Gwamnatin tarayyar Najeriya
Gwamnatin jihar Zamfara ta kaddamar da raba tallafin kudi har Naira biliyan 4.9. Mata, marasa lafiya, 'yan agaji da malaman Islamiyya za su samu tallafin.
Dattawan Igbo sun jaddada bukatar kafa jihar Anioma a shiyyar Kudu maso Gabas, suna masu kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dauki matakin tabbatar da hakan.
Gwamnatin Bola Tinubu ta fadi abin da zai faru da Najeriya a shekarar 2025. Wale Edun ya ce za a samu habakar tattali a 2025 saboda tsare tsaren tattalin arziki.
Hukumar RMAFC ta ce dokokin gyaran harajin Shugaba Bola Tinubu sun saba wa tsarin mulki, tana mai bada shawarar amfani da tsarin raba VAT da zai zamo adalci ga kowa.
Bayan Majalisa ta tabbatar da naɗinsa, sabon hafsan rundunar sojin Njeriya, Laftanar Janar Oluyede ya kama aiki a hukumance yau Litinin, 9 ga Disamba.
Gwamnatin tarayya ta yi cikakken bayani kan yadda kudurorin gyaran harajin Shugaba Bola Tinubu za su amfani talaka da kuma kananan 'yan kasuwan Najeriya.
Kamfanin mai na kasa watau NNPCL ya fara tura saƙonni ga waɗanda suka ci jarabawar CBT da aka kammala, ya gayyace su zuwa tattaunawar baki kafin ɗaukarsu aiki.
Gwamnatin tarayya ta ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki lamarin abinci da matuƙar muhimmanci, burinsa kowa ya ƙoshi kafin ya kwanta a kowace rana.
Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana fatansa ga Najeriya. Ya faɗi burinsa bayan ya shafe shekaru 99 a duniya inda ya dade ya na fafutukar ci gaban ƙasa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya
Samu kari