Borno: Yan Sanda Sun Cafke Mutum 2 da Ake Zargi da Kisan Diyar Dan Majalisa

Borno: Yan Sanda Sun Cafke Mutum 2 da Ake Zargi da Kisan Diyar Dan Majalisa

  • Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta yi caraf da wasu mutum biyu da ake zargi da.kisan ɗiyar ɗan majalisar dokokin jihar
  • Mutum biyun da aka kama dai akwai mijin matar tare da abokinsa waɗanda suka kai gawarta ofishin ƴan sanda
  • Rundunar ƴan sandan sun bayyana cewa kafin rasuwar matar sun samu saɓani da mijinta kan zargin cin amanar aure

Jihar Borno - Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta tabbatar da kama wasu mutum biyu, Adamu Alhaji Ibrahim, mai shekara 31 daga Dikechiri da Bukar Wadiya mai shekara 39 daga Dikechiri bisa laifin kashe wata ƴar shekara 24 ɗiyar ɗan majalisar jihar Borno mai wakiltar ƙaramar hukumar Ngala.

Marigayiyar kafin rasuwarta ita ce matar Ibrahim, wanda shi ne ake zargi na farko.

Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi da kisan diyar dan majalisa
Yan sanda sun cafke mutum biyu da ake zargi da kisan diyar dan majalisa a Borno Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Idan dai ba a manta ba dai marigayiyar ta rasu ne bayan da wasu da ba a san ko su waye ba suka shaƙe ta har lahira a Gidan mijinta a kusa da Gidan Dembe da ke Maiduguri a ranar Talata da ta gabata, yayin da aka yi jana’izar ta a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Miyagun Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Arewacin Najeriya, Sun Halaka Mutane Masu Yawa

Rahotannin farko sun nuna cewa, lamarin ya faru ne da ƙarfe 7 na dare, inda aka ce mijin ya bar harabar gidan zuwa masallacin da ke kusa da wajen domin yin sallah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun cafke waɗanda ake zargi

Rundunar ƴan sandan ta fitar da sanarwa a ta hannun kakakinta, Sani Shatambaya, a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba, dangane da cafke mutum biyun da ake zargi, cewar rahoton Vanguard.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"A ranar 18/10/2023 da misalin ƙarfe 6:00 na safe wani Adamu Alhaji Ibrahim mai shekara 31 a unguwar Dikechiri bayan Gidan Dambe a Maiduguri ya tafi ofishin ƴan sanda na Gwange tare da rakiyar Bukar Wadiya mai shekaru 39 tare da motar Honda mai lamba MAG 230 AP da CHASIS NO ANR742256679821 ɗauke da gawar wata mata wacce Adamu Alhaji Ibrahim ya yi iƙirarin cewa ita ce matarsa ​​kuma ya nemi taimakon ƴan sanda."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Zulum Ya Bayar da Muhimmin Umarni Bayan Miyagu Sun Halaka Diyar Dan Majalisa a Jihar Borno

"Daga baya an bayyana matar da suna Fatima Alhaji Bukar. Mijin ya bayyana cewa shi ma'aikacin bankin UBA ne, kuma ya dawo daga wurin aiki da misalin karfe 5:00 ya same ta kwance cikin jini."
"Binciken farko ya nuna cewa kafin faruwar lamarin, ma'auratan sun samu saɓani a cikin gida kan zargin cin amanar aure da mijin ya yi a gidan aurensu."
"Babu wata shaida ta karyewa ko shiga gidan da ƙarfin tsiya, kuma mijin ne kawai ke da makullin buɗe gidan daga waje."
"An kama mijin da Bukar Wadiya matsayin wadanda ake zargi. Ana cigaba da gudanar da bincike mai zurfi dangane da lamarin."

Zulum Ya Ba Yan Sanda Umarni

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Borno ya ba ƴan sanda umarni kan kisan ɗiyar ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar ƙaramar hukumar Ngala.

Gwamnan ya bayar da umarnin a gudanar da bincike kan gawarta domin gano musabbabin abin da ya halaka ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel