"Kiran da Ka Yi a Tsige Wike Bai da Amfani" Ugochinyere Ya Caccaki Gumi

"Kiran da Ka Yi a Tsige Wike Bai da Amfani" Ugochinyere Ya Caccaki Gumi

  • Dan majalisar tarayya ya caccaki kalaman da Sheikh Ahmad Gumi ya yi kan ministan Abuja, Nyesom Wike
  • Ikenga Imo Ugochinyere, ya ce kiran da Malamin ya yi cewa a cire Wike daga muƙamin bai da amfani ko kaɗan
  • A cewarsa bai kamata hukumomin tsaro su haɗa hannu su bar waɗan nan kalaman kiyayyar su wuce haka nan ba

FCT Abuja - Sheikh Ahmad Gumi na ci gaba da shan suka daga mutane da dama kan kiran da ya yi ga shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya cire Nyesom Wike daga matsayin Ministan Abuja.

Wani ɗan majalisar wakilan tarayya, Honorabul Ikenga Imo Ugochinyere, ya gargaɗi fitaccen Malamin addinin Musuluncin na Kaduna kan kalaman da ya yi.

Dan majalisar wakilan tarayya ya maida martani ga Gumi.
Ugochinyere ya yi tir da kalaman Sheikh Ahmad Gumi Hoto: Ikenga Imo Ugochinyere, Sheikh Gumi
Asali: Facebook

A wani wa'azi da ya wallafa a shafin Facebook ranar Alhamis na sama da mintuna 14, Sheikh Gumi ya kira Wike da "Shaidan."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Shugaba Tinubu Ta Fara Kukan Babu Kuɗi a Ƙasa, Ta Ce da Kame-Kame Ake Biyan Albashi

Shahararren Malamin ya yi wa ministan lakabi da shaiɗan ne saboda ya karɓi bakuncin jakadan ƙasar Isra'ila a ofishinsa da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan Malamin ya bayyana cewa idan shugaba Tinubu bai ɗauki mataki ba za a dakatar da shi daga zarce wa zango na biyu a kan madafun iko.

Ɗan majalisa daga kudu ya maida martani

Amma, da yake maida martani ga kalaman Gumi, Ugochinyere, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilai kan albarkatun man fetur, ya nuna rashin jin daɗi da kalaman malamin.

Dan majalisar ya bayyana cewa kiran a tsige Wike bashi da tushe balle makama kuma ya fito ne daga wurin da aka tsani ’yan Kudu da mabiya addinin Kirista.

A cewarsa idan har ba a yi gaggawar ɗaukar mataki kan irin haka ba, za a iya wayar gari lamarin ya munana ya kai ga ɓarkewar rikicin ƙabilanci da addini a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Reno Omokri Ya Yi Martani Yayin da Sheikh Gumi Ya Caccaki Wike Kan Hada Kai Da Isra’ila

Ya ce yana fatan kalaman da Sheikh Gumi ya yi ba zasu ɗauke hankalin Ministan Abuja daga gyaran da ya ɗauko yi tun bayan kama aiki ba.

Ugochinyere ya ce wannan kalamai da Gumi ya yi na ƙiyayya bai kamata hukumomin tsaro su bari su wuce haka nan kawai ba.

Kwantena Ta Fado Daga Bayan Tirela

A wani rahoton na daban kuma Wata mata da har yanzu ba a gano bayananta ba ta rasa rayuwarta yayin da wata kwantena ta faɗo daga bayan Tirela a jihar Anambra.

Kwantenar mai tsawon kafa 40 ta murkushe matar har lahira a yankin Ize-Iweka da ke garin Onitsha ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel