Amurka Ta Yi Kuskure da Ta Yi Magana kan Harin 'Yan Bindiga a Kaduna

Amurka Ta Yi Kuskure da Ta Yi Magana kan Harin 'Yan Bindiga a Kaduna

  • Amurka ta yi Allah-wadai da harin da ya kashe aƙalla mutum 30, ciki har da yara, a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya
  • Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce za ta ci gaba da matsa wa gwamnatin Najeriya kan matsalar tsaro a yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
  • Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya umarci hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen gano waɗanda suka kai harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kaduna - Amurka ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wani ƙauye a jihar Kaduna a ranar 26 ga Yuli, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 30, ciki har da yara.

Sashen Harkokin Afirka na Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce zai ci gaba da matsa wa gwamnatin Najeriya lamba domin ta magance abin da ya bayyana a matsayin yaɗuwar hare-haren da ake kai wa Kiristoci a yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan shan suka Gwamna Abba ya kare matakin ba 'yan APC filaye sama da 1500

Amurka ta yi magana kan harin 'yan bindiga a Kaduna
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hakan na kunshe ne a cikin wani saƙo da sashen ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, 1 ga watan Agustan 2026.

Me Amurka ta ce kan harin Kaduna?

Amurka ta bayyana harin a matsayin abin takaici tare da miƙa ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Sanarwar ta ce:

“Amurka ta yi Allah-wadai da harin da aka kai da sanyin safiyar ranar 27 ga Yuli a wani ƙauye da ke jihar Kaduna a Najeriya, wanda rahotanni suka ce ya kashe aƙalla mutum 30, ciki har da yara. Muna miƙa ta'aziyyarmu ga iyalai da masoyan waɗanda suka mutu."
“Za mu ci gaba da kira ga gwamnatin Najeriya da ta magance yaɗuwar hare-haren da ake kai wa Kiristoci a yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya.”

An kai harin da daddare

Sai dai an kai harin ne da misalin ƙarfe 11:00 na daren Lahadi, 26 ga watan Yulin 2026 ba da sanyin safiya ba kamar yadda hukumar Amurka ta bayyana.

Kara karanta wannan

INEC ta yi fatali da sanya sojoji a tsarin zaben Najeriya, an ji dalili

'Yan bindigan dai sun yi kisan ne bayan sun afka ƙauyen Naridon da ke gundumar Kamaru, a ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Maharan sun riƙa harbin mazauna ƙauyen ba tare da bambanci ba, tare da ƙona gidaje da shaguna.

Sakataren mai unguwar Naridon, Dogon Rana, ya shaida wa jaridar The Punch cewa an tabbatar da mutuwar mutum 30, ciki har da yara takwas.

Ya ce wasu mutum huɗu suna cikin mawuyacin hali sakamakon raunukan da suka samu. A cewarsa, wani iyali a ƙauyen ya rasa yara biyar a dare guda, yayin da mutum ɗaya kacal ya rage da rai kuma yake fafutukar tsira.

An zargi jami'an tsaro

Wani mazaunin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya yi zargin cewa mutum 22 daga dangin Rana ne aka kashe.

Ya kuma ce harin ya ɗauki kusan sa'o'i uku ana kaiwa, ba tare da jami'an tsaro sun kai ɗauki ba, duk da cewa akwai jami'an tsaro da ke kasa da kilomita biyu daga ƙauyen.

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi Allah-wadai da kisan tare da umartar hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen gano waɗanda suka kai harin.

Kara karanta wannan

Iran ta tsokano Trump, ya sha alwashi bayan an shammaci Amurka

Ya kuma umarci hukumar kula da ayyukan gaggawa ta jihar da ta kai kayan agaji ga iyalan da harin ya shafa.

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Amurka ta fasa kai hari a Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ce ya janye shirin kai hari kan Iran bisa sharadin cewa za a iya cimma yarjejeniya cikin gaggawa.

Trump ya ce Iran da wasu kasashen Gabas ta Tsakiya sun bukaci Amurka ta dakatar da kai hare-hare, yana mai cewa an riga an cimma matsaya kan muhimman sharuddan yarjejeniyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng