Yadda Sojoji Suka Yi wa 'Yan Bindiga Kwanton Bauna a Wurin Karban 'Haraji'

Yadda Sojoji Suka Yi wa 'Yan Bindiga Kwanton Bauna a Wurin Karban 'Haraji'

  • Sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar mafarautan sun yi wa wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne kwanton bauna a Gombi ta Jihar Adamawa.
  • An ce ‘yan ta’addan na karbar haraji da suka laftawa wasu makiyaya a kan hanyar Gaba zuwa Dzangola da ke gundumar Guyaku
  • Sojojin sun kwato miyagun makamai da suka hada da bindigar AK-47 guda day da harsasai a lokacin da suka taka da gudu bayan sun ji wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Adamawa – Sojojin Rundunar Sojin Najeriya, tare da hadin gwiwar mafarauta sun yi wa wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne kwanton bauna yayin da suke karbar haraji daga makiyaya a Karamar Hukumar Gombi ta Jihar Adamawa.

Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan na gudanar da ayyukansu ne a kan hanyar Gaba zuwa Dzangola da ke gundumar Guyaku, lamarin da ya sa sojojin Bataliya ta 226 suka kafa kwanton bauna a wani muhimmin wuri.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, an kashe fiye da 65 yayin da aka ceto mutane 360

Sojojin Najeriya sun tarwatsa yan bindiga
Wasu daga cikin yan bindiga, zaratan dakarun Najeriya Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa majiyoyin soji sun ce an gudanar da aikin ne da misalin karfe 11:15 na dare a ranar 6 ga watan Agusta.

Sojoji sun tarwatsa yan bindiga

Jaridar The Cable ta kawo labarin cewa a cewar majiyar, sojojin sun yi arangama da ‘yan ta’addan da misalin karfe 4:42 na safiyar ranar 7 ga watan Agusta, 2026 inda suka tilasta masu ja da baya cikin rudani bayan artabun.

Ko da yake ba a iya tabbatar da adadin ‘yan ta’addan da suka mutu ko suka jikkata ba, sojojin sun kwato makamai da harsasai da dama daga hannun kungiyar yayin da take tserewa.

Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai bindigar AK-47 guda daya, magazin din AK-47 guda daya, harsasan Special 7.62mm guda 15, bindiga kirar gida guda daya da kuma harsasan 9mm guda uku.

Sojoji sun yi nasara

A cewar rahoton, babu wani rahoto da ke tabbatar da cewa wani soja ya rasa ransa ko ya jikkata yayin da aka kwashe tsawon lokaci ana dauki ba dadi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun shafe mako suna ruwan wuta kan 'yan ta'adda, an kashe 69

An gwabza tsakanin yan bindiga da sojoji
Taswirar jihar Adamwa da ke Arewa maso Gabas a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An bayyana cewa duk da cewa an dauki lokaci mai tsawo ana musayar wuta, sojojin sun iya tsayawa tare da mayar da martani mai karfi da kuma hana kwacen kudin makiyayan.

Majiyoyin sun ce bayan an kammala aikin kora yan bindigan zuwa daji, wadanda suka fito aiki sun koma sansaninsu a cikin kwanciyar hankali.

Sojoji sun kashe yan bindiga 69

A wani labarin, kun ji cewa Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan ta'adda 69 tare da ceto mutane 363 da aka yi garkuwa da su a ayyukan da ta gudanar cikin kwanakin bakwai.

Sojojin sun kuma kama mutane 49 da ake zargi da aikata laifi tare da tarwatsa matatun mai uku ba bisa ƙa'ida ba da kuma kwato lita 251,600 na ɗanyen mai da aka yi garkuwa da su.

Daraktan Yaɗa Labarai na DHQ, Manjo Janar Michael Onoja, ya ce soja ɗaya ya mutu yayin da wani ya jikkata a cikin ayyukan da aka gudanar wanda aka samu gagarumar nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng