Yara 13 Sun Mutu, an Faɗi Mummunan Abinci da Ƴan Bindiga Ke ba Su

Yara 13 Sun Mutu, an Faɗi Mummunan Abinci da Ƴan Bindiga Ke ba Su

  • Wata ma’aikaciyar jinya da na cikin mutane 163 da aka ceto ta ce kusan yara 13 sun mutu yayin da aka tsare su na tsawon watanni
  • Ta ce masu garkuwa sun jefa waɗanda aka sace cikin mawuyacin hali, inda suka ba su abinci kaɗan, musamman gero, gishiri da Maggi
  • Gwamnan Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ya karɓi waɗanda aka ceto, inda ya ce mutane 46 an kwantar da su asibiti domin samun kulawar lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - Kimanin yara 13 ne aka ruwaito cewa ba su cikin mutanen 176 da ƴan bindiga suka sako bayan shafe watanni da dama.

An tabbatar da cewa yaran sun mutu yayin da aka tsare mutanen da aka yi garkuwa da su daga wasu al’ummomi a ƙaramar hukumar Kaiama ta Kwara.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun mayar da yaran da suka sace cikin kungiyarsu

Yara 13 da ke hannun ƴan bindiga sun mutu
Gwamna Abdul Rahman Abdul Razak na jihar Kwara. Hoto: Kwara state Government.
Source: Twitter

Saliu Amira, wata ma’aikaciyar jinya kuma ɗaya daga cikin mutane 163 da hukumomin tsaro suka ceto, ta ce wasu yara 12 sun bi masu garkuwar yayin wannan lokaci, cewar TheCable.

Ta ce waɗanda aka yi garkuwa da su sun fuskanci matsanancin yanayi, inda masu garkuwar suka ba su abinci kaɗan yayin da suke tsare da su.

Ta ce:

“Abincin da suke ba mu a can... Ranar da muka isa wurin, sai kawai suka kawo mana gero tare da gishiri da Maggi.
“Sun bar mu a cikin kogin; yaran da suka mutu sun kusan 13, yayin da waɗanda suka bi su suka kai 12; jimillarsu 25.”

Nicholas Rume, kwamandan rundunar 22 Armoured Brigade, ya ce an ceto waɗanda aka yi garkuwa da su ne sakamakon haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

“Yau ina farin cikin gabatar muku da mutanen da muka samu damar ceto ta hanyar haɗin gwiwar hukumomin tsaro.
“Na gode wa sauran hukumomin tsaro da suka taimaka sosai a duk ƙoƙarin da muka yi. Abin da ya faru yau ya nuna irin haɗin gwiwar da ke tsakanin hukumomin tsaron ƙasar.”

Kara karanta wannan

Sojoji sun shafe mako suna ruwan wuta kan 'yan ta'adda, an kashe 69

- Cewar Nicholas Rume

Abdulrahman Abdulrazaq, gwamnan Kwara, ya karɓi waɗanda aka ceto a Ilorin, babban birnin jihar, ranar Juma’a.

Gwamnan ya yaba wa hukumomin tsaro kan nasarar aikin, inda ya ce kafa sabuwar rundunar soji zai ƙara ƙarfafa tsaro a jihar.

Abdulrazaq ya ce mutane 46 daga cikin waɗanda aka ceto an kwantar da su a asibiti, inda suke samun kulawar lafiya a wata cibiyar gwamnati.

Waɗanda aka ceto na daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a ranar 3 ga Fabrairu, lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai hari Woro, Nuku da wasu al’ummomi a Kaiama.

Yan bindiga sun mayar da yara cikinsu

An ji cewa yara 25 da ke cikin mutanen da aka sace a Kebbi, Kwara da Neja sun mutu a hannun ’yan ta’adda kuma aka binne su a cikin daji.

Mutane 315 sun samu ’yancinsu bayan shafe watanni shida a hannun ’yan ta’adda, yayin da wasu 12 suka shiga rundunar ’yan ta’addan.

Mata biyu da aka sace suna da ciki sun dawo da jarirai biyu, bayan ’yan uwansu sun ce masu garkuwar ba su taba su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.