Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani game da Tallafin N50,000 da Aka Fara Turawa Mutane a Najeriya
Yayin da Gwamnatin Tarayya ta fara shirin raba tallafin kuɗi na N50,000 ga talakawa da masu fama da matsin rayuwa a faɗin Najeriya, mutane da dama na son sanin yadda za su samu damar amfana da shirin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
An sanar da shirin mai suna National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI) ne a ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026, ta hannun Ministan Harkokin Jin Ƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro.

Source: Twitter
Ma'aikatar harkokin jin kai da rage talauci ta wallafa cikakkiyar sanarwa da bayanai kan wannan shirin tallafi a shafinta na yanar gizo.
Sanarwar ta ce ƙaddamar da tallafin ne domin rage wa al’umma raɗaɗin hauhawar farashin kayan abinci da kuma tsadar kayayyakin masarufi.
A cewar ministan, waɗanda suka cancanci tallafin za su riƙa karɓar N50,000 a kowane wata domin taimaka musu wajen biyan buƙatun yau da kullum da rage musu nauyin tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan
An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC
Ma’aikatar ta ce tana aiki tare da kamfanonin hada-hadar kuɗi ta intanet da aka ba lasisi domin tabbatar da cewa an raba kuɗaɗen cikin aminci da gaskiya.
Legit Hausa ta tattaro muku abubuwan da ya kamata ku sani game da wannan tallafi da gwamnatin tarayya ta fara raba wa mutane masu karamin karfi.
Waɗanne mutane za su amfana da N50, 000?
NTA News ta rahoto cewa Bernard Doro ta ce an tsara shirin ne domin bai wa talakawa da masu rauni a cikin al’umma tallafin kuɗi, musamman waɗanda hauhawar farashin kayan abinci da tsadar kayayyakin masarufi suka fi shafa.
Shirin zai taimaka wa waɗanda suka cancanta wajen biyan muhimman buƙatun gidajensu tare da rage musu matsin tattalin arzikin da ake ciki.
Ta ya za a zaɓi waɗanda za su amfana?
Bayanan da aka wallafa kan shirin NERSI sun nuna cewa za a zaɓi waɗanda za su amfana daga sahihan bayanan katin shaida na ƙasa da kuma Rajistar Jin Ƙai ta Ƙasa (National Social Register).
Bayan haka, za a tantance bayanan domin gano gidaje matalauta da masu rauni waɗanda suka cancanci tallafin.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta fara biyan tallafin N50,000 duk wata ga 'yan Najeriya, an ji masu amfana
Gwamnatin ta ce za a zabi mutanen da za aba tallafin N50,000 din ne bisa la’akari da buƙatar mutane, sannan a raba kuɗaɗen a matakai daban-daban.
Yadda mutane za su karɓi kuɗin
Gwamnatin Tarayya ta ce tana aiki da kamfanonin hada-hadar kuɗi ta intanet guda uku domin gudanar da rabon tallafin.
Kamfanonin hada-hadar kudin su ne:
- ALAT na Wema Bank
- MoMo Payment Service Bank (PSB)
- NairaGram
Shirin zai bai wa waɗanda suka amfana damar karɓar kuɗinsu ta manhajojin ajiyar kuɗi a wayar hannu da aka haɗa da lambobin wayoyinsu da kuma Lambobin Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN).
Waɗanda suka karɓi kuɗin za su iya cire su ta bankuna ko wajen masu POS. Haka kuma, za su iya amfani da kuɗin kai tsaye daga asusun subna waya wajen biyan buƙatunsu.
Shafin yanar gizo na wannan shirin ya kuma bayyana cewa mutanen da ba su da wayoyin zamani ko damar amfani da intanet za su iya duba ko suna cikin wadanda za a ba tallafin ta hanyar danna lambobi USSD.
Yadda za ku duba ta wayoyinku
Duk wanda yake son sanin ko ya samu shiga cikin jerin waɗanda za su amfana da tallafin kuɗi na N50,000 da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar karkashin shirin NERSI, zai iya duba cancantarsa ta hanyar danna lambobi a wayarsa.
Kowane kamfanin hada-hadar kudi da gwamnatin tarayya ta ambata a sama yan atandi lambobin da mutum zai suba ko an zabe shi cikin wadanda za a ba tallafin. Ga su kamar haka:
- ALAT (Wema Bank): *945*23#
- MoMo PSB *671*0#
- NairaGram: *726*00#
Bayan ka danna lambar da ta dace da tsarin da kake amfani da shi, zaɓi Check Eligibility domin sanin ko kana cikin waɗanda suka cancanta.

Source: Getty Images
Ana biyan kudi kafin karbar tallafin?
Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi ’yan Najeriya da su guji biyan wasu mutane ko wakilai da ke ikirarin za su taimaka musu wajen samun shiga cikin jerin waɗanda za su amfana da tallafin.
Bayanan da aka fitar kan shirin sun nuna cewa babu wani tsarin neman tallafin kai tsaye ko kuɗin rajista da za nemi mutum ya biya kafin sanya shi a cikin wadanda za su samu tallafin NERSI.
Maimakon haka, za a tuntuɓi waɗanda aka zaɓa ta saƙon waya (SMS) daga ɗaya daga cikin kamfanonin hada-hadar kudi da aka amince da su domin su karbi tallafin.
Saƙon zai nemi izinin wanda aka zaɓa kafin a tura kuɗin zuwa asusun kamfanonin hada-hadar kudi ta waya. Ana buƙatar wanda ya karɓi saƙon ya bi umarnin da ke ciki domin amincewa da karɓar kuɗin.

Kara karanta wannan
Yadda 'yan bindiga suka kafa gwamnatinsu, suke karɓar haraji kala 3 a jihohin Arewa 2
Yaushe za a fara biyan kuɗin?
Duk da cewa Gwamnatin tarayya ta sanar da fara shirin NERSI a ranar 30 ga Oktoba, 2026, ba ta wallafa cikakken jadawalin lokacin da kowane rukuni na waɗanda za su amfana zai karɓi kuɗinsa ba.
Gwamnatin ta ce za a gudanar da biyan kuɗin ne a matakai daban-daban. Saboda haka, ba lallai ne duk waɗanda aka zaɓa su samu saƙon sanarwa a lokaci guda ba.
Haka kuma, har yanzu gwamnati ba ta bayyana tsawon lokacin da shirin zai ɗauka ko ranar da za a dakatar da biyan tallafin ba.
A sanarwar da ya fitar, Minista Doro ya ce za a riƙa nazarin shirin lokaci zuwa lokaci bisa sauye-sauyen da ake samu kan tsadar rayuwa.
Ya ƙara da cewa za a sanar da waɗanda suka amfana kai tsaye kafin a yi duk wani sauyi a tsarin tallafin. Sai dai ministan bai bayyana takamaiman tsawon lokacin da shirin zai ɗauka ba.

Source: Twitter
Tarihin tallafin gwamnati
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa wannan ba shi ne karon farko da Gwamnatin Tarayya ke ƙaddamar da irin wannan shiri na tallafa wa talakawa ba.
A shekarar 2016, Gwamnatin tarayya ta haɗa kai da Bankin Duniya wajen ƙaddamar da National Social Safety Nets Project (NASSP), domin ƙarfafa tsarin tallafin jin ƙai da kuma taimaka wa gidaje matalauta da aka tantance.
Shirin ya ƙunshi tsarin rabon tallafin kuɗi na ƙasa, wato National Cash Transfer Programme, wanda ke bai wa gidaje matalauta da masu rauni waɗanda aka gano ta hanyar Rajistar Jin Ƙai ta Ƙasa tallafin kuɗi.
Yadda za ku nemi rance daga gwamnati
Kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bullo da tsarin SPARK da zai bai wa ’yan Najeriya damar karbar rancen kudi domin sayen wayoyin hannu da sauran na’urori.
Tsarin zai bai wa yan Najeriya damar neman rancen kudi daga gwamnatin tarayya domin sayen wayoyi ko kwanfutoci ta kananan wayoyinsu ba tare da sun yi amfani da intanet ba.
Masu bukatar amfani da tsarin za su iya shiga ta hanyar danna lambobi (USSD Code) a wayoyinsu na hannu da ba su da intanet
Asali: Legit.ng

