Najeriya na iya Rasa Tallafin Amurka na Dala Biliyan 1.4, an Gano Babban Dalili

Najeriya na iya Rasa Tallafin Amurka na Dala Biliyan 1.4, an Gano Babban Dalili

  • Najeriya na iya rasa wani sabon tallafin lafiya da agaji na Amurka na dala biliyan 1.4 idan gwamnatin tarayya ba ta ɗauki matakan da za a iya aunawa ba kan kare Kiristoci daga hare-hare
  • Yarjejeniyar fahimtar juna da Najeriya da Amurka suka sanya hannu ta tanadi kusan dala biliyan 2.1 cikin shekaru biyar domin yaƙi da cututtuka da inganta ayyukan lafiya
  • Amurka ta kuma danganta ci gaba da wasu shirye-shiryen tallafin da matakan Najeriya na kare al'ummomin Kirista daga tashe-tashen hankulan masu tsattsauran ra'ayin addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja - Najeriya na iya rasa wani sabon tallafin lafiya da agaji na Amurka da ya kai dala biliyan 1.4.

Hakan zai faru idan gwamnatin tarayya ta gaza ɗaukar matakan da za a iya aunawa wajen magance tashin hankalin da ake yi wa Kiristoci, kamar yadda sharuddan wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ƙasashen biyu suka tanada.

Kara karanta wannan

An gano kasashe 3 da gwamnatin Tinubu ta yi nazarinsu don kafa ƴan sandan jihohi

Najeriya na iya rasa tallafin kiwon lafiya na dala biliyan 2.1 daga Amurka.
Najeriya na iShugaban Amurka, Donald Trump da takwaransa na Najeriya, Bola Tinubu Hoto: Chip Somadevilla/@officialABAT
Source: UGC

Tallafin lafiya na $2.1bn daga Amurka

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa an kulla wannan yarjejeniyar tsakanin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka da gwamnatin Najeriya a ranar 20 ga Disamba 2025.

Yarjejeniyar ƙarƙashin tsarin America First Global Health Strategy (AFGHS), ta tanadi cewa Amurka za ta kashe kusan dala biliyan 2.1 cikin shekaru biyar a fannin ilimin Najeriya.

An ce za a kashe wadannan kudin ne domin faɗaɗa ayyukan rigakafi da maganin HIV, tarin fuka, zazzabin cizon sauro, lafiyar mata da yara da kuma cutar shan inna.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, ana kuma sa ran Najeriya za ta ƙara kashe kusan dala biliyan 3 daga kuɗaɗen cikin gida kan harkokin lafiya a tsawon lokacin yarjejeniyar.

An bayyana wannan a matsayin mafi girman gudunmawar kuɗin cikin gida da ƙasa za ta bayar a ƙarƙashin shirin AFGHS.

Asibitocin addini na cikin shirin

Wani babban ɓangare na kuɗin da Amurka za ta bayar an ware shi ne ga cibiyoyin lafiya da asibitocin da ƙungiyoyin addini ke gudanarwa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda za ku duba sunayen waɗanda hukumar Kwastam ta ɗauka aiki a 2026

Yarjejeniyar ta ce akwai kusan cibiyoyin lafiya 900 da ƙungiyoyin addini ke gudanarwa a Najeriya, waɗanda a halin yanzu suke yi wa sama da kashi 30 cikin 100 na 'yan Najeriya hidima.

Sai dai yarjejeniyar ta ƙunshi wasu tsauraran sharudda da za su iya shafar ci gaba da samun tallafin.

Yarjejeniyar ta ce an kulla ta ne bisa la'akari da sauye-sauyen da gwamnatin Najeriya ta yi domin ba da fifiko wajen kare al'ummomin Kirista daga tashin hankali.

Ta kuma tanadi "gagarumin tallafi na musamman" ga cibiyoyin lafiya da ƙungiyoyin Kirista ke gudanarwa.

Amurka ta sanya wa Najeriya sharadi

Yarjejeniyar ta kuma bayyana cewa Shugaban Amurka da Sakataren Harkokin Wajen ƙasar na da ikon dakatarwa ko kawo ƙarshen duk wani shiri da bai yi daidai da muradun ƙasar ba.

Ta ƙara da cewa gwamnatin Donald Trump na sa ran Najeriya za ta ci gaba da samun ci gaba wajen yaƙi da tashin hankalin masu tsattsauran ra'ayin addini da ake yi wa al'ummomin Kirista masu rauni.

Wannan sharadi ya ƙara samun ƙarfi bayan Majalisar Wakilan Amurka ta kada ƙuri'ar danganta tallafin da Najeriya ke samu da matakan da za a iya tabbatar da su wajen magance tsananta wa Kiristoci.

Kara karanta wannan

Bayani kan ƙarin albashi da Tinubu ya yi wa ƙanana da manyan sojojin Najeriya

An ce wani kudiri da majalisar ta amince da shi a watan da ya gabata ya bukaci gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakai na zahiri domin tabbatar da dawowar mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon rikici zuwa garuruwansu na asali.

Haka kuma, kudirin ya bukaci a tabbatar da kare Kiristocin da ake tsananta wa a yankin Middle Belt.

Amurka za ta ba Najeriya tallafin kiwon lafiya amma da sharadi
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump.
Source: UGC

Amurka ta ware dala biliyan 1.4

A cikin sabon tallafin da Washington ta amince da shi ƙarƙashin AFGHS, Amurka ta ware dala biliyan 1.4 domin tallafa wa ayyukan lafiya ta hanyar asibitoci da cibiyoyin lafiya da ƙungiyoyin addini da al'umma ke gudanarwa a ƙasashe sama da 20.

Daga cikin wannan kuɗi, dala miliyan 850 za ta bi ta wani shiri mai suna Faith and Community Initiative Award, wanda zai tallafa wa World Vision da masu aiwatar da shirye-shiryen lafiya na ƙungiyoyin addini a ƙasashe 17.

Shirin zai ƙarfafa sama da asibitoci da cibiyoyin lafiya 2,500 tare da horarwa, biyan kuɗi da samar da kayan aiki ga ma'aikatan lafiya na al'umma sama da 30,000.

Ƙarin dala miliyan 570 kuma za a tura kai tsaye ga asibitoci da cibiyoyin lafiya na ƙungiyoyin addini da al'umma ta hanyar yarjejeniyoyin fahimtar juna da gwamnatoci, ciki har da Najeriya.

Kara karanta wannan

"Farfaganda ce": Atiku ya zargi gwamnati da jefa Najeriya a wahala

An ware ƙarin kuɗin agaji

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta kuma sanar da ware dala miliyan 538 domin ayyukan agaji da Samaritan's Purse da haɗin gwiwar World Vision da Compassion International za su gudanar.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa kuɗin zai taimaka wajen kai agaji ga mutane miliyan bakwai da rikice-rikicen jinƙai suka shafa a ƙasashe 16.

An kuma ce sama da dala miliyan 100 za a samar nan take domin tunkarar bala'o'i a ƙasashe 23 da ke fuskantar barazanar aukuwar bala'o'i.

Najeriya na fuskantar sharadin tallafin

A game da Najeriya, yarjejeniyar ta ba da muhimmanci na musamman ga masu samar da ayyukan lafiya na ƙungiyoyin Kirista, inda aka bayyana su a matsayin cibiyoyin da suke da muhimmiyar rawa wajen ƙara ƙarfi ga ayyukan cibiyoyin lafiya na gwamnati.

Amurka ta kakaba sharadi ga Najeriya don samun tallafin kiwon lafiya
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (hagu) da Shugaban Amurka, Donald Trump (dama).
Source: Getty Images

Yarjejeniyar ta zo ne a lokacin da Amurka ke karkatar da ƙarin albarkatu zuwa cibiyoyin lafiya da ƙungiyoyin addini ke gudanarwa a ƙasashen da suke karɓar tallafi.

Kara karanta wannan

Amurka ta yi kuskure da ta yi magana kan harin 'yan bindiga a Kaduna

A wasu daga cikin waɗannan ƙasashe, irin waɗannan cibiyoyin suna samar da kashi 40 cikin 100 ko fiye na dukkan cibiyoyin lafiya.

Saboda haka, yadda Najeriya za ta ci gaba da samun damar cin gajiyar sabon tallafin zai dogara ne kan matakan da gwamnatin tarayya za ta ɗauka wajen magance damuwar da aka bayyana a Washington kan kare Kiristoci daga tashin hankalin masu tsattsauran ra'ayin addini.

Amurka ta shirya dakile tallafinta

A wani labari, mun ruwaito cewa, Majalisar Wakilan Amurka ta amince da kudirin dakatar da duk tallafin Amurka ga ƴan Najeriya da kasar baki daya.

Masana sun gargadi cewa idan kudirin ya zama doka, shirye-shiryen HIV, tarin fuka, zazzabin cizon sauro, rigakafi da lafiyar mata da yara za su shiga hadari.

Sun bukaci gwamnatin Najeriya ta inganta tsaro, karfafa dangantaka da Amurka, tare da samar da hanyoyin cikin gida domin daukar nauyin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com