Maimuna, Budurwan da Ta Yanke Al'surar Saurayinta Ta Fara Girban Abin da Ta Shuka a Kano

Maimuna, Budurwan da Ta Yanke Al'surar Saurayinta Ta Fara Girban Abin da Ta Shuka a Kano

  • Kotu ta ba da umarnin ci gaba da tsare wata budurwa mai suna, Maimuna Idris mai shekaru 25 a gidan gysran hali bisa zargin yanke mazakutar saurayinta
  • An gurfanar da Maimuna gaban kotu ne kan tuhume-tuhumen da suka shafi zarginta da yunkurin kisan kai da kuma jikkata mutum
  • Kotun majistare da ke Kano ta dage sauraron karar zuwa 9 ga Satumba, 2026 domin ci gaba shari'a kan wannan batu da ya ja hankalin jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa an gurfanar da wata matashiyar budurwa mai shekaru 25 da haihuwa, Maimuna Idris s gaban kotun kan zargin yanke al'aurar saurayinta a Kano.

Bayan gurfanar da ita a gaban kotun majistire da ke Kano, alkali ya ba da umarnin ci gaba da tsare Maimuna Idris, a gidan gyaran hali bisa zargin yanke mazakutar saurayinta, Ashiru Sani.

Kara karanta wannan

An tsare tsohon jami'in DSS a gidan kaso kan zargin alaka da kungiyar ta'addanci

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Maimuna, yar asslin karamar hukumar Maigatari ta jihar Jigawa, na fuskantar tuhume-tuhume biyu da suka hada da yunkurin kisan kai da kuma jikkata mutum mai tsanani.

Lauyan masu gabatar da kara, H.A. Sani-Buhari, ya shaida wa kotun cewa an aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Yuli a Badawa Quarters da ke Kano.

Yadda lamarin ya faru a Kano

A cewar mai gabatar da karar, da misalin karfe 12:50 na rana a ranar da lamarin ya faru, ‘yan sandan Badawa suka samu rahoto daga otal din Durbar cewa wadda ake zargin ta kai wa saurayinta hari da wuka mai kaifi.

Ta ce kafin hakan, da misalin karfe 11:00 na safe, Maimuna ta yanke mazakutar saurayin nata bayan ta gano cewa yana shirin auren wata mace.

“Nan take aka garzaya da saurayin zuwa Asibitin Urology na Abubakar Imam da ke Kano domin a duba lafiyarsa,” in ji mai gabatar da karar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare matafiya, sun budewa jama'a wuta

Maimuna ta amsa laifinta a kotu

Maimuna ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi a gaban kotun ba tare da wani ɓata lokaci ba.

A cewar mai gabatar da kara, laifuffukan sun saba wa tanade-tanaden sashe na 229 da 248 na kundin hukunta laifuka na Penal Code.

Kotun ta dage sauraron karar

Alkalin kotun, Mai Shari’a Sadiya Usman, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Maimuna a gidan gyaran hali.

Kotun ta kuma dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Satumba domin sake gabatar da karar a gabanta.

Matar aure ta kusa yanka mijinta a Katsina

A wani labarin, kun ji cewa wata matar aure yar kimanin shekara 23, Sadiya Lawal ta yi yunkurin kashe mijinta ta hanyar yanka masa wuya yana cikin barci a jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa matar ta daba wa mijinta wuƙa a wuya a yayin da yake barci, lamarin da ya jikkata shi amma bai mutu ba har zuwa yanzu.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sun kama matar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262