Sheikh Daurawa Ya Rubuta Zungureriyar Wasikar da Za Ta Matasa Su Shiga Taitayinsu
- Sanannen malamin addinin Musulunci, Shekh Aminu Ibrahim Daurawa, ya rubuta wasikar tunatarwa ga matasa
- Sheikh Daurawa ya yi nasihohi masu ratsa hankali ga matasa kan abubuwan da ya kamata su yi don inganta rayuwarsu
- Malamin addinin musulucin ya bukaci matasa su yi abubuwan da za su amfane su domin su ne ginshikin gobe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi muhommin kira ga matasa.
Sheikh Daurawa wanda malamin addinin Musulunci ne ya bukaci matasa da su fara gyara kawunansu kafin su nemi gyara duniya.

Source: Facebook
Sheikh Daurawa ya yi tunatarwa ne ga matasa a cikin wasikar da ya rubuta wadda ya sanya a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, 9 ga watan Agustan 2026.
Meyasa Daurawa ya rubuta wasika ga matasa?

Kara karanta wannan
Fitattun 'yan TikTok 3 sun fara ganin sakamako bayan sun taɓa mutuncin shugaban ƙasa
Sheikh Daurawa ya ce ya rubuta wasiƙar ne ba domin ya zargi matasa ba, sai domin tunatar da su cewa su ne ginshiƙin gobe.
Malamin ya ce abin da matasa suka zama yau shi ne zai taimaka wajen gina ko rusa al’ummar da za mu rayu a cikinta gobe.
Abin da wasikar Daurawa ta kunsa
"Kada ka raina shekarunka. Kada ka ce kai ƙarami ne, domin manyan canje-canje a tarihi sun faru ne ta hannun matasa masu manufa, ilimi, imani da jajircewa."
"Ka gyara kanka kafin ka nemi gyara duniya. Ka fara da sallarka, halinka, maganarka, abokanka, iliminka da yadda kake amfani da lokacinka."
"Ya kai matashi, ka sani cewa lokaci shi ne jarinka mafi girma. Idan ka ɓata shi, ba za ka iya dawo da shi ba. Kada ka bar wayar hannu, shafukan sada zumunta da nishaɗin banza su sace maka shekarun da ya kamata ka gina makomarka."
"Ka karanta. Ka koyi sana’a. Ka nemi ilimi. Ka koyi fasaha. Ka girmama iyaye. Ka zaɓi abokan kirki. Ka nisanci miyagun ƙwayoyi, zina, shaye-shaye, caca, tashin hankali da duk abin da zai lalata maka rayuwa."

Kara karanta wannan
Bincike kan shirin yi wa Tinubu juyin mulki ya rutsa da fitaccen jarumin fim a Najeriya
"Kada ka bari wani ya yi amfani da fushinka wajen cimma manufarsa. Kada a yaudare ka da ƙabilanci, siyasa, jita-jita ko ƙiyayya. Ka zama matashi mai tunani; kada ka yarda da duk abin da aka gaya maka sai ka bincika gaskiyarsa."
"Ka sani cewa jarumta ba ta cikin faɗa kawai. Jarumin gaske shi ne wanda yake iya sarrafa fushinsa, ya iya gafartawa, ya iya cewa “na yi kuskure”, ya iya neman ilimi, ya iya aiki domin al’umma, kuma ya iya tsayawa kan gaskiya."
"Idan kana son canza al’umma, ka fara da kanka. Idan kana son zaman lafiya, ka zama mai zaman lafiya. Idan kana son gaskiya, ka zama mai gaskiya. Idan kana son ci gaba, ka fara da ƙoƙarin kanka. Idan kana son a girmama ka, ka girmama wasu."
"Ya kai matashi, kada ka kwatanta rayuwarka da ta wasu. Kada ka yi baƙin ciki saboda wani ya samu abin da kai ba ka samu ba. Kowane mutum yana da lokacin da Allah Ya ƙaddara masa. Ka yi aiki, ka yi addu’a, ka yi haƙuri, ka dogara ga Allah."
"Kada ka manta da Lahira. Dukiya za ta ƙare, kyau zai shuɗe, ƙarfi zai ragu, amma ayyukan da ka yi za su kasance tare da kai. Saboda haka, ka gina rayuwarka a kan imani, ilimi, aiki, kyakkyawan hali da hidimar al’umma."
"Ya kai matashi, Kada ka jira gobe domin ka zama mutumin kirki. Ka fara yau. Kada ka ce: “Zan tuba idan na tsufa.” Kada ka ce: “Zan yi karatu daga baya.” Kada ka ce: “Zan gyara rayuwata nan gaba.”
"Domin ba a yi wa kowa alkawarin gobe ba. Ka yi amfani da ƙarfinka kafin rauni ya zo. Ka yi amfani da lokacinka kafin ya wuce. Ka yi amfani da damar da Allah Ya ba ka kafin ta gushe. Kai ba kawai matashi ba ne; kai amana ne. Amanar iyayenka. Amanar al’ummarka. Amanar addininka."
"Kuma a ƙarshe, za a tambaye ka yadda ka yi amfani da shekarunka da ƙarfinka. Saboda haka, ka zama matashin da al’umma za ta yi alfahari da shi, iyaye su yi farin ciki da shi, kuma addini ya yi shaida da kyawawan ayyukansa."
- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Source: Facebook
Daurawa ya yi wa matasa addu'a
"Allah Ya shiryar da matasanmu, Ya kare su daga fitintinu, Ya ba su ilimi mai amfani, sana’o’in halal, kyawawan abokai da kyakkyawan ƙarshe."
"Ya Allah, ka sanya matasanmu su zama jagororin alheri, ba mabiyan ɓarna ba; masu gina al’umma, ba masu rusa ta ba. Amin."
Shugaban APC ya ziyarci Daurawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar Hisbah a Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya karbi shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Farfesa Nentawe Yilwatda a ofishinsa.
Bayan ziyarar, Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa dangartakarsa da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ta fara ne tun shekarun baya.
Asali: Legit.ng

