Zaman Kashe Wando Ya Kare, An Bude Wa Matasa 80,000 Damar Samun Aiki a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta horar da kusan ‘yan Najeriya 80,000 kan sana’o’i daban-daban domin rage rashin aikin yi da zaman kashe wando tsakanin matasa
- Horon da aka bai wa wadannan matasa na gudana ne karkashin shirin IDEAS-TVET na Ma’aikatar Ilimi ta tarayya
- Masu horaswa sun bukaci matasan da su yi amfani da dabarun da za su koya wajen gina sana’o’i da samar wa kansu ayyukan yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Gwamnatin tarayya, ta hannun shirin koyar da sana'o'i da fasaha na IDEAS-TVET ta horar da kusan ‘yan Najeriya 80,000 kan sana’o’i daban-daban domin rage rashin aikin yi da zaman kashe wando tsakanin matasa
Mai kula da shirin IDEAS-TVET ta kasa, Mrs Blessing Ogwu, ce ta bayyana hakan yayin kaddamar da horar da wasu matasa 900 a Ibadan, Jihar Oyo.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta rahoto cewa ana gudanar da horon ne karkashin rukuni na uku na shirin Ma’aikatar Ilimi ta tarayya, tare da hadin gwiwar cibiyoyin horaswa guda shida (TSPs) a jihar.
Za a sake ba mutane 900 horo
Ogwu, wadda Mrs Ihuoma Francisca ta wakilta a wajen taron, ta ce horon mai zurfi zai bai wa matasa masu shekaru tsakanin 15 zuwa 35 dabarun aiki a fannoni daban-daban na sana’o’i.
Ta ce za a horar da mutane 200 kan noma da sarrafa su, yayin da mutane 150 kowanne za su samu horo kan gyaran kwamfuta da wayoyin hannu, kiwon kifaye, kiwon dabbobi, da harkokin girki da kula da baki.
Za kuma a horar da wasu mutane 100 kan dabarun zamani, ciki har da gyaran kayan aikin kwamfuta da wayoyin hannu.
Abubuwan da aka koya wa matasa
Ogwu ta ce shirin IDEAS-TVET ya bada horon sana’o’i kai tsaye ga kusan ‘yan Najeriya 80,000 ta hannun cibiyoyin horaswa da ke fadin kasar, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Ta ce an horar da wadanda suka ci gajiyar shirin kan fannoni daban-daban na sana’o’i, ciki har da dinkin zamani, fasahar sadarwa da bayanai (ICT), noma, harkokin masauki da kula da baki, gine-gine da sanya na’urorin lantarki.

Source: Twitter
Sana’o’in da suka shafi motoci, walda da kera kayayyaki, gyaran waya, kula da kwamfuta, aikin famfo da sanya na’urorin amfani da hasken rana na cikin wadanda aka koyar.
Gwamnati ta fara rijistar matasan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin ShugabaNBola Ahmed Tinubu ta kaddamar da shirin rijista da tattara bayanan matasa na NYDB a fadin Najeriya.
Gwamnatin ta bukaci ’ yan Najeriya masu shekaru 15 zuwa 35 su yi rajista da shirin NYDB, inda ta ce hakan zai taimaka wajen gano kwarewarsu, bukatunsu da wuraren da suke.
Ta ce rijistar za ta shafi matasa da ke bangaren aiki na hukuma da wadanda ke gudanar da sana’o’in kansu, ciki har da masu aikin gona, wasanni, masana’antun kirkire-kirkire da fasaha.
Asali: Legit.ng

