Gini Ya Ruguje a Kano, Ana Fargabar Mutane da Dama Sun Maƙale a Buraguzai
- Kwana guda bayan faruwar lamarin, Ma’aikatar kashe gobara ta Kano ta ceto mutane 16 bayan wani ginin zama ya ruguje a Fagge
- Wasu mutane na ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin baraguzan ginin, yayin da jami’an ceto ke gudanar da aikin neman waɗanda suka makale
- An ceto yara uku da ba su cikin hayyacinsu, yayin da jami’an kashe gobara suka ce ba a gano musabbabin rugujewar ginin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - A ranar Asabar, 8 ga Agustan 2026, wani ginin zama ya ruguje a yankin Dan Dishe da ke Kwanar Yashi, ƙaramar hukumar Fagge a Kano.
Ma’aikatar kashe gobara ta Kano ta ce ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 4:32 na safiyar Asabar, inda aka sanar da ita rugujewar ginin.

Source: Original
An ceto mutane 16 a kasan ginin
Kakakin ma’aikatar, Saminu Abdullahi, ya ce jami’an sashen ba da agajin gaggawa daga hedikwatar ma’aikatar sun isa wurin nan take domin gudanar da aikin ceto, cewar Tribune.
Ya ce jami’an sun gano cewa ginin zama mai tsawon kusan ƙafa 20 da faɗin ƙafa 30 ya ruguje gaba ɗaya.
Jami’an kashe gobarar sun samu nasarar ceto mutane 16 daga ƙarƙashin baraguzan ginin, ciki har da yara uku da suka kasance a sume.
Yaran uku su ne Affan Yusuf mai shekaru biyar, Hassana Yusuf mai shekaru bakwai da Ummulkursum Yusuf mai watanni tara.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa, Abdullahi ya ce Ma’aikatar Kashe Gobara ta Kano ta samu rahoton rugujewar ginin ne daga wani ma’aikacinta, Aminu Sani Warure.
Sanarwar ta ce:
"Ma’aikatar Kashe Gobara ta Kano na sanar da jama’a cewa da misalin ƙarfe 4:32 na safiyar yau, Asabar, 8 ga Agustan 2026, sashen ba da agajin gaggawa na ma’aikatar ya samu kiran gaggawa daga ɗaya daga cikin ma’aikatanta, Aminu Sani Warure, wanda ya bayar da rahoton rugujewar wani gini a Dan Dishe, Kwanar Yashi, ƙaramar hukumar Fagge. “Bayan samun rahoton, an tattara jami’an ma’aikatar daga hedkwatar ta kuma aka tura su wurin da lamarin ya faru. Bayan isarsu, sun gano cewa wani ginin zama mai tsawon ƙafa 20 da faɗin ƙafa 30 ya ruguje.”
Jami’in ya bayyana cewa har yanzu ba a gano musabbabin rugujewar ginin ba, yayin da aka fara gudanar da bincike domin gano abin da ya haddasa lamarin.
Ma’aikatar Kashe Gobara ta Kano ta bukaci jama’a da su ɗauki dukkan matakan kariya da suka dace, musamman a lokacin damina, domin kauce wa irin waɗannan munanan abubuwa.
Lamarin ya faru ne ƙasa da wata guda bayan mutum ɗaya ya mutu, yayin da aka ceto wasu mutane uku bayan wani ginin bene uku da ake ginawa ya ruguje a ƙaramar hukumar Nasarawa ta Kano.
Ƙarin bayani na tafe. .
Rugujewar gini: Kwamishina ya ajiye aiki
An ji cewa Kwamishinan tsare-tsare da raya birni a jihar Legas ya hakura, ya ajiye aikinsa saboda wasu dalilai.
Ana yawan samun rugujewar gine-gine a jihar Legas, musamman daga bara zuwa tsakiyar wannan shekarar.
Gwamnatin jihar Legas ta kafa kwamitin da zai bincike musabbabin yawaitar rugujewar benaye a jihar Read more:
Asali: Legit.ng

