INEC Ta Yi Wa Jam'iyyu Adalci kan Mika Sunayen 'Yan Takarar Gwamna da Majalisa
- INEC ta yi matsaya kan bukatar tsawaita wa’adin mika sunayen ’yan takara a zaben gwamna da na Majalisar Dokokin Jihohi na 2027
- Hukumar ta ce ta dauki matakin ne bayan jam’iyyun siyasa sun nemi karin lokaci domin kammala loda sunayen ’yan takararsu
- INEC ta kuma bayyana cewa wa’adin sauke kwafin PVC da za a iya bugawa ga masu zaben gwamnan Osun zai kare da tsakar daren Lahadi, 9 ga Agustan 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tsawaita wa’adin da jam’iyyun siyasa za su mika sunayen ’yan takararsu na zaben gwamna da na Majalisun Dokokin Jihohi na 2027.
Hukumar INEC ta tsawaita wa'adin mika sunayen 'yan takarar ne zuwa ranar Talata, 11 ga watan Agustan shekarar 2026.

Source: Facebook
Hukumar ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da Mohammed Kudu Haruna, kwamishinan kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na INEC, ya fitar ranar Asabar, 8 ga watan Agustan 2026 a shafin X.

Kara karanta wannan
Ta faru ta ƙare: APC ta ɗora sunayen yan takarar gwamna da mataimakansu a shafin INEC
Tun da farko, wa’adin mika sunayen 'yan takarar na gwamna da majalisun dokokin jihohi zai kare ne a ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026.
Sai dai hukumar ta ce ta tsawaita wa’adin ne sakamakon rokon da jam’iyyun siyasa suka yi na a ba su karin lokaci domin kammala loda sunayen ’yan takararsu a shafin da aka tanada.
Wa’adin sauke kwafin PVC
A wani abu da ya shafi zaben gwamnan jihar Osun mai zuwa, INEC ta ce wa’adin da masu kada kuri’a da suka nemi sauya katin zabe na dindindin (PVC) da ya bata, ya lalace ko ya goge za su sauke kwafin katunansu da za a iya bugawa zai kare da tsakar daren Lahadi, 9 ga Agusta, 2026.
Hukumar ta bayyana cewa matakin zai ba ta damar tattara bayanan adadin katunan PVC da aka sauke tare da tantance alkaluman karshe na jimillar katunan PVC da aka karba kafin zaben gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta, 2026.
INEC ta tuna cewa an fara rabon PVC a matakin yankunan rajista a jihar Osun daga ranar 22 zuwa 28 ga Yuli, 2026.
Bayan korafe-korafen cunkoson jama’a da matsalolin da masu kada kuri’a suka fuskanta a cibiyoyin karbar katunan, hukumar ta amince da tsawaita rabon a matakin yankunan rajista zuwa ranar 31 ga Yuli.
Daga bisani, aka mayar da rabon PVC zuwa matakin kananan hukumomi, inda aka ci gaba da rabon daga ranar 1 zuwa 7 ga Agusta, 2026.
An sauya katunan da aka sace
INEC ta kuma bayyana cewa ta samar da sababbin kwafin PVC da za a iya saukewa ga masu kada kuri’a a kananan hukumomin Odo-Otin da Ife Central, wadanda ’yan daba suka kwashe katunansu bayan mamaye cibiyoyin rabon katunan biyu.
Hukumar zaben ta jaddada cewa ba za a iya amfani da katunan da aka sace wajen kada kuri’a ba.
INEC ta tabbatar wa al’ummar jihar Osun cewa a shirye take ta gudanar da zaben gwamna na ranar 15 ga Agusta, 2026 cikin ’yanci, adalci, gaskiya da kuma bai wa kowa damar shiga.

Source: Facebook
Ba a ga Jonathan a jerin 'yan takara ba
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen ƙarshe na 'yan takarar zaɓen gama gari na shekarar 2027, wanda ya kawo ƙarshen dogon jiran da aka yi.
Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, wanda tsagin PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya ce ya miƙa sunansa ga INEC a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, bai bayyana ba.
Asali: Legit.ng

