Yadda Rikicin Atiku da Obasanjo Ya Jawo Hadakar 'Yan Adawa ta Watse
- Rikicin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da tsohon mataimakinsa Atiku Abubakar ya haddasa rarrabuwar kawuna a hadakar adawa karkashin jam’iyyar ADC
- Majiyoyi sun ce Obasanjo ya yi kokarin hana Atiku samun tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC
- An ce lamarin ya taimaka wajen ficewar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso daga jam’iyyar ADC ta 'yan hadaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Rikicin da ke tsakanin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar, ya kawo nakasu ga jam'iyyar ADC.
Majiyoyi sun ce rikicin Obasanjo da Atiku ne ya haddasa rarrabuwar kawuna a hadakar jam’iyyun adawa karkashin jam'iyyar ADC.

Source: Facebook
Wasu sahihan majiyoyi daga ADC da Kungiyar Kwankwasiyya suka bayyana hakan ga jaridar The Punch.
Obasanjo bai so Atiku ya samu takara
Majiyoyin sun yi zargin rashin nasarar Obasanjo na hana Atiku zama dan takarar shugaban kasa na ADC ne ya zama farkon rarrabuwar kan jam’iyyar.

Kara karanta wannan
Ta faru ta ƙare: APC ta ɗora sunayen yan takarar gwamna da mataimakansu a shafin INEC
A cewar wani babban jami’in ADC, Obasanjo ya kira wasu shugabannin jam’iyyar tare da umartar su da kada su bari Atiku ya zama dan takarar jam’iyyar idan har suna son ya goyi bayan ta.
“Obi bai ma fara tunanin ficewa daga jam’iyyar a lokacin ba. Bayan waccan tattaunawa da Baba (Obasanjo), magoya bayan Obi suka fara taken ‘Obi ko babu kowa’, sannan rikici ya barke, amma muka samu damar shawo kansa."
“Amma Baba da Obi sun fassara taron Ibadan Opposition Coalition Summit da cewa muna son gabatar da tikitin Atiku da Makinde. Saboda haka suka fara shirin ficewa daga jam’iyyar,” in ji jami’in jam’iyyar.
Aregbesola ya nemi sasanta Su
Jami’in ya ce lokacin da ya bayyana cewa Obi na son ficewa daga ADC, sakataren jam’iyyar na kasa, Ogbeni Rauf Aregbesola, da wasu mutane sun je wajen Obasanjo a karshen watan Afrilu domin lallashinsa ya yi magana da Obi kada ya fice.
A cewar wani dan jam’iyyar ADC kuma wanda ke da masaniya kan lamarin, Obasanjo ya dage cewa sharadin da zai sa Obi ya ci gaba da kasancewa a ADC shi ne jam’iyyar ta tabbatar da cewa Atiku bai samu tikitin takarar shugaban kasa ba.
“Hadakar Atiku da Obi da ta samu nasara za ta iya tabbatar wa ADC nasara, amma a fili Baba bai son Atiku ya cimma burinsa na zama shugaban kasa. Wannan shi ne ra’ayina,” in ji majiyar.
Wani aminin Aregbesola da ya yi magana da jaridar ba tare da bayyana sunansa ba, ya tabbatar da cewa sakataren ADC ya yi kokarin hana Obi ficewa daga jam’iyyar.
“Ba karya ba ce. Oga (Aregbesola) ya yi duk abin da zai iya domin hana Obi da Kwankwaso ficewa daga ADC. Ya gana da Obasanjo da wasu manyan shugabannin kasar. Sai dai ban sani ba ko Obasanjo ne ya umarci Obi ya fice daga jam’iyyar,” in ji shi.
Obasanjo ya taka rawa wajen ficewar Obi
Haka kuma, wani jigo a Kungiyar Kwankwasiyya, wata kungiyar siyasa mai biyayya ga tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya ce Obasanjo na da muhimmiyar rawa wajen ficewar Obi daga ADC.
“Tun farko, tsohon Shugaban Kasa yana son a ba Obi tikitin takarar shugaban kasa na ADC. Shi ne ya tsara tafiyar Obi zuwa ADC. Yana goyon bayan tikitin Obi da Kwankwaso."
“Obi da Kwankwaso suna da kwamitin hadin gwiwa kan tikitin nasu wanda ke tsara dabarunsu. Amma lokacin da ya bayyana cewa ba za a iya kwace tikitin shugaban kasa na ADC daga hannun Atiku ba, shugabanninmu suka sanar da shi (Obasanjo). Na yi imanin cewa daga nan ne Obi da shugabanmu (Kwankwaso) suka yanke shawarar ficewa daga ADC,” in ji shi.
Tsohon jigon na NNPP ya ce Obi ko Kwankwaso ba za su iya yin abin da ya saba wa burin Obasanjo ba, yana mai cewa bacin ran tsohon Shugaban Kasa ga Atiku ya ci gaba da cutar da tsohon mataimakin shugaban kasar.

Source: Facebook
ADC ta ce Obasanjo ya kitsa ficewar
Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya tabbatar da cewa Obasanjo ya yi tasiri kan matakin karshe na Obi na ficewa daga ADC.
Ya ce kiyayyar Obasanjo ga tsohon mataimakin shugaban kasa na daga cikin manyan dalilan da suka sa ya umarci Obi ya fice daga jam’iyyar.
Obasanjo ya yi zargi kan Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zargi tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar, da kitsa yunkurin tsige shi daga kan mulki.
Olusegun Obasanjo ya zargi Atiku da bayar da N5m ga tsohon shugaban majalisar wakilai, marigayi Ghali Na’Abba, domin fara yunkurin tsige shi a wa’adinsa na farko.
Asali: Legit.ng

