Gwamnatin Sokoto Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibai 15 a Kasar China

Gwamnatin Sokoto Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibai 15 a Kasar China

  • Gwamnatin Sakkwato karkashin Gwamna Ahmed Aliyu zata fara tura ɗalibai zuwa ƙasashen waje domin su yi karatu
  • Shugaban hukumar bada tallafin karatu ta jihar, Abdulƙadir Ɗan'iya, ya ce a makon farko na watan Nuwamba ɗalibai 15 zasu tafi China
  • Ya ce za a kara ɗaukar nauyin ƙarin ɗalibai zuwa ƙasashen waje domin su karancu kwasa-kwasan da zasu amfani al'umma

Sokoto - Gwamnatin jihar Sakkwato za ta tura ɗalibai 'yan asalin jihar zuwa ƙasar China domin su yi karatu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta ɗauki nauyin karatun daliban su 15 zuwa ƙasar China kuma za su tafi nan ba da jimawa ba.

Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu.
Sokoto ta ɗaukin nauyin tura ɗalibai zuwa kasar waje neman ilimi Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Sokoto, Abdulkadir Dan’iya ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a ofishinsa ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Waiwayi Leburori, Ya Ce Zai Ɗauki Nauyin Karatunsu Har Su Gama Jami'a Bisa Sharaɗi 1

Ya kuma yi bayanin cewa ɗaliban da za su ci gajiyar wannan tallafin karatu, za su karanci kwasa-kwasan injiniyarin daban-daban a ƙasar Sin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe ɗaliban da zasu tafi?

Abudulƙadir Ɗan'iya ya kuma bayyana cewa zasu bar ƙasar nan a makon farko ko kuma mako na biyu na watan Nuwamba mai zuwa a 2023 da muke ciki.

Shugaban hukumar bada tallafin karatun ya ce:

"A halin yanzu suna kan ɗaukar horo da kuma wayar da kai wanda ya zama wajibi saboda zaman da zasu yi a ƙasar waje."
"Tuni gwamnatin jihar Sakkwato ta biya masu kuɗin makaranta da sauran hidindimun da zasu yi yayin zaman karatu a can ƙasar."

Dan’iya ya kara da cewa za a kara daukar nauyin karatun wasu dalibai a kasashen waje domin su karanci kwasa-kwasan da suka dace da jama’a.

Kara karanta wannan

Albashi: Malamin Firamare N250k, Sakandare N500k, Lakcara N1m? Majalisa Ta Bada Bayani

Ya kuma shawarci daliban da aka ɗauki nauyi a yanzu da su yi aiki tukuru kar su ba gwamnatin jihar Sakkwato kunya bisa yardar da ɗora a kansu, Tribune ta ruwaito.

Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Kwastam

A wani rahoton na daban Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da Adewale Adeniyi a matsayin kwantrola janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya.

An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa mai dauke da sannun Wille Bassey, Direktan Watsa Labarai na ofishin SGF a ranar Juma'a 20 ga watan Oktoba a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel