A wani rahoton na daban Gwamnatin Sakkwato karkashin Gwamna Ahmed Aliyu zata fara tura ɗalibai zuwa ƙasashen waje domin su yi karatu.

Shugaban hukumar bada tallafin karatu ta jihar, Abdulƙadir Ɗan'iya,.ya ce a makon farko na watan Nuwamba ɗalibai 15 zasu tafi China.

Asali: Legit.ng

Online view pixel