Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Nollywood Da Ke Halin Rashin Lafiya

Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Nollywood Da Ke Halin Rashin Lafiya

  • Gidauniyar tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ta biya kudin asibitin jarumin Nollywood da ke fama da rashin lafiya, John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu
  • An tabbatar da ci gaban ne a cikin wata wallafa da aka yi a shafin gidauniyar na Facebook a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba
  • Bayan fama da matsananciyar rashin lafiya, ana sa ran za a fitar da Mista Ibu waje domin samun kulawar da ya kamata a kwanaki masu zuwa

Gidauniyar Abubakar Bukola Saraki ta biya dukkanin kudaden asibitin shahararren jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu.

An bayyana wannan labarin ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a shafin gidauniyar na Facebook a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba.

Bukola Saraki ya dauki nauyin asibitin Mista Ibu
Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Nollywood Da Ke Halin Rashin Lafiya Hoto: Mr Ibu/Abubakar Bukola Saraki
Asali: Facebook

Kamar yadda yake kunshe a cikin sanarwar, gidauniyar ta ce tana matukar farin cikin taimaka wa Mista Okafor, fitaccen jarumin wasan barkwanci wanda ya haskaka talbijin dinmu tare da sanya farin ciki da raha ga gidaje da dama cikin shekaru arba’in da suka gabata.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Amince Da Nadin Sabbin Shugabanni Biyu a Ma’aikatar Lafiya

Sanarwar ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Lokacin da muka sami labarin rashin lafiyarsa na baya-bayan nan da kuma nauyin kudin da ke tattare da jinyarsa, sai muka ji nauyi ne da ya rataya a wuyanmu don taimakawa ta kowace hanya da za mu iya. Ba tare da bata lokaci ba muka biya masa dukkan kudaden asibitinsa har zuwa ranar Laraba.
"Muna karfafa wa duk wanda zai iya fitowa don taimakawa ta kowace hanya, imma da gudummawar kudi ko addu'a, gwiwar yin haka.
"Muna yi masa fatan samun sauki cikin gaggawa."

Mista Ibu ya koka, yana neman taimako

Ku tuna cewa a cikin makon nan ne, shahararren jarumin ya nemi taimakon yan Najeriya daga gadonsa na asibiti domin su taimaka su dauki nauyin asibitinta a bidiyo.

Mista Ibu ya koka cewa baya so a yanke masa kafa domin halin da yake ciki yana tsananin bukatar kulawar likitoci a kasar waje.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Abun Murna Yayin da Tinubu Ya Amince Da Biyan Malaman ASUU Albashinsu Da Aka Rike

A je a dawo mu na tare da Atiku, Tauraron ‘Dan wasan fim ya kunyata magoya-bayan Tinubu

A wani labarin, shahararren ‘dan wasan Nollywood, John Ikechukwu Okafor wanda aka fi sani da Mista Ibu, ya yi watsi da jita-jitar da ake yi a kansa game da zaben 2023.

John Ikechukwu Okafor ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Instagram, yace rade-radin cewa ya bi jirgin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, sam ba gaskiya ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng